← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 208

Sashe 83

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nashi a gaban shi amman sai yaga Aji ya zauna kawai ya bu e tuwan hannun shi ya kafa kai ya fara sha sai kawai ya saki baki kafin ya ce" Ya haka Aji? Ina nawa ruwan? Kai tsaye ya ce"Ba ka da kafa ne? Balagagge da kai sai ka zauna ina maka aiki" Nasir sai ya ka a kai ya mike lokaci aya yana fa in" ba laifin ka ba ne, dole ka min wulakanci tunda ka ga na gama shiga na fita an gama wannan auran cikin rufin asiri." Sai kawai suka ji Aji na fa in" Ai ni ban gayyace ka ba, abunda ka zo ka yi kuma wannan ra'ayin ka ne Nasir kada ma ka yi tunanin watarana zan iya gode maka." Nasir ya auko ruwansa ya dawo ya zauna ya bu e ya sha bai ce komai ba Makama ne ya gyara mganar da cewa" Ai mu ba abokan ka ba ne mun zama an'uwan ka, mune ma masu gayyatan wasu." Nasir ya ce" shiyasa ai na tura masa. aniyarsa" Yana jinsu bai yi mgana ba Mu'azzam kuma yana duba wayarsa ne ya na mirmishi Ahmad kuma yana waya da Kostomomin shi na can ya na gaya musu in sha Allahu gobe zai dawo. Makama na dariya ya ce"Shege tela ya ha a ka shi ya gudu" Ahamad dariya kawai ya yi bai yi mgana ba. Aji daman ke gefensa ta hannun dama sai kawai ya dafa kafa ansa lokaci aya yana fa in" Thank you so much Ahmad gobe ka koma wajen aikinka kada ka samu wata matsalar." Sai ya jinjina masa kai lokacin har ya gama waya da sauri ya ce" Ba wata matsala in sha Allahu" Nasir ya yi wata dariya ya buga kafa kafin ya ce" Mu ai sai ka tsine mana ka ji tunda ba mu yi maka komai ba." Aji ya kallesa lokaci aya ya!a aga masa gira guda aya, Nasir sai ya fara dariya Makama na taya shi, Mu'azzam na can wajen bin kiraye kiranye da aka yi masa daga jiya zuwa yau bai gani kawai sai ya ga Anty Mami ta kira shi kamar yadda ya yi Saving in sunanta a wayarsa. Da Sauri ya gyara zama yana fa in" kai azu ashe Anty Mami ta kirani ban gani ba." Gaba ayansu suka kalleshi a tare barin ma Aji da ya kafeshi da ido ya na wani nazari. Nasir ya yi saurin cewa" To ba dole ta kira ka ba, tun jiya ba ta ga gilmawar Angonta ba.". Aji ya balla masa harara kafin ya yi mgana Nasir ya yi saurin cewa" ba inciki kake yi mana da cin girkin Amarya da yanzu yadda mu ka shigo gidan nan mun samu kyakyawan tarba daga Amarya da girkinta." Aji ya yi kamar bai ji ba sai can ya muskuta kafin ya ce"Har yanzu dai baka daina kwa ayi baa ko Nasir? To sai dai ka Mutu ba za ka ci girkin Mimi ba, ai ba girki na auro ta ta ri a yi ma garada ba, wannan daga gani matarka na shan wahalar ka" Nasir bai samu sararin maida martani ba Mu'azzam ya kira wayar Mimi har ta auka sai shi kuma ya saka ta acikin speaker Suna ta jin hayaniya ga hiran su Bintu, kenan har lokacin t na akin Inna Meri sai bayan sun gama gaiasawa sannan Mu'azzam ya ce" Kiyi Ha uri Anty Mami da Safe ban ga kiran ki ba sai yanzu da ina duba wayar, ina fatan dai lafiya ko? Daga can bangarem Mimi dake cikin mayafinta ta ce" Ba wata matsala daman a azun ruwan wanka nake so kuma ina kunyar fita to sai na le a ma na ga walida sai na yi mata mgana." Sai Mu'azzam ya ce" Ayya bakomai Ina fatan dai ba wata matsala ko? Nasan ai ke yanzu ba ki da ba unta? Sai ta yi mirmishi ba tare da ta yi mgama ba sai Nasir me ya karkata kai ya na fa in" ga mu nan zuwa siyan baki tare da Angon naki." Suna jiyo sautin mirmishinta kafin ta ce"Allah ya kawo ku lafiya" Sannan ta katse wayar Nasir ya kalli Aji da ya yi shuru bai yi mgana ba da Sauri ya ce"Ango ka tashi ka shirya mu je mu mi a ka mu taya ka siyan bakin Amarya, kowannen mu nan a matse yake da yaje gida ya samu natsuwa da matarsa Ahmad dai sai gobe Mu'azzam kuma in ba zai iya jiran gobe ba ya ja matarsa su ke Ya karishe fa a yana yar dariya Makama ya shuru kafar Nasir, Ahmad kuma sai kawai ya yi dariya Mu'azzam kunya duk ya kama shi ya kasa ha a ido da yayan na shi da irin maganganun nan ba su ta a shiga tsakanin su ba akwai girmamawa a tsakanin su sosai. Sai falon ya au shuru Nasir ke ta dariya yana nfa in" Kun yi wani shuru kamar mutuwa ta gifta, gaskiya na fa a ko kunyar wannan tazurin angon kuke ji? Oh sorry amman ai yanzu zai zama an gari shima wa ya sani ma ko ya fi mu matsuwa." "Nasir..!" Aji ya kira sunanshi a kausashe sai ya juya yana kallonsa kafin ya ce" miye arya na fa a? Aji ya yi shuru bai yi mgana ba sai kawai ya kalli Mu'azzam kafin ya ce"Mu'azzam shiga aki na ka duba min wayata." Shi kuma sai yace toh ya mike ya shiga akin nasa ya na rufo kofa Aji ya juya a fusace yana kallon Nasir kafin ya ce" Ko ba ka ji kunya ta ba, ya kama ta kaji kunyar Mu'azzam ta ya za ka zauna kana irin wa anan mganganun masu nauyi a gabansa? Dariya da mamaki su kama Nasir ya Juya ya na kallon Makama shima sai ya juya ya na kallon Ahmad dukkansu kuma sai su ka maida hankalinsu kan Aji dai dai lokacin da yake fa in" Nasir ba na so ba na so ka sake irin wannan mganar a gaban anina." Nasir ya bushe da wata dariyam renin hankali kafin ya ce"Shi Mu'azzam in? Ko ka manta yana da mata har da Aji ya ce a fusace"So what don ya na da mata? Ai ba ka fi ni sanin ya na da mata da a ba, ni irin maganganun nan ne ina jin nauyin in ina waje kana yin su, ni ban damu in ba na nan ka yi tayi ba amman ba na so kana yi ina wajen shima kuma yana wajen ba na jin da in haka" Nasir yace"To ai shike nan amman ai kasan ya fi ka sanin harkan yanzu, kila ma sai da ma ya koyar da kai." Dai dai Lokacin da Mu'azzam ya fito daga cikin akin auke da wayar a hannunsa yana kuma fitowa tun kafin ma ya ariso Mansoor ya ce masa a kausashe" Mu'azzam koma ciki zan yi magana da Nasir" Sai Mu'azzam ya juya ya koma ciki Ahmad da Makama suna ta faman danne dariyansu Nasir kuma mamaki ne ma ya hana shi mgana. Shi kuma Aji ya na ganin Mu'azzam ya koma ciki sai kawai ya kalli Nasir kai tsaye yana fa in" Duk abunda kake tunanin ka sani ni bansa ni ba, ka yaudari kanka Nasir na san da yawa ma acikin abunda ba ka sani ba, ni tsakanina da anina akwai girmamawa ba irin wa anan mganganun a tsakaninmu, ba na so ka na yi a gabansa in ina wajen saboda gudun reni ko wani abu ya gifta a tsakanimmu duk da nasan waye anina amman gwara dai ka kiyayen zai fi" Nasir ya kar e mganar da cewa"To wai anin naka yaro ne? Ko kuma mu ba mu da anne ne, sai ka ri a nuna kamar ba kamar Mu'azzam a gaban mu." Sai kawai su ka ga ya yi mirmishi mirmishin da su ka da e ba su ga ya yi kamarsa ba domin har fararen ha oransa na bayyana, Cikin wani sauti ya ce" Sunan anin ka Salisu ni kuma sunan anina Mu'azzamu ka ga kenan suna da banbamci ko ta wajen suna kai sunan ka Nasir yayan Salisu, ni kuma sunana Mansoor yayan Mu'azzam, kuma ni har gobe ko tsufa Mu'azzam zai yi ba zan daina ganin sa a matsayin aramin anina da ya taso a tare da ni ina ba shi umarni ya na bi ba, har gobe a haka nake aukan Mu'azzam ka gane ko? Nasir sai ya yi dariya makama kuma ganin kamar abun zai koma hayaniya sai ya ce a bar mganar yanzu dai Aji ya je ya shirya su raka shi kai tsaye ya ce" Ni yaro ne da sai kun ta sa ni a gaba kun kai ni, ai nasan hanya in na gama a bunda nake yi zan je da kaina" Suna jin haka sai suka mimmi e har da Nasir da ya yi mi a kafin ya ce"To har mu masu auran ya ce yasan abunda ba mu sani ba, Ai lamarim Aji sai Allah ya shirya kawai ai ba'a fa in sauran zencen." Aji na ka a kai kafin ya ce" Duk abunda ka ke tunani haka ne Nasir kila ma harda wanda ba ka yi tunanin ba" Daga haka ya mi e ya isa kofar cikin akinsa yana kiran sunan Mu'azzam daga ciki da ya amsa sai ya ce ya fito sai ko ga shi ya fito, kawai sai Mansoor ya dafa kafa arsa yana fa in" Sai na zo ko? Sai Mu'azzam ya ce"Shike nan zan kwana wajen Ahmad" Sai kawai yace"To nan in fa? Kai tsaye Mu'azzam yace"Ya yi nisa, kuma gobe asubanci za mu yi." Aji sai ya jinjina kai kawai, har kofar gida ya raka su, Nasir ya auke kai ya shiga gaban motar Mu'azzam Aji ya bishi yana fa in" Nasir ina godiya fa." Nasir ya wani ha e rai kafin ya ce" Bakomai yi wa kai ne." Dariya ta kama su Ahmad sai da suka dara shi kuma Aji ya dafa kafa an Nasir yana fa in" Good Boy." Kafin ya bar jikin Motar su ka ja suka wuce, motar Mu'azzam na gaba tare da Nasir sai ta makama a baya Ahmad na tare
Chapter 83 · 0% Book details