Sashe 132
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da kunya ne? Bintu ta tura baki tana fa in" Inna to ba ki ji abin da yake cewa ba ne, ni zai da ka? To wallahi kar ya fasa." Inna Meri ta ja Bintu ta turata cikin aki har su Hibba ta ce su shige da yaran kar wacce ta sake fitowa, itama sai Baba Danjuma ya riketa ya na neman tura ta cikin akin yana yi mata magiyan ta yi shuru lokacin fa har su gaje sun jiyo hayaniya sun shigo gidan. Amman Inna ta kafe ta ce ita ba fa a za ta yi ba mgana za ta fa a musu sai ya sake ta. Kallonsu ta yi dukkansu kafin ta ce" Ku kwantar da hankulanku zaman Binta a gidan nan tun jiya ya are, ga aki nan ku yi yadda kuke so da shi. an yau ne ka haife shi ba ka haifi halin shi ba, in da ace Baban Inna mai jin mgana ne wallahi da yau ba ta zo ba, amman ku yi hakuri ga aki nan in kuma nan ma bai isa ba, ni ma kuna son na tashi na bar ma shi Saddiqun shashen ne gaba aya sai in ta shi, miye a ciki? Ai ba wani damuwa tunda gidan ubansa ne, ni kuma matar babanshi nake kuma ya fini iko da gidan gaba aya" Da sauri Baba anjuma ya ce" Ki fita ki bar musu shashen? To ban animce ba, ba ke ba ko Manaoor ba in da zai je." Inna Meri ta ce"Magana ai ta kare kuma, ga aki nan zan kira Hajiya su zo su kwashe kayan su, abin duk bai kai na fa a ba." Sai mamaki ya kamasu Baba anjuma cikin mamaki ya ce"Ban gane ba, ina ita Bintar? "Ta na gidan su tun jiya.? "Me ya faru? Inna ta kalle shi lokaci aya kafin ta yi mirmishi tace" Ina ga sun rabu ne." Gaba aya su Baba Sani suka zaro ido, ita Inna Meri aki ta shige da sassarfa Baba anjuma ya bi bayanta cikin mamaki. A ka bar su Magajiya a tsakar gida suna ta magana asa asa. Magajiya ko har dariyan mugunta ta saka da karfi ta ce"To daman ina wannan auran zai yi karfo? An gama karyan arziki ya auro wacce ta fi karfin shi, ai daman hausawa sun ce kwarya ta bi kwarya in ta hau akushi sai ta fashe fasss." Ita dai tunda an ba da aki ta yi wucewarta shashenta tana wa e wa Ta bar su Baba Sani na mganganun su, Gaje ta bi bayanta Harira dai duk ba ta ji da in abin da ya Faru ba,.Haka suka fito suna ta dariyan cewa Daman ai tun farko ya kai kansa in da aka fi karfinsa , Saddiqu ma sai dariyan mugunta yake yi domin ya ce ya na jin haushin Mansoor ya yi ta nuna yafi kowa sa'an rayuwa. A can aki kuwa Baba Danjuma ya tsare Inna Meri sai da ta maida masa abin da duk ya faru a daran jiya. Cikin tashin hankali y ace"Innalillahi! Ban san duk haka ya faru ba, jiya na gaji sai na kwanta da wuri amman Meri me ya sa kika barta ta tafi? Inna Meri ta bar gaban Baba anjuma sai ta koma gaban tibin dake akin tana neman Sigan da za ta saka ma Kuni lokaci aya tana in"me ya sa kuke tunanin zan hana ta tafiya? Shi wanda ya ijiyeta da kanshi muna ji ya ce ta tafi in zai fi, ni kuma a wa da zan ce kar ta tafi,? wallahi na auki Binta a matsayin ata kamar Bintu ko itace Bashir ya yi mata wannan wula anci sai na dawo da ata gabana sannan na saka ya sake ta tunda ba a zaman aure dole ko domin alfarma." Baba anjuma da ya fahimci ranta ya aci sai ya ce"Yanzu Shi Baban Inna yana ina? Inna Meri ta yi masa banza ta duka tana saka ma kuninta siga, sai ya shiga walama Walida kira sai ga ta fito ita da Bintu su yake tambaya Mansoor walida ta ce tun jiya da ya fita bai dawo ba sannan Yaya Mu'azzam ya ce yana ta kiransa bai same shi ba. Baba Danjuma ya fice yana fa in bari ya neme shi ya gani ko zai same shi. Ya na fita Bintu ta ce" Yaya Mansoor bai kyauta ba, ga shi yanzu saboda shi an zo Anci mutumcin Inna" Nan suka zauna suna mai da yadda akayi Inna ba ta saka musu baki ba tana dai ta hidima da yara abin ta, Bintu ce ta kira Yaya Amina da Yaya Halima ta ce su zo gida su dai sun ce in Inna ba za ta saka baki ba su za su saka, in ta kama sai su je su ba ma Mimin hakuri da kansu, tunda Hibba nata kiran wayarta ba ta auka ba,daga baya ma sai su ka ji wayar a kashe. ****** *MANSOOR.!* Tun a daran jiya da ya bar gidan ya isa camp in su domin a tunanin shi anan zai samu natsuwa. Sai dai Ina! wannan natsuwar da ya ke fata ya kasa samun shi, ga adaya ji ya yi kamar ya na cikin nadama wata zuciyarsa tana fa a masa abin da ya aikata ma Mimi bai kyauta ba? A asan ran shi ya ke jin rada in maganganun da ya gaggayamata sannan a cikin kunnuwansa ya ke jin sautin kukan ta, me ya sa? me ya aikata? Menene laifin Mimi da ya ri eta a cikin ransa? In har zai yi adalci da ita da shi duk suna matsayi aya ne a lokacin. Amman sai wata zuciyarsa ke fa a masa abin da ya aikata shi ne dai dai domin duk abin da ya faru Babanta ne sila, kuma ya san duk barazana ce ba za ta iya tafiya ko ina ba saboda ta na son shi, bai ta a tunanin da gaske Mimi za ta iya tafiya ba in da ace yasan za ta su uce masa da bai tafi ba da ya tsaya ya bata hakuri. Ko ya yi tunanin kamar ya tashi ya koma gidan ya ba ta hakuri amman sai zuciyarsa mara kyan ta hana shi, sai yake ganin kamar shi za ta ba ma hakuri domin shi aka fi Sa amawa da wannan tunanin ya sa ya kasa dawowa amman barcinsa rabi da rabi ne gaba aya sai yake jin sa kamar wani mai laifi, yana ji kamar ba shi da gaskiya sannan yana jinsan kamar wanda ya auki wani irin nauyi mai girma a saman kansa. Uwa uba ga kallon da Inna ta yi masa a jiya nan yasan ba shi da bakin kare kan shi, sai kuma ya yi tunanin bai kyauta ba ya fara nadama sai wannan ba ar zuciyar tasa ta rinjayeshi ya ji kamar abin da ya aikata daidai ne, amman kwana ya yi da ya runtse ido sai ya ga Mimi ta na wannan kukan. Da asuba ya kashe wayarsa saboda wata zuciyarsa na zuga shi akan ya aga waya ya kira wayar Mimi ya ji lafiyanta ita kuma wacce ba ar zuciyar nasa na nuna masa shi ne akan dai dai. Saboda kar ta rinjayesa ya kira ne ya sa ya kashe wayar ga adaya. Ranar morning traning gare su sai dai ya wakilta Zinder ya tsaya da su, ya ce ba ya jin da akinsa dake cikin camp ya koma ya kwanta saman aramin gadon yana faman tunani ya yi juyi ya fi sau goma amman Mimi ce a cikin ransa! Ko ya koma gidan ne ya ga halin da take ciki? Ko kuma ya kira ta a waya ne? Haka yake ta wannan tunanin sai ya ji kamar ya amince ya ta shi ya je ya ganta sai wata zuciyar ta ce"Me kake shirin aikatawa? Ai ba ka yi mata laifi ba duk abin daka fa amata gaskiya ka fa "A'a na na yi mata arya, na yi mata karyan cewa ba na sonta ahalin duk duniya duk wata macen bayan uwata da an'uwana su biyo bayan Mimi a zuciyarsa duk saboda ita ne ya koma haka saboda tsananin kishinta da yake yi ne ya sa a tsawon shekarun zuciyarsa ta kasa zama cikin salama a baya yana da tabbacin in da ace Mimi wani ta aura ba shi ba, to ko bai mutu ba sai ya Ta ggayara. Duk yadda da ya so ya manta da abin da ya faru ya asa, sai ya yi tunani ya bari ta huce, amman a ransa yata ta addu'an Allah ya sa ta daina kuka, sai kuma gefen zuciyarsa ta fa a masa Inna za ta lallasheta sannan ga Walida ga matar Mu'azzam ya tabbata ba za su barta ta yi ta kuka ba. Ya yi tunanin ko ya Kira Mu'azzam ne saboda halin da yake ciki a karon farko yana son ya tattauna da wani na kusa da shi Amman sai ya ji ba zai iya yin wannan maganar da Mu'azzam ba, har gobe aninsa ne kuma shi a arami na asa da shi yake kallon sa. Duk wanda tunaninsa ya kawo masa sai ya ga ba haka ba ne. Daga karshe sai ya yi tunanin kiran Ahmad sai kuma ya fasa tuna ya yi nisa, kuma shi ba shi da wasu abokai bayan su, ko zamanin da ya yi karatu ban da gaisuwan nutumci har ya gama bai yarda ya yi aboki ba rayuwarsa kawai yake yi a bangaren kwallo ma sai da yaran dake asan shi da Caach in dake saman shi suma maganar aiki ce kawai a tsakaninsu ba shi da wani sakewa da nutane kuma a wannan halin yana son ya yi mgana da na kusa da shi wanda ya san shi sosai domin yana bukatar ya amsa masa wasu yan tambayoyi. Ya yi tunanin Makama sai ya ga bai san gidan shi ba sai dai gidan Nasir shima tunda da da ewa lokacin ana ginin gidan suka je gidan yanzu ma baya tunanin zai iya gane gida. Duk da ya san iskancin Nasir amman a yanzu ba shi da mafita tunda yana bukatar shi. Jaket in sa ya auka da wayarsa sannan ya ora saman riga