← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 208

Sashe 28

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka an yaga kaurin cikinta a waje wani irin hayaki yaji kamar idanuwansa na fita na zafin kishi, yanzu maza nawa ne a wannan wajen? In suka kalle mata jiki fa? Kawai sai yaji kamar ya mutu. Ita kuma Mimi kuka ta fashe da shi cikin raunin murya take fa in "Don Allah don Allah Mansoor." Rukkaya ce ta ariso wajenta da gudu ta riketa ranta ya baci cikin masifa ta ce"Mimi me ye haka? Ta ya ya za ki zauna wani wanda bai isa ba yana wulakanta ki haka?. Ya ji ta saboda har ya fara takawa zuwa wajen Motar Mu'azzam sai kuma ya fasa ya dawo da zafin namansa lokacin Rukkaya da wata kawar Bibi sun tada Mimi tsaye sai ya ga ana ganin jikinta, tuni idanuwansa suka rufe yana tafiya kamar ya ji ya tashi sama. Tsabar kishi da ya rufe masa ido yasa bai san lokacin da ya daka mata wani irin tsawa ba. "Ki tsaya anan kar kuskura ki ara taku ko aya FATIMA.." Ya kirata da sunanta da ba kowa ke kiranta da shi ba. Jikinta na rawa ta juya ta lna kallonsa kowa kuma sai ya koma yana kallonsa baki sake hatta ko su Mu'azzam Nasir har sai da ya Murmusa shi fa daman yasan har gobe Aji bai daina son Mimi ba, kuma a kishinta kamar mahaukaci haka ya ke jin kansa. Wajensu ya nuna yana zuwa ya cilla ma Mu'azzam key in motarsa ya ca da sauri, shi kuma sai ya mika ma Ahmad hannunsa da sauri ya ora masa key in motarsa ya juya kamar wani namijin zaki ya wuce wajen motarsa shi duk saurinsa kar Mimi ta juya baya wajen maza su ga jikinta in hakan ta faru ai sai ya kusa mutuwa saboda bakinciki. Rukkaya kuma haushi wannan mulkin mallakan ya kamata a fusace ta ce"Dilla mu tafi yanzu ya gama wulakantaki sai kuma ya dawo ya na ba ki umarni? waye shi Mimi na hawaye ga kuka cikin sauri ta ce"Umarninsa kamar dole ne a gare ni na bi Rukkayya" Rukky ta saki baki galala tana kallon Mimi dai lokacin da Aji ya dawo da wata bakar Jaket baka tana da tsawo nashi ne ta jima acikin motarsa ashe zata yi masa amfani. A gif gif in sa ya dawo gabansu ya saita rigan ya saka a jikin Mimi bai samu salama ba sai da ya ga jaket in ta sauko har ta rufe in da ya yagen sannan ya sakar mata rigan. Bai kalleta ba duk kuwa nacin kallon da take yi masa , ga hawaye a saman fuskanta lokaci aya da wani irin mirmishin da ta jima ba ta yi kamar sa ba. Kamar walkiya ya bar wajen har ya shiga motarsa Rukkaya ta saka hannu za ta warce rigan jikin Mimi tana fadin"Ba za ki saka ba, ya damu da ke ya ture ki, ki ka fa i a gaban jama'u? Gam ko Mimi ta rike rigan idanuwanta da hankalinta na kan Aji da ya shiga cikin mota. Duk da motar ba in gilasai ne jikinta na ba ta ita yake kallo, kamkame rigar tayi cikin Mirmishin dake tafe da hawaye Ta ce"Ki bar min Rukky a kallah bayan tsawon shekaru na kara samun tabbacin matsayina bai sauya ba, yana sona har gobe tunda bai daina kishin wasu mazan su ga jikina a bu e ba" Rukky ta bi ta da kallo kamar mai ta hankali sakinta ta yi ta so ne ta isa wajen motarsa ta zage shi sai dai kafin ta karisa ya fige motar da gudu ya fice daga haraban wajen Rukky ta aga murya tana fadi'n" an wulakanci kawai, za ka ha u da dai dai da kai a gaba kana ba in mutum sai fa in rai da nuna isa aikin banza kawai.". Ranta ya baci ganin gaba aya ya ata musu biki ta na juyawa ta nufi wajen su Usman da kamar an da sa su. Bibi kuma da sauran awayenta sun rufe Mimi suna yi mata sannu. Cikin masifa Rukky ta ce" Usman wannan wani an wula anci ne? A gaban ku ya ci zarafin awata waye shi? Kai tsaye Nasir ya ce"Aji.. MANSOOR IBRAHIM AJI. Gombe State United Captain" A fusace ta wurga ma Nasir harara kafin ta ce"Aikin banza shi ne me? don yana wallo sai ya yi mata wannan tozarcin wallahi ya ci sa'a ya bar wajen nan da sai ya raina kansa wlh." Nasir ya ba ta amsa kai tsaye da cewa" Sai dai ki raina kanki, ke ba ki ga abin da ya yi ma ita awar taki ba ne,? Rukky za ta kara mgana Usman ya tare ta da fa in"Ki yi hakuri Anty Baby ko an yi miki bayani ba za ki gane ba. Aji abokina ne tare mu ka tashi dukkanmu nan tare muke wannan kuma da kike gani aninsa ne Mu'azzam" Ya fa a ya na nuna mata Mu'azzam wanda ya yi shuru kamar ruwa ya cisa. Cikin ufuluwa Rukky ta kallesa kafin ta ce" Miye ha an'uwanka da awata da zai mata wannan wulakanci.? Sai ya kasa ba ta amsa Nasir ne ya ce" Ala ace mai karfi a tsakaninsu ke ba ki gane haka ba? To tsohuwar budurwansa ne bayan wasu shekaru yau suka ha u shike nan kike son ji? Ya fa a ya na mai kureta da ido, ta kasa mgana saboda mamaki dai dai lokacin da Mimi ta kariso wajen jikinta kamkame da rigar da Aji ya ba ta kamar wani zai wace mata. Tana zuwa wajen ta saki baki tana kallonsu cikin mamaki ta ce"Su waye na ke gani haka? Ai baza ta a mantawa da su ba sai ta tuna islamiyan Mallam Dahiru cikin bu e baki tare da murnan ganinsu ta fara nuna su aya bayan aya. "Makama.." Ya amsa mata da" Na'am Mimi" Sai ta nuna Ahmad tana fadin"Ahmad.." Shima ya amsa mata da cewa"Na'am Mimi shekarun da yawa" Sai ta koma ta nuna na kusa da shi "Nasir" Nasir na dariya ya ce"Na san ai ko ba ki gane Nasir don komai ba kya iya gane ni da kullum sai Aji ya yi fa a da ni akan ki. Hajiya Mimi ai ni mun ta a haduwa shekarun baya." "Kin gane wannan?. Ya fa a ya na dafa kafa Mu'azzam sai ta kura masa ido kafin ta ce"Laa wai Mu'azzam ne? an Inna ne ya koma haka? an Innan da ta fa a ya sa suka fashe da dariya shima Mirmishi ya yi kafin ya ce"Anty Mami ashe baki manta da ni ba." Saboda tun a baya baya kiranta da Mimi Sai dai ya ce mata Anty Mami. Farinciiki ya kara cika kirjin Mimi cikin fara'a da tuni ta manta da kukan da take yi ta ce" Mu'azzam ina Inna? fatan tana nan cikin koshin lafiya" Kai tsaye ya ce"Inna na nan lafiya kalau, ina su Hajiya?sai ga shi mun sake ha uwa bayan wasu shekaru a bikin Makama" Sai ta nuna Makama kafin ta yi mgana ya yi saurin cewa"Usman ba wanda ya auri anwar Anty Baby." Mamaki ya hana Mimi mgana sai faman mirmushi take yi, Rukky ta gaji da ganin abun mamaki ta kalli Mimi tana fa in " Duk a ina kikka san su ne wai? Mimi ta ce"Na san su shekaru da da ewa Rukky."Sai ta saki baki tana kallonta ba ta kara mgana ba Dinner ai ta gama rushewa wasu har sun fara tafiya gida tun dare ya yi sha biyu ta wuce. Ita kuma Mimi su Nasir kawai take kallo ta na mamakin yadda duk su ka zama magidanta, tambayansu bayan rabuwa ta fara yi Nasir ke gaya mata dukkansu sun yi aure har Mu'azzam. ta rike baki tana fa in"Muzamman ikon Allah" Sai ta bashi kunya Nasir na dariya yace"Ajin ki ne kawai ya rage gauro har mun gaji da biyan yara suna masa ki an gauran ci." Mirmishi kawai ta yi, amman ta kasa mgana sai ta saki mganar ta kama wata in da take gaya ma Nasir a baya da suka ha u ta kar i lambarsa ta yar da wayarta ne shi ya sa ta rasa lambarsa. Shi kuma Usman na wajen Amaryasa tana kunkuni a zo a kai su gida ita kuma Rukky ta koma gefe tana mgana a waya, Dole dai su Nasir in ne za su maida mutane gida ga shi motoci uku ne a hannunsu tunda Aji ya tafi da ta wajen nashi Mimi ta samu ke ewa da Mu'azzam da Sauri ta ce"Mu'azzam ka bani lambar wayar yayanka mana.". Mu'azzam ya yi shuru ya na kallonta ya kasa mgana ita kuma sai ta yi mirmishin karfin hali kafin ta ce"Ba ka son ba ni ne? Kar ka damu ba zan ce a wajen ka na samu ba." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Ina tsoro ne kinsan halinsa fa, ba ya sauya ba ne in ya ji ni na baki lambarsa tamu da shi za ta yi muni." Da sauri ta ce masa in sha Allahu bazai sani ba. Jakarta ta kar o wajen Rukky ta auki wayarta ta kwafe lambar suma dukkansu ta kar i lambobinsu wannan karon ba za ta kara bari Aji ya su uce mata ba. Ganin dare ya yi ga sauran mutane ya sa Mimi ta ce Rukky ta tuka su da sauran awayen Bibi sai su je ta sauke su, ita sai ta wuce gida domin ba ta gayama Hajiya zata kwana ba. Tare suka bar wajen aya saura na dare suka maida Amarya da tawaganta zuwa gidanta dag nnan Mimi ta ce za ta tafi gida Rukky ta ce ba za ta bar ta ta tafi ita ka ai ba. Za ta rakata sai ita ta kwana a wajen Mimi in. awayen Bibi ma duk nan za su kwana Ango ya yi musu lamuni tunda dare ya yi ga kuma yadda abubuwa suka kasance. Anan suka yi sallama su Mu'azzam ya auke su sauran abokan masu mota kowa ya kama gabanshi, suna tafe a tare motar Mimi na gaba ta su na baya sai da suka zo shatalelen da kowa zai auki anguwar da zai je sannan suka yi ma juna hon su suka auki
Chapter 28 · 0% Book details