Sashe 63
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Meri lokaci aya tana in"Meri har da shi Mansoor in Murja ke son gani za ta sauke nauyin marigayi ne da ta auka." Inna Meri ta yi kasa e kafin ta ja gauran numfashi Ta ce"To sai dai na kirasa a waya Allah yasa yana kusa." Ta fa a lokaci aya tana mi ewa Walida ta ke kira sai taji Shuru sai Mommy ta ce in wayarta taje nema gata nan saman Kujera. Sai ta auka ta shiga ciki da yake Inna Meri ba ta da duhun kai ta iya dubo suna ta yi kira. Baba anjuma ta fara kira ta tambaye shi ko yana ina ne? ya ce ga shi ma a kofar gida sai ta ce ya kariso suna da ba Baban Inna kuma kira byu ta yi masa bai dau a ba tana shirin ijiye wayar ta fito sai ga kiran shi Muryan shi a Cunkushe ya ce mata ya an kwanta ne, ba ji kiranta daga farko ba Itama Innan muryanta a cushe ta ce ya zo gida tana son ganin shi, bai kawo komai ba ya auka ko wani abu ne ya taso, bai ta a tunanin wani abu daya danganci yarinyar da sanadinta mafarkinsa ya ruguje ba. Inna Meri na dawowa falon ta a musu Hajiya ta kira su a waya sai ga Baba anjuma shi tun a waje ma ya ga mota, Gaje ce ta shigo samun ruwa wajen Magajiya ta ga shigowar su Hajiya shi ne ta je ta kira Harira suna ta tsegumin son sanin su waye suka zo wajen Meri masu kudi haka sun tambayi Magajiya ta ce ita bata sani ba, Walida kuma da ta fito sanin halinta yasa ba su tambayeta ba domin su san ba za ta gaya musu ba. Kuma ganin Baba anjuma ya shigo kuma ya wuce bangaren Inna Merin da sauri ya sa su ka san tabbas da wani abu. Kuma suna son sanin abin da ke faruwa amman ba hali ita kanta Magajiya sai tunane tunane take yi Hajiyar ne take ganin kamar ta ta a ganin ta sai dai ta rasa in da ta santa amman acikin ranta tana tunanin kamar akwai wani abu daya danganci zuwan da yarinyar nan mai aiki a gidan tibi ta yi, jikinta na bata kamar taron ya na da alaqa da ita. Cikin girma da arziki Hajiya suka gaisa da Baba anjuma yana zauna a kasa kusa da Inna Meri Mommy ma ta sauko asa ta zauna lokaci aya ta gyara zama Inna Meri ce ta fa a masa matar Marigayi ce shima nan take ya yi mata gaisuwa ta amsa kafin ta ora da fa in" Bisa abin da ya faru shekarun da su ka gabata ne tsakanin yaron ku da ar mu Mimi wanda har ya jawo rashin fahimta abubuwa suka faru da ba su yi ma kowa da i ba, dalilin haka ya sa sai zumunci ma ya yanke gaba aya, saboda kalaman major a kan yaron wajen ku sai dai wallahi tallahi kun ji rantsuwan Musulami Habibi ya rasu ana gobe za mu zo Gambe da niyar ya zo ya baku hakuri ya kuma jemi gafaran Mansoor sai dai Ubangiji bai amince ba yana gangaran mutuwa yana jaddamin wasiyar na nema masa gafara a wajen sa daku iyayensa shi ne naga ya dace na tako da kafata na zo na wakilce sa don girman Allah ku yi hakuri, ku yafe abunda ya faru kuskure ne kuma kowani an adam ba ya wuce kuskuren sa domin tara yake ba mu cika goma ba. Ku duba Allah ku yafe masa tunda ba shi a duniya nan kuma kafin rasuwarsa ya yi nadama matuka har ya so ya nemi gafaran abin da ya faru da kansa." Mommy ta dakata tana sharan walla da gefen mayafinta kafin ta cigaba da fa "Habiba ya cika a gabana sannan da Mimi a bakinsa ku yi hakuri ku yafe masa." Baba anjuma ya yi saurin tare ta da fa in"Haba Hajiya ki daina kuka, wallahi ba komai tun a lokacin mu ba mu ri e ku a ranmu ba mun yafe Allah ya yafe mana gaba aya, shi kuma Allah ya ji an sa da rahma ya sa ya huta." Gaba aya su ka amsa da Amin Inna Meri Ta ce"Ai na gaya ma Hajiya tuni wannan ya wuce a wajen mu tuntuni." Baba anjuma Ya ce"Kwarai ma kuwa kuskure duka aka samu tun a wancan lokacin, rayuwar duka nawa take ma Allah na tuba? Allah dai ya sa mu dace ko da ba ku zo ba ma Hajiya babu komai." Hajiya tace"Hakane mun gode kwarai Allah ya bar zumunci Amin." Mommy kuma kanta na asa Ta ce" Ina son ganin Mansoor domin shima na bashi hakuri." Inna Meri tabce" Yana hanya zai zo in sha Allahu." Sun yi shuru na wani lokaci sai Baba anjuma ya mi e da niyar fita sai Hajiya ta kira shi ya dawo ya zauna. Mommy ta kallah ta ga kuka take yi sai ta girgiza kai kafin ta ce"Meri tun kwanaki na fa a miki kafin rasuwar Kabiru ya janye kalamansa kan Mimi ya ce ya amince in har ta na son Mansoor to a aura mata shi saboda farincikinta" Inna Meri ta yi shuru kafin Ta ce"E, kuma ai tun a lokacin na gaya miki ni ba ni da matsala, in ma da matsala yana wajen Baban inna ne" Baba anjuma Ya ce"Gasikiya sai dai a jira a ji ta bakinsa ko ba haka ba Hajiya? Hajiya tace to shike nan sai a jira in, nan Hajiya ta cigaba da ga ya musu saboda Mansoor har yau Mimi ta kasa kula kowa kuma har gobe yana ranta shi take so farincikinta na tare da Mansoor. Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba domin ta san halin abin da ta haifa shi kuma Baba amjuma kai tsaye Ya ce"Dama mu ba muki ta ba, matsalan daga bangaren kune amman tunda ku da kanku kun amince sai ayi mgana da shi Mansoor in sai muji ko yana ra'ayinta har yanzu, mu namu fatan alheri ne kawai." "Assalamu Alakaimu." Muryan Mansoor ta katse Baba ajuma da zence da ya kwararo, gaba ayansu suka aga kai ya na tsaye a kofar akin bayan ya aga labulen akin, sai dai fuskokin da ya gani ne ya sa bai shigo ba. Biri daman ai ya yi kama da mutum, ya ga mota a kofar gida sannan ya shigo ya ga su Magajiya na binsa da wani kallo ya zo kuma ya yi mummunan gani. Da ga Hajiyar har Mommy ba wacce bai gane ba, shi ya sa ya wani ara ha e rai kamar an aiko masa da sakon mutuwa. okarin ma komawa da baya ya ke yi Baba anjuma ya kira sunanshi ya amsa ya kuma ba shi Umarnin Shigowa. Kamar ma ba zai shigo ba ya na ta tukubiri ya cire takalmin kafarsa ya shigo daga barci ya tashi daga shi sai jallabiya mai ruwan kasa da dogon wando. A kofar akin ya durkusa yana gaida su Inna da kwana bangaren su Hajiya kuma ko kallo kamar ya ga kashi. Su kuma suna ta kallonsa da mamakin sauyawarsa ya kara girma fiye da tunaninsu Hajiya ma ta fi mamakinsa duk ko a baya ta san shi da tsawo amman bai kai haka bu ewa da kiba ba, ita kuma Mommy daman ba wani ganinsa ta yi sama da sau uku ba, ta dai san ya samu bambamci mai yawa tsakanin baya da yanzu. Inna Meri ce ta kalle shi kafin Ta ce"Ba ka ga ba i bane? Ko ba ka gane su ba ne? Kai tsaye ya ce"Na gansu Inna, kuma na gane su." Ya fa a cikin saka mamaki a cikin ganin nasu a gidansu kafin ya cigaba da fa in"Naga kakar Mimi naga mahaifiyarta abun mamaki me ya kawo su? ko sun manta cewa babu sauran wata alaqa a tsakaninmu ne? Ya fa aa ya na mai kallon fuskokinsu aya bayan aya sai kuma a cikin su aka rasa wanda zai fara magana daga Hajiyar har Mommy ya yi musu warjini. Sai Baba anjuma aka bari da rattaba masa bayanin da Mommy ta musu bai ko gama saurara ba ya kausasa murya Ya ce. "Baba." "Baba." Baba anjuma ya amsa da na'am domin shi kanshi yasan akwai rigima. Cikin shan alwashi ya cigaba da fa in" Na rantse da wanda raina ke hannunsa ba zan iya yafe masa. Shari'a da ni da shi sai a gaban Ubangiji." Ya karishe fa a ya na jin wani irin nauyi acikin irjinsa an ma rai na masa wayau bayan an gama tozarta shi an lalata masa rayuwa shi ne za'a zo ana gaya masa mganar banza. Uban kuturu to ya yi ka an ma yana jin Hajiya ta fara masa nasiha tana fa in "Shi kabirun ma ya rasu ba za ka yi hakuri ba? Kai tsaye Ya ce"Kowani mai rai ai mamaci ne, nima wata rana zan mutu za muje gaban Ubangijin da ya yi talaka da mai ku i a gabansa sai ya fitar min da ha ina" Daga nan sai jikinsu ya yi Sanyi Mommy na jin haka sai ta fashe da kuka tana fa in"Wlh ya yi nadama don Allah ka bar komai ya wuce." Kamar a fusace Ya ce" Ba komai ba ne ballantana na bar shi ya wuce, rayuwata gaba aya ne aka lalatamin kinga kuwa ba kamar a bar shi ya wuce ba ne. Akwai hisabi tsakanina da wannan mutumin kuma yadda ya sha alwshin yarsa ta fi karfina nima yanzu na fi karfinta da duk abin da ya ke takaman tana da shi." Hajiya ta ce"Ka yi hakuri ba laifin Binta ba ne, har gobe tana sonka ka amince ka aureta sai ku manta baya ku fuskanci gaba." "Ni ba ni da kudin auranta. Har yanzu ni talaka ne, sannan mahaifina har ya mutu a kauye ne kuma har gobe ni agola ne a gidan nan kinga kuwa har gobe ban chanchanta ba." Ya ba ma Hajiya amsarta sai su ka kasa mgana Baba Damjuma ne ya ce" Mansoor ka yi hakuri ka ji ko! Ko Allah muna yi masa laifi ya yafe mana." Inna