Sashe 147
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ce zai zo fa ki kwantar da hankalin ki, shi ko tunanin tafiyar ne amman haka nan dai ya sauke girman kansa da wannan rikon da ya yi a ranshi a ransa ya kudurta ba zai shiga gidan ba sai dai ya tsaya daga haraba.. Bayan Mu'azzam ba wanda yasan zai je Abuja Jirgi ya bi zuwa can ranar wata Asabar da safe domin ko da sha aya ta yi sun sauka a garin Abuja, a direshin ya nuna ma mai Taxi in sai ga su har kofar gidan Marigayi Major Kabir Dabo dake anguwan Gwamrinpa. Tsawon shekaru goma anguwar ba ta sauya masa a i do ba. Sannan gidan kan shi bai sauya masa, sama da mintina talatin ya na bakin get in gidan yana kokuwa da yanayinsa domin ji ya ke kamar a wancan lokacin ne da suka sauka shi da Mu'azzam kawai sai komai yake dawo masa daki daki kamar a lokacin yake faruwa ya yi tunanin ba zai shiga gidan ba, in fa ana son a samu masalaha har gobe ba zai daina ganin ba in wannan gidan da mutanen dake cikin sa ba. Wayarsa ya auka ya kira Mimi abin mamaki wannan karon Mimi ta aga wayarsa. "Hello, na iso gani a kofar gida amman ki fito ba zan shigo ba." Cikin yanayin maganarta tacce"Ni kuma ba zan iya fitowa ba, in ka na so in saurare ka sai ka shigo cikin gida." A ransa sai ya ji da i da ya ji muryanta amman kuma yana tsoron wani abu da sauri ya ce" Kada ki sake ki shirya wani abu, domin na ga alaman kin sakani cikin dangin ku bangaren abokan wasan ki." Dariya ta saki mai kayatarwa kafin ta ce"Kar ka damu, yi ma megadi mgana ka ce kai ba o na ne." Daga haka ta katse wayar ba karamin jarumta ya yi ba. Har sai da ya kai zuciyarsa nesa sannan ya iya tun karan get in ya buga megadi ya leko sai ya ga yau kam ba Soja, wani dattaijo ya gani bayan sun gaisa ya ce masa ya zo wajen Mimi ne sai ya bu e masa kofa ya shiga amman sai ya ce ya jirasa bari ya shiga ya sanar musu. Yana bin haraban gidan da kallo, ba sojoji ba motoci ba iko ba komai sai haraban gidan wayam, Rayuwa kenan yana nan tsaye ya na kallon abun kamar yau yake faruwa Sanye yake da manyan kaya har da hula saboda Sumar kansa ta yi yawa kuma bai je ya rageta ba. Megadi ya dawo ya ce Hajiya ta ce ya shiga ciki, kamar yace a'a sai kuma ya bi shi a baya shi ya yi masa jagora har cikin falon Gidan da ba abin da ya sauya a sanin da ya yi masa a baya sai dai an samu sauyin abubuwan dake falon. Duk yadda ya so ya zauna kasa zama ya yi kawai ya yi tsaye hannayensa goye a bayansa ya na jinsa kamar akan aya Ita kuma Mommy tana cikin akinta tana fa waya da Mimi domin ita ta kira ta ta ce Aji na waje ta saka a shigo da shi. Mommy cikin fa a ta ce"Au kin ma san zai zo shi ne ki ka saka kafa kika yi tafiyar ki? Mimi ta marairaice kafin ta ce"Ni fa ban sani ba, yau yake gaya min." Mommy ta san karya ne. Rana Tsaka shekaranjiya ta ce Kano za ta je gidan Dr da ta hanata sai ta yi mata karyan kwana biyu za ta yi ta dawo, kuma daman sun yi waya da Hajiya ta san da labarin zuwan shi can gidan da ta kira Alhaji Hamza ta yi masa mganar tun dai ya zo ya neme sa a sansanta lamarin shi kuma sai ya ce har yanzu bai zo gabar da nake so ba, in har yana son Sasanci tsakaninsa da Mimi ya san in da zai same shi. Mommy ba ta fito ba sai da ta kira Asmau a waya dake akin ta ta ce ta fita falo ta kai ma mijin Mimi ruwa da lemu a falo. Da to ta amsa mata sannan ta saka lullu i ta fita falon ta ganshi tsaye kamar yana kan aya ba ta ta a ganinsa ba sai sau aya a wajen Kwallon da aka yi amman ta gane shi. Cikin girmamawa ta gaishe shi ya amsa sau aya kafin ya ce"Ina Mimin? Sai ta yi shuru cikin mamaki kafin ta kalle shi cikin mamakin shi bai san Anty Mimi na kano ba ne? "baka sa ni ba? Anty Mimi ba ta nan ta tafi kano." Mirmishin gefen baki ya yi kawai domin in yace zai ata ransa ya rantse ds Allah sai ta raina kanta ya yarda ma kansa Mimi tana masa wasa da tunani da hankali. Kitchen ta shiga ta ha o masa lemu da ruwa da kofi saman faranti sannan ta kawo masa falon ta ja center table ta ijiye masa, Juya ya yi zai yi tafiyarsa sai ga Mommy ta fito Allah ba domin ta kira sunan shi ba so ya yi ya ficewarsa har shi za a yi ma Iskanci. Dole ya dawo amman tsabar kamar akan aya yake bai ko cire sahu cikin takalmin da ke kafarsa ba, daga gefe ya tsugunna ya gaishe da Mommy kadahan Kadahan ta amsa itama cikin yar sakewa ka "Sannu da zuwa. Ba ku yi waya da Mimin ba ne? Ba ta nan tana Kano gidan Dr." Kawai sai ya samu kanshi da cewa ya kira ta bai same ta ba, kai tsaye Mommy ta aga wayarta tana fa in" Bari na kira ta, ka zauna a kan kujera mana nan ma ai duk gida ne." A ransa ya ce ban ga gida anan ba amman a fili sai ya yi shuru kansa na kasa ya ji Mommy na fa in" Ya ce wayarki ba ta shiga, ga shi ku yi mgana amman ki tabbatar da kin dawo yau ko gobe." Daga haka ta mi e ta isa har in da Aji yake ta mi a msaa wayar hannunta ya amsa ita kuma sai ta koma ciki lokaci aya tana kwalama Asma'u kira. "Wai ke a tunaninki wahala kike son ba ni? Uhm ba za ki iya ba ni wahala ba Fatima, sai dai mu wahalar da juna." Mimi ta yi yar dariya kafin ta ce"Sorry fa, na je duba matar an'uwana ne." "Da izinin wa kika tafi? "Da izinin mijin da zai sake ni kwananan mana." Baki ya bu e kafin ya yi mgana ta yi saurin cewa" Shi ya ce in na ga dama na wuce Abuja ma shi ya sa na tafi." Kai ya jinjina ba tare da ya yi mgana ba Daga can bangaren ta ce"Ko za ka ariso kanon ne? Wlh ina gidan Dr." Kasa ma mgana ya yi, domin ba shi da abun cewa dakyar ya samun bakin cewa" Ki sani dai akwai nauyin igiya uku a kanki, duk wani abun da za ki yi na sa a ma mijinki Mala'iku suna rubuta miki, gwara ma ki sani ba ni kika yi nawa ba kan ki kika yi ma wa." Daga haka ya kashe wayar kawai ya yi shuru ya na furzar da iska daga bakin shi,Da gaske ne Mimi ta fara bashi Wahala, da niyarsa ya yi tafiyarsa amman Mommy ta hana shi tafiya ta ce sai ya tsaya yq huta ya ci abinci sannan, kuma kamar an rufe masa baki sai ya kasa yi mata Gaddama haka ya zauna a falon gidan su Mimi a are. Har Asma'u ta gama yi masa lafiyayyan fride rice da naman kaza an yi Pepe. Da farko ya so ne ko ruwa bai zai sha ba sai ga shi har abincin sai da yaci daman da yunwa ya fito ko karyawa bai yi ba. Ya kusa ma yin abun kunya ka an ya rage abincin sai daga baya ya ri a jin haushin kansa. Karfe biyu da wani abu ya baro gidan, Mommy ta jaddada masa Mimi za ta dawo kuma da kanta za ta dawo da ita gombe, duk da bai wani saki jiki ba amman shi kan shi ya yi mamakin kanshi ko a tarihi bai auka kafarsa za ta kara taka wannan gidan ba, sai ga shi a karo na biyu ya dawo saboda Mimi. Airport ya je ba jirgin gombe dole ya nemi hotel ya kama ya kwana da safe ya samu jirgin Gombe zuwa sha biyu na rana yana gidansa kwance yana tunanin Yadda zai yi ma Mimi rashin Mutumci in ta dawo ba dai shi za ta wahalar ba jiya ba har tana tura masa sako. "Ya gajiyan tafiya? Mommy ta ce yau dai Aji ya ci abincin gidan Major Kabir Dabo. Na yi mamaki warai amman na ji da i. My ex husband." Ko ba Ex ba haka ya rika maimaitawa shi ka ai, wata zuciyar ta ce ko dai ta samu wani da take yi masa haka? Zabura ya yi cikin ta shin hankali, sa o ya tura mata tunda ba ta aga wayarsa. "In na sake ki kina da tabbacin akwai wanda zai aure ki ne a bazawara? Tsakanin sa on shi da nata mimtina hu u ne ta turo masa da amsar da ya kusa barazanar yafiya da numfaahin sa. B"E, mun daidaita da shi, kai ka ai yake jira mganar shi ta je wajen Daddy. Ya na sona sosai domin tun kafin na aure ka ya so ni, sai na za e ka a tunanina kana sona sai daga baya na gane cewa na yi rashin masoyin warai da kaina na neme shi na bashi hakuri. Saboda haka ka sani aurena da kai ya are Mansoor. Ina jiran takardan saki na." Fatima Kabir Dabo. Wannan sa on na Mimi ka an ya rage bai kashe shi da ranshi ba,Allah ne ma ya sa kwanan shi na gaba. Da gaske take yi ta nemi wani namijin? Lalle akwai in duniya na uku matukar akwai wanda ke ganin matarsa da sunan so. *Janafty* *INZB3006* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping