← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 208

Sashe 156

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baka gq murnan da ya yi ba." Dariyansu na manya ya yi kafin ya ce"Shi ma dai sakarai ne, mace da mijinta bai sake ta ba ne yake murna a kanta? Ke ce kuma ba ki ga ya masa gaskiya ba gwara tun da wuri ya hakura da Mimi in da ace tana son shi da ta za e shi amman tunda ba ta iya za arsa a baya ba yanzu ma ba za ta za e shi ba, ki zauna ki gaya masa gaskiya Mimi ta haramta gare shi gwara tun lokaci bai ure masa ba ya nemi wata domin ba zan barshi ya tsallake shekaran nan bai yi aure ba." Yana gama fa in haka ya mike ya shige ciki ya barta zaune da tagumi, har Allah ta na jin haushin Hajiya domin ita ta i ba ma Jaheed goyon baya in da tana so da Mimin ba ta isa ta yi gaddama ba, amman an na ce an ce sai abin da take so ga ta nan ga abin da ta ke so in nan ya na wahalar da ita. Ranta ba da i itama ta bar falon zuwa aakinta tana tunanin kiran anwarta Hajiya Turai su tattauna mganar. ******* *MIMI* Lokacin da Daddy ya samu wayar Madiha wajen kwana uku da zuwan Aji wajensa ya na ta kiran wayar Mimi ba ya samu sai ya kira ta Madihan tunda suna tare, bayan sun gaisa ya ce ta ha a shi da Mimi sai ta ce tana na akinta in sun fito zuwa masallaci da yammah zata sanar da ita akan ta kira shi. Wannan sa on Madiha ta gaya ma Mimi sai ita kuma ta kunna wayarta ta nemi Daddy a waya suka yi mgana ba tare da wani dogon mgana ba ya ce" An gaya miki mijin ki nata zuwa neman ki baya samun ki? Sai ta amsa masa bai ba ta samar mgana ba ya cigaba da fa in" To daga arshe dai ya zo ya same ni mun tattauna ya kar i laifukansa ya ce zai gyara na ba shi damar ya same ki ku yi mgana kin ji ko? Gaddama ba halinta ba ne ya sa ta ce masa in sha Allahu sannan ya ara da cewa"Yaushe za ku dawo? Kai tsaye tace" Bansa ni ba amman ina tunanin cikin satin nan." Sai ya ba ta umarnin in ta dawo ta nemi mijinta su yi mgana har ya kara da cewa" kada ki damu na yi mgana da shi na fahimci fushin zuciya ne amman shima ya na sonki kuma ya fa amin ma da bakin shi, kawai dai ki yi amfani da wannan damar ki sauyashi zuwa yadda kike son ya dawo kin ji ko? Cikin girmamawa ta amsa masa sannan su ka yi sallama sai ga ta rumgume da waya a kirjinta tana hamdala karfinta zuwanta umra akan Aji ne ta ro i rabil samawati ya sausauta zuciyar bawansa Mansoor ya sanya masa salama da Aminci da natsuwa ya daidai ta masa rayuwarsa sannan ya Ha e kansu shi da ita su zauna Lafiya su gina rayuwa mai kyau tare da zuru'a ayyiba, in da alheri a komawarta in kuma babu alheri ya cire mata son shi salin alim a cikin zuciyarta. Itama dai tuni duk wani fushi da take yi ta ji komai ya yaye mata ta ji ta yafe masa duk da cin zarafin iyayenta da ya yi in ta tuna ranta na aci, sannan kuma sintirin da ya ri a yi a kanta ya tabbatar mata da cewa tana da wata ar daraja a wajensa Sai yanzu ta ke ganin amfanin shawaran Rukky kuma a yanzu take da damar sauya rayuwarsa kamar yadda Daddy ya yi mata gugar zana. Daman tun da suka zo garin Ma'aiki ta kashe wayarta tana Ibadunta, wayar da suka yi da Daddy ya sa ta fara yi ma Madiha zencen komawa, ita kuma daman ta na siyayya shi ya sa a satin ba su samu dawowa ba sai da wani satin ya shiga sannan suka dawo lokacin suna da sati hu u kenan a can. Sun dawo suka iske Jawahir ta sauka amman sai da aka yi mata C.S. Shi ya sa kwana uku kawai mimi ta yi ta huta sai ta bi jirgi daga lagos Jirgi zuwa Kano Ta kunna wayarta ta yi mgana da Hajiya da Rukky tana gaya mata halin da a ke ciki Rukky ta buga shewa kafin tac e"Dakyau. Lokacin mu yanzu ya fara, ki kira shi ki sanar da shi kin dawo amman za ki tsaya a kano saboda haihuwar Matar Dr" Haka ko ta yi amman ta kira shi har sau bai auka ba sai ta tura masa sa "Na dawo, amman Ina kano Anty Jawahir in Dr ta haihu, zan kai sati ina ga kafin na dawo Gombe." Amman har dare ba ta ga kiran shi ba har ta fara jin haushi shi kuma suna Jos a lokacin sun je buga wasa sai dare ya ga kiranta da sa on ta a lokacin ya ga ji sai kawai ya tura mata da cewa " Allah ya raya abunda aka samu, in kin dawon ki sanar da ni, nima ba na gari ina Jos" Ta yi barci sai da safe ta ga sa on sa. Sai ta yi masa uzuri tunda ta ji ya ce baya gari to sun je buga wasa ne tabbas. Sai kawai ta share kafa a gidan Dr, Jawahir kuma samar matar likita ne tuni cikin kwana uku ta fara motsa jikinta Shi y asa ba'a aga suna ba.Dangin Mommy da suka zo barka su ga Mimi ba su kawo wani abu ba har Inna Zainaba tunda Mommy ba ta sanar da su an samu wata matsala ba, Sai da suka zo suma mata tsiyan sai dai ta zo ta tsaya gidan Dr sh ine fa ta ji kunya ta bi inna Zainaba gidanta ta kwana ra an zaga yan'uwa tare da dangi na kusa kwananta biyu a Soron inki ta tuno da Hibba sai ko ta aga waya ta kirata bayan ta cire ta daga Kullenta da ta yi, Hibba kamar amafarki ta ga kiran Mimi ta auka cikin mamaki tare da neman yi mata tsiya Mimi na dariya ta ce tana kano ta tura mata adireshi gidanta za ta zo sai su yi mgana jiki na rawa Hibba ta tura mata, Mu'azzam na Office ta kira shi ta na gaya masa suna da babban bakuwa Mimi za ta zo, shima cikin murna ya ce zai baro Office ya zo su gaisa. Tana tura mata ba da ewa ta baro gidan Inna Zainaba, mai adaidaita ta nuna masa kwatance ya ce ya san Gidan ya na bakin hanya ne da ba ta gane ba ta kira Hibba Sai ta fito bakin gidan sannan ta hangeta, Bayan ta sallami mai adaidaita ta karisa suka rumgume juna da Hibba wacce ke yi mata tsiyan cewa" Anty Mimi idon ki kenan? Mu kan ba da laifi ba duk an ha amu an hukunta." Ta na dariya ta ce" Shi ya sa na zo ban hakuri." Suna dariya suka karisa cikin gida Hibba ta rasa ina zata saka Mimi ta kawo mata Breakfast domin lokacin sha dayan safe ne Hibba ta ce ta karya sai dai na rana tunda nan za ta yi mata yini. Nan fa suka zauna suna ta hira Hibba ta ce" Mu dai me muka yi ne gaba aya a ka kulle mu Hajiyar Allah? Mimi na dariya ta ce" Ba fa abib da kuka yi kawai dai lokacin sai a hankali na kuma san ro o na za ku yi ni kuma ba zan iya muku abin da ku kuke so lokacin ba shi ya sa." Hibba ta ce"Duk da haka dai, ni dai kinsan ba zan matsa miki kan abib da ba ki yi niyya ba, mu ka je har gida kika hanamu ganin ki sannan a wayar ma duk an rufe mu yanzu kin kyauta kenan? Laifin Babba Yaya sai ya shafe mu? arishe fa a ta na yar dariya Mimi na dariyan take yi tana ba ta hakuri. Hibba ta ce"Ya muka iya? Dole mu hakura amman bayan an gama bamu wahala, Kawai sanadin ki sai ga Yaya Mansoor har gidan nan." Mimi na mamaki ta ce"Kai don Allah." Hibba ta ce" Wlh ai albarkacin kaza ma Kadangare kan sha ruwam kasko, kin ciru tuta tun dai ya na basarwa har dai ya fahimci ke in ce, sai faman sintiri yake yi a saman hanya saboda ke fisabillahi mu dai a kyale mana Yaya haka anan ai dai ko a haka aka tsaya jikin ta aura ya yi la'asar." Mimi na dariya t ace"Tabbas haka ne." Nan ta shiga ba ma Hibba labarin wayarsu da Daddy da abin da ya ce. Duk da Mu'azzam ya gaya mata Yaya Mansoor ya je can gidan kuma an samu daidato sai Mimi ta dawo amman bai bu e mata ba, Hibba ta ce"Ma sha Allah haka ake so, Wlh Yayammu ya sauya kamar ba shi ba. Gida kuma ai sai dai ya siya miki wani tunda har Inna ma yanzu ba ta a gidan." Mimi ta zaro ido kafin ta ce" Innar? Me ya faru? Sai Hibba ta shiga warware mata abib da ya faru ta are da cewa"To dai yanzu Inna ta samu cigaba tana gidan Yaya mansoor, ya kuma ce ya mallakaa mata har Abada." Mimi na jinjina kai ta ce"Allah Sarki. Na yi ma Inna Murna, daman ni tuni nasan wannan Maeesha makira ne, kai Allah ya kyauta dai." Hibba ta amsa da Amin lokaci aya tana fa in" Ke kam ai sai dai ki ba da izini kawai a fara ora miki gini." Mimi na dariya ba ta yi mgana ba, Hibba kuma ta kara da cewa" A yi hakuri in sha ba za mu ara ba, kuma muna da ku i za mu gina miki duk irin gidan da kike so.".! Nan ta bar Mimi da dariya. Haka suka cigaba da hiraran su, Mimi ba ta oye ma Hibba komai ba kan shirin da suke yi ita da Rukky itama ta goyon baya da cewa"Dakyau, wlh ban ga laifin ki ba gwara ki gwara
Chapter 156 · 0% Book details