Sashe 105
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baki kafin ta samu damar mgana Mimi ta shige mota tana yi mata dariya. Daga gidansu Rukky gidan su Hibba suka koma, bayan an yi mangriba suka auko Inna Ita kuma Hibba ta ce sai zuwa jibi in an gama watsewa, yau da wuri suka dawo kamar yadda Baba anjuma yace gidan Alhaji Buba ta saka motar ta, tama yin Hon megadi ya leko su ka gaisa sai ta nuna masa gidan wanzamai ta ce daga nan take ita ce za ta rika ajiyan Mota sai ya ce yalla ai ya sanar da shi. Bintu ta so ta ara kwana Inna ta ce ba a gidan nan ba dole anwar naki ta koma gidan ta amman ba haka rai ya so ba. Ranar lahadi Mimi ta samu hutu a gida, ranar kuma Mu'azzam ya koma kano ya bar Hibba anan sai bayan bikin Saddiqu saboda bikin ya kusa saura sati biyu da wani abu Sai yace kawai bari ya barta anan ita da Junior Allah bar shi in ya dawo aurin aure sai su koma tare, ai ko Hibba kamar ta zuba a ruwa ta sha tsabar murna. Saboda tun bayan auran su jaihuwan Junior ne ka ai ta zo Gombe ta jima sai dai su zo su yi kwanaki su koma tare shi ya sa ta ji da i da ya ce ita ta zauna har zuwa a gama bikin Saddiqu. Shi ya sa ana watse biki ranar litini zuwa talata ba i suka koma gidajensu, laraba ta tattaro ta dawo wajen Inna Meri. Ginin Saddiqu tuni ya kammallah fenti ka ai ya rage aiko ma da Auwalu ku i yake yi ana yin aikin, da yake magajiya na yawon fa in shima Saddiqu ar masu arzi i zai aura, Baban yarinyar an kasuwa ne sannan mamanta ma'aikaciya ce kuma ita ka ai su ka haifa mace suna sonta gatan duniya duk a kanta ya are ar nan anguwan Jeka da fari ce. Kuma komai na shiirin biki ba agidan nan suke gudanar da shi ba, Inna Meri ko sau aya Magajiya ba ta ta a ce mata ga wani abu na game da bikin nan ba, Sa anin Inna Meri komai ya shafi ya'yanta da kanta za ta bi Magajiya har aki ta sanar da ita ko da ba za ta nuna maraba da mganar ba, amman ita ta ware ta daga ita sai anta sai su gaje kawai ke shiga da fita, In Inna ta ji wani abu sai a bakin Baba anjuma. Har ta kayan lefe zuwaira ta ha a a can gidanta kuma ko gidan nan ba'a leko da shi ba. Sai dai wa anda aka fa a mawa a suka ri a zuwa can suna gani, Itama Inna Meri abunda ya sa ta sani Mariya a hanyar islamiya ne suna tafiya tare a hanyar makarantar take fa a ma Walida an gama ha a lefen Saddiqu akwatuna niyar suna gidan Yaya Zuwaira sati mai zuwa za'a je a kai. Da Walida ta fa a ma Inna ba ta nuna rashin jin da inta ba, ta shiga har akin Magajiya ta yi mata murna sannan ta saka albarka a ginin da a ka gama. Bu e bakin Magajiya sai ce ma Inna Meri ta yi " Eh gani na yi Agola ma ya samu waje ya kamkame an masu gida na gefe, gwara shima ya zo ya gina ya zauna ko banza yana da gado a gidan." Sai ga Inna Meri ta dawo jiki duk a sanyaye, abun bai yi mata da i ba, har sai da ta yi maganar ta ce duk Baban inna ya ja za mata wannan wulakancin, Bintu da ta zo ta ji labari sai cewa ta yi " Ke ma Inna kin cika abu, me ya kai ki? abin da ba'a so ka ji ba ai sai ka nuna baka sani ba, ko mu da muke yan'uwansa ba'a gayyace mu ba. Nima shekaranjiya ne Jummai ta shigo gidana a bakinta nake ji wai muje mu ga kaya za'a kai ranar asabar kai tsaye na ce mata ba za mu je ba, ai ba'a so mu gani da an so mu gani da an sanar damu takanas in har muna da muhimmanci kenan." Su Yaya Amina duk suna gidan, suma suka ce gaskiya abin da aka yi bai kamata ba, domin ko ankon bikin da suka fitar daga akin Inna Meri ba'a nuna ma kowa ba ashe sun fitar da Atamfa da leshi Zuwaira ce har da matar Auwalu Maryama. Isu isu tare da ya'yan su Gaje da makota da yan garin da suka auka an'uwa sai dangin Magajiyar, Ko Walida da ke karama ba ta ci arzikin a nuna mata ba tunda sun kwa i mariyan ba ta yi mganar da Walida ba. Ankon ma dalilin ganin su Yaya Halima ce makociyar ta awar Zuwaira ce a wajenta ta ga ankon ta ce ba ta san da shi ba kai tsaye ta ce" Ankon gidan ku ne fa? na auran Saddiqu." Sai Yaya Halima ta kasa mgana, Ita ta zo musu da mganar ankon, Bintu ta ce to ba za su yi ba tun da dai haka ne to ko Bikin ma in takama sai su sha zaman su. Inna Meri ta ce" Sai mene? tunda basu saka ku ba ai yan'uwanku ne suna da hakkin ku shiga a yi daku, kar naji kun kara mganar ba za ku shiga bikin nan ba da ku za'a yi komai in sha Allahu." Fa an Inna yasa suk ce sai dai su fito da ankon su na dabam amman ba za su yi irin na su ba, Mimi sai mganar ankon ma ta ji duk da tasan yanayin gidan daman sai a hankali ita kanta ba ta ta a ganin Magajiya ta yi mata dariya ba, in ta gaisheta da yar ta ke amsawa. Mimi suka ce ta za a musu Atamfa, mai kyau da za su yi fitar biki da shi, Bintu ta ce ai su nasu Atamfa ce dole su kuma su sauya taku aka ce leshi Bintu ta ce sai dai su yi material ko shadda. Dakyar aka tsaida shawaran yin Material Hibba daman tana kasuwanci ta saka aka turo mata kaya suka za a, kowacce ita ta biya ma kanta, Mimi ta siya ma kanta tare da Walida ta ce a auko ma Inna Atamfa mai kyau na fitar biki, Bintu ta ce Inna ba ta da matsala tana da Sabbin kayan da ba ta saka ba tun na bikin Yaya Mansoor Mimi tac ce duk da haka dai itama za ta yi sabo, Inna Meri n ta godiya da son barka. A na saura sati aya biki aka kai kayan oefe, Kuma da gaske suke yi ba su gayyaci kowa ba Inna Meri ma tusa kanta ta yi Gaje ta shigo take fa a mata ita kuma ta shirya ta bi Gajen suka tafi tarec daga can gidan Zuwaira a ka je da ita kai kayan, Inna ta so ko Bintu ta zo a je da ita Bintu ba ta ma zo gidan ba ta ce Basheer ya ha na ta fita. Duk da kowa yasan ba ta yi niyya ba ne amman Bashir ba ya hana ta zuwa gida. Kuma an musu sha tara na arziki dai dai da ruwan da aka basu da a ka dawo dashi gidan ba a kawo ma Inna Meri nata rabon ba, kuma har su cincin da su pepe chicken an yi sun taho dashi har da ku i kuma an raba amman ko abunda ba a so ba ta gani ba Walida na ta kufar baki inna Meri ta ce su yi ta kaya ita abun duniya baya gabanta, Cincin kuma ga shi nan har da su cake a akin ta Domin Mimi sauran nata ta kwaso ta kawo ma inna har ya fara daskarewa saboda Ajiya, Aji ne daman ta ijiyema ko zai ba ma abokansa da ta yi masa mgana ya ce shi yaro ne da zai ri a rabon abu? Wannan ai aikin mata ne ta cire shi aciki shi ya sa tattara sauran ta kawo nan akin Inna. Kuma duk abin da ke faruwa Baba anjuma bai sani ba, Inna Meri ce za ta fa a masa kuma ita ba ta da irin wannan, kuma ba ta rike abun a ranta ba ta saka Mu'azzam ya turo ku i Mansoor ma ta ce ya kawo hatta su Amina Halima Bintu sai tace su samu abunda za su ha a auran an'uwan su ne, Mansoor bai cika zuwa gidan ba sai an kwana viyu suna ta shirye shiryen tafiya Ibadan buga wasan Premie League tare da yan kudu za su buga 100k ya ba da Mu'azzam kuma dubu Hamsin. Yaya Amina 10k, Yaya Halima 15k, Bintu kuma da yar ta ba da 5k ba domin ba ta da abunda ya fi haka ba, ta ce ne ba za ta ba da ba, Inna Meri ce ta yi ma ta jan ido ya sa ta ba da dubu Biyar in ma. Haka inna ta ha a 200k cir daga bangaren ta ita da anta ta kai ma Magajiya amman ta kar a ko godiya a wula ance ma kamar daman dolene su ba ta ku i mai yawa haka. A na saura kwana biyar auran Saddiqu bai ko samu dawowa garin ba an ce sai ranar Al'amis, Mimi ta samu wayar Baaba Uwani ashe Hajiya ba ta da lafiya, yini ta yi a asibiti Daddy ne ya zo ya gan ta kwance zazzabi ya rufe ta, tunda daman Mimi ta daina zuwa kai Mota ba ta kara zuwa gidan ba sai dai su yi mgana ta waya. Ranar ma ta na wajen aiki ta kira da safe ba ta auka ba, da rana ma ta ara kira shi ne hankalinta ya tashi ta ji ba'a auka ba sai da ta dawo gida ta Kira wayar Baaba Uwani sai take fa a mata suna asibiti amman ga su za su dawo gida. Hankalin Mimi ya tashi nan da nan ta Kira Mommy ta sanar da ita sai ita kuma ta ce ta yi maza ta shirya ta je ta ga jikin Hajiyan Aji ba a gidan ya kwana