← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 203 OF 208

Sashe 203

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ji ma gani in sun isa su sauya ma tuwo suna. Mimi ce ka ai a gidan itama sun yi da Aji zai zo bai kuma zo ba sai bayan azahar shima da labarin Mommy ta tare shi sai ya washe baki yana ri e da Ummi lokaci aya yana fa in"Ma sha Allahu abun alheri madallah. Na yi ma Mommy murna Allah ya ba su zaman lafiya." Kawai sai ta saka masa,kukan me ya sa zai yi murna saboda Momny ta yi aure? Ba ya kishin Abi ne me ya sa Mommy za ta ara aure? Cikin Mamaki ya kalli Mimi kafin ya ce"Ban gane ba? Saboda addini ya ba ta wannan damar gwara da ta yi auranta sai mutumcinta ya fi fitowa a idanuwan wa anda suka santa, sannan kuma kwanciyar hankalinku ne ku tuna yau tana da miji kuma sannan kun kara samun wani abu a karo na biyu." Kawai sai Mimi ta saki baki ta kasa mgana, Aji ba zai gane ba ne shi ya sa ba ta ma samu damar gaya masa abunda ya faru da su khadi ba sai da ya shiga suka gaisa da Hajiya ita ke gaya masa har ta na cewa" Ga ta nan duk da itama ba ta ce komai ba amman zuciyarta ba da i ka sake yi mata fa a don Allah kada su saka ma Murja hawan jini." Aji ya kalli Mimi da ke gefen sa kafin ya ce"Haba Hajiya, suma in yarinta ne amman in su san ciwon kansu ai ba za su yi haka ba, sannan su mata tunanin su a karkace yake, shi Dr da yake namiji ne ai ya fahimta kada ki damu Mommy auran da ki ka yi masalaha ne ga rayuwarki da ta su gaba aya ba za kuma su fahimta ba sai nan gaba ka an." Inna Zainaba ta ce" Ka ji maaganar masu hankali, itama sai ata rai take yi tunda an'uwan sun yi fushi sun tafi." Kuma da gaske nan ko fara'a Mimi ba ta yi Mommy ma duk ranta a jagule ga shi sai kiranta a ke yi masu yi mata murna, tunda acan kano aka aura auran shi kan shi Al ali bai je ba. Sai dai waliyyansa kuma da kan shi ya fa a mata an ce babban anta ne ya arbi sadakinta wato Dr Sulaiman farinciki ya cika Mommy har sai da ta yi kuka a ranta ta yi ma Sulaiman fatan ya gama da duniya lafiya shi da iyalansa yadda ya ke faranta mata shima Allah ya faranta masa haka. Aji bai tsaya wani lallashin Mimi ba saboda ya ga kamar abun na su har da iskanci, bai nuna ma ya gane ta na jin haushi ba bai da e ba ya tafi sun rabu akan itama gobe za ta koma, cikin zolaya ya ce" Ki tsaya mana ko zuwa laraba ku gaisa da sabon Abin naku mana." Hararansa ta yi sai ya yi shuru ya na dariya , har ya ci abinci ta tafi raka shi tana kumbure kumbure shine ma ya sa ta saki fuska tunda cakulkuli ya ri a yi mata tana dariya. Yana kuma tafiya ta koma yadda take, Mommy ba ta yi gayya ba amman ta gayyaci abokan aikinta sun zo mata murna tunda da aurin auren da tariyan duk aya ne ita a gidanta za ta zauna shi ne zai rika zuwa wajenta in ranar girkinta ya shiga, bai zo a daran ba sai washegari da safe da ta ce ya zo su gaisa da Hajiya da Mimi za su koma Gombe. Gaskiya a ido mutum ne mai kamala da dattako ba yaro ba ne domin zai iya yin sa'an Abin ma, sun gaisa cikin girmamawa da Hajiya, Mimi kuma tana gaisheshi ya kama sunanta da cewa"Mimi auta ko? Yau dai navga auta." Ya fa a ya na mirmishi ya mi a hannu ya kar i Ummi yana fa in"Ga kuma Ummi maryama ko? Sai Mimi ta gya a masa kai a ranta tana fa in su Mommy manya, ta sha kwaliyarta suna ta yi ma juna wani kallo. Ba ta gama mamaki ba sai da ta ji ya na tambayan su Madiha tunda Mommny ta gaya ma sa dukkansu sun zo. Da sauri ta ce Madiha za ta koma saboda yara ita kuma Khadi saboda aikinta sai ya ce bakomai wata rana ai za su ha u Dr dai yana kano sun ha u tunda shi ya ba da auran Mommyn tashi ya fa a har ya na kashe ma Mommy ido, Mimi ta ji kamar ta make shi saboda haushi. 10k ya saka ma Ummi a jikinta sannan ta yi masa sallama ta bar falon zuciyanta na aci saboda haka ta matsama Hajiya suka koma Gombe a ranar domin ba za ta iya zaman ganin wannan bakincikin ba Aji ma ya yi da ita ta zauna da Mommy ko na sati ne sai su koma tare amman ta ki sai ta fake da aiki shi kuma ya san dalili amman sai ya yaleta. Kuma da ta dawo ko a zencen ba ta ta a fa an cewa Mommy ce ta yi aure ba. Ko Inna ba ta gaya mawa ba ta kuma san Aji ba shi da surutu daman dai Mu'azzam ne, Rukky dai ta samu labari ta bangaren Jaheed da ta kira ta ta na tambayanta ashe kuma Mommy ta yi aure sai kawai ta ce"Uhm" daga nan ta sauya mganar har Rukky dai ta gano Mimi ba ta son mganar. sannan da kanta ta kira su khadi ta na gaya musu abin da ya faru sanda Al ali ya zo tana gaya musu Mommy ta ba shi labarin kowa ya san shi ya sunan sunan shi. Madiha bakin ciki kamar ta mutu sai ta ce" Wai mommy yarinya ce? Ji fa wannan aikin da take yi mtswww.." Ta yi tsaki duk suka ara saka Mimi a tafiyarsu na ba su amince da auran ba shi ya sa ko da ta dawo ko sau aya ba ta kira Mommyn ba sai ita ce ta kirata tana cewa ba ta kira ta ba kada bakin Mimi sai ta ce"Ina zan kira na takura miki Mommy, na baki lokaci ne ki ci amarcin ki.' Mommy sai ta kasa mgana jiki a sanyaye ta ce"Ke ma kin kasa fahimtata ko Fatima.? Da Sauri Mimi ta ce"Na fahimta kina son aure kuma kin yi, Allah ya ba da zaman lafiya. Daga nan ta kashe wayarta daga ranar ba ta ara nemanta ba, itama Mommy sai ta ba ma zuciyarta ha uri ta tsaya ganin in da suka dosa. Matar al ali da yayansa sun kar eta sosai sai ita ce ke da yayan da ke yi mata barazana in ka cire Sulaiman Asma'u sai murna take yi ta samu Abba amman ban da su Madiha da suke kishin Abi sannan suna ganin kamar abun kunya ne. Hibba ta saamu labarin auran da Mommy ta yi ta bakin Jawahir tunda sanadin Mimin suna zumunci ta je gidan shi ne ana hira labari ya kawo ta fa a mata, tana komawa kuma ta fa ama mijinta shi kuma sai ya xe bai ji ba, bayan ya kira yayanshi ya tambayeshi sai ya ce eh da gaske ne. Ke Hibba sai ki ka ga Mimi a chart sai kika ce mata" Matar Yaya ashe kuma Mommy ta yi aure? Allah ya sanya alheri." Sai ta tura emojin dariya har da na rawa, wannan abun Mimi ta gani sai ranta ya aci kawai sai ta yi ma Hibba vioce da cewa miye take mata dariya saboda Mommy ta yi aure? Abun dariya ne ya faru da za ta ri a mata dariya? Tun Hibba na ganin wasa har Mimi ta maida mgana fa a ta kira Hibba a waya tana gaya mata mganganu marasa da i har tana fa in in abun dariya ne to ta bari in nata Baban ya rasu mamanta ta sake wani auren za ta yi mata dariya ta ji in da da i. Ran Hibba ya aci sukavyi ta gayama juna mgana ita da Mimi a ka rabu ba da i har da su blocking in juna. Hibba ta nata kuka haka Mu'azzam ya dawo ya ssme ta da ya tambayi ba'asi sai ta gaya masa abin da ya faru tun farko sannan ta kunna masa Vioce in Mimi da wayar da su ka yi domin ta yi recording abun dai duk ba da i ya yi ma Hibba fa a me ya sa ba ta ba ta hakuri ba? Ita kuma sai ta ce ita fatan alheri ta yi ba na tsiya ba, saboda dai a kashe mgana ya sa ya kira Mimi da kansa domin ya ba ta hakuri shima ta shafe su ba ta aga wayarsa ba sai ya kira Inna Meri ya gaya mata abin da ya faru, ta ce itama ba ta ma san Mommyn ta sake aure ba tun da daga Binta har Mansoor ba wanda ya fa a mata sai ta ce ya bar mganar a hannunta Mansoor shi zai kashe wannan fitinar. Ta fahimci Binta dai tana kishin Babanta ba ta so auran Mommy ba. Shi ya sa duk rayuwaka suka aci itama kuma Hibba ta na ganin ba wani abu ta fa a ba sai a ka kasa samun fahimtar juna gaba aya. Inna Meri da kanta ta kira Mansoor ta fa a masa abin da ke faruwa ta ara da cewa" Ba ina goyon bayan Hibbatu ba ne, amman zencen gaskiya ta fi matarka gaskiya saboda ita ba ta san abin da ke faruwa ta yi mata fatan alheri, daga karshe sun kasa fahintar juna har abubuwa suka lalace, na so na je na bata hakuri amman sai na yi tunanin ba hurumina ba ne tunda ba ta gaya min ba, ba na so a fara samun baraka daga matayenku saboda in hakan tana faruwa wata rana kuma araka za ta iya bayyana daga bangaren ku, kai ka yi ma Binta mgana ka fahimtar da ita shima Mu'azzamu na gaya masa ya fahimtar da matarsa in an samu daidaito sai su kira juna Hibba ta ba ma Binta hakuri magana ta wuce." Sai Aji ya ce cikin
Chapter 203 · 0% Book details