Sashe 16
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mahaifiyarsa ce Mama sai Amaryanta da suke kira da Anty. Gidan Alhaji Hamza Sulaiman Dabo gida ne na rayuwar yan boko, kowa kuma abin da ya ga dama shi yake yi shi ba mutum ba ne mai zama an siyasa mai jama'a, kuma ba shi da takura da matsawa rayuwar boko zallah kawai iyalansa ke gudanarwa. Ko da suka shiga akin Mama Jaheed suka iske kwance kusa da Maman kamar zai koma cikin cikinta. Ga kanwarta nan a cikin aakin amman bai saka shi ya fita ba. Ya juya yana ta magana a waya sai da yabji mganar Mimi da Hajiya ne ya yanke wayar da ya ke yi ya juyo ya na sakin Mirmishi ya ce" "Hajiyata Amaryata." Hajiya ta balla masa harara tana fa in"Ni ai ba na mijin da kai, tafi can solo iyo kullun kwance akin uwa kamar wani jariri, ke Hansa'u hala nono kike ba shi ne? Gaba ayan su ka fashe da dariya shi kuma sai ya hau shafa kansa. Mama ta ba ma Hajiya wajen zama na saman kujera guda aya da ke cikin bedroom in ta. Kanwarta mai suna Hajiya Turai ta kada baki ta ce"Ai Jaheed jin sa ya ke kamar Yaya bata yaye shi ba." Mama ta yi dariya ba ta yi mgana ba, saboda ita macece mai kaunar ya'yanta haka zaka ga ko masu auran in suka zo Jikiko su hau jikinta iyayensu su kwanto kan Jikinta. Ita Anty ma ba ta ta a haihuwa ba sai dai suna zaune lafiya sai dai kishi na halitta. Bayan an gaisa da yambayan jki Mama ta ce ta samu sauki, Hajiya ta ce"Sannu! Allah ya kara lafiya.' Ta amsa da Amin Jaheed kuma kusa da Mimi ya koma ya zauna kamar zai shige jikinta ta yi saurin matsawa kusa da Hajiya Turai daman a gefen gadon ta zauna a kusa da ita. A cikin kunnenta ya yi mata ra a" Me na yi miki ba ki aukan wayata? Mimi ta kalleshi ta na masa inkiya da su Mama sai kawai ya aga murya yana fa in" Mama ga Mmin ba kin ce za ki yi mata mgana ba? Mama ni fa Mimi ta ce ba ta sona me na rasa mene ne bazan yi mata ba in mu ka yi aure? Ya fa a cikin yar shagwa a Mimi kunya ya kamata sai ta yi saurin tashi, Mama kuma idon Hajiya ya sa ba ta yi magana ba sai Hajiya Turai ce ta kalli Mimi tana fa " Mimi miye aibun Son da ba ki son shi? gaye na nunawa daga nan har london? Ta karishe fa a cikin zolaya Mimi ta kasa mgana kanta dai na kasa Hajiya sai Mirmishi ta ke yi ba ta ce komai ba. Baaba Uwani ta ce"Ai daga nan har gaba da london ma Hajiya, wane mutum.." Mirmishi ya yi kafin ya mike ya na fadin"To na rasa me ya sa ba ta so na" Yadda ya fa kamar zai yi kuka, Hajiya ta ta e baki kafin ta ce"Ba dole ta ce bata son ka ba, kana mgana kamar wata mace. Ni kuma Binta na namiji take son aura ba yaron mama ba." Kamar magana ce Hajiya ta sakarma Jaheed in da uwarsa amma sai ba wanda ya nuna Dariya kawai aka yi, sai ya nufi Hajiya zai mata shagwa a ta mike tana fa in"Ni matsa tafi wurin uwarka ita zata iya da wannan lagen wuya naka kamar wata mace mai laulayi." Mimi sai da ta saka dariya shi kuma sai ya tura baki. Hajiya Turai ta ce"Ko dai hajiya na kishi ne." Ta karishe fa a cikin zolaya Hajiya ta wuce gaba tana fa in"Allah ya tsareni ko tsohon mijina Sulainmnu kafin ya bar duniya duk tsufansa ya fi min wannan lange langen an naku. Allah ya kara lafiya Hansa'u Binta mu je ko? Hajiya ta fa a tana kallon Mimi daman kamar akan aya take ta yi saurin fita daga akin. Mama da Jaheed suka biyo bayansu suna fa in" Tun yanzu za su tafi ba za su bari Alhaji ya dawo ba? Hajiya na cigaba da tafiya ta ce"Wani Alhajin kuma? Hamza ko da safe ya zo mun gaisa." Jin haka suka yi shuru Anty jin tafiyar su, ya sa ta fito suka yi sallama har bakin mota Jaheed ya rakasu. Ya za ga ya ta bangaren Mimi cikin yar shagwa a ya ce," In zo gobe? Mimi ta ce"No ina wajen aiki? Da sauri ya ce" Sai na same ki acan mana." Mimi ta yi saurin cewa"A a ka bari in na dawo zan kira ka." Karya wuya ya yi kafin ya ce" Jibi zan koma saboda haka promise" Ya fa a har ya na mika mata hannu sai taki kamawa sai kawai ta girgiza kai kafin ta ce"In sha Allahu zan kira ka." Sai lokacin ya yi mirmishi ya zaga ya wajen da Hajiya ke zaune ya zaro ku i Sabbi daga aljihun Jeans in da ke Jikinsa ya orama Hajiya a saman cinyarta, sannan ya sagala Hannu ya mikama Baaba Uwani nata ta kar a tana masa godiya. Sai kawai ya ce"Baaba uwani addu'a zaki yi min Allah yasa Mimi ta so ni." Baaba Uwani ta ce"Da ikon Allah zata so ka an Alhaji kuma kun bala'in dacewa da juna." Ta fa a tana yar dariya, Jin haka ya sa ya kara dumbuza mata ku i ya mika mata ta kar a tana saka albarka da addu'an Allah ya ba shi Binta. Mimi ta ji hauahi ya isheta ta yi ma motar ta key, ya aga ma Hajiya hannu yana fadin"Amaryata sai na zo, na ba da kudin cefane ba na son gori." Hajiya ta ce"Sai ka zo tunda kana yi da ni ai shik enan Allah ya yi albarka." Yana aga musu hannu har suka bar haraban gidan. Sai da suka hau titi Baaba uwani na dariya ta ce"Dubu ashirin ne an Alhaji ya bani Hajiya" Hajiya ta ce"Kin gode kuwa." Mimi na tuki ba ta ce komai ba, Baaba Uwani na soke kudinta a ha an zaninta ta ce"Binta ina laifin an Alhaji? ga shi an uwanki don Allah ki saurareshi mu yi tuwo na maina" Mimi na jin ta ba ta yi mgana ba Hajiya ce ta ce"Ai Babanta ma ya ce tunda ba ta so a bar mganar, kuma Ya fa a ma Hamza, shi dai yaron ne ya kasa hakura." Baaba Uwani ta ce"Wayyo wallahi ya na son Bintar ki Hajiya ki saka baki ta saurere shi." Hajiya ta ce" Ba ruwana ai ba ni zan zauna ma ta da shi ba, in sun daidaita kansu zan fi kowa murna da haka." Mimi na jin haka ta ka a kai kafin ta ce"Baaba uwani ni fa Jaheed baya cikin, irin jerin mazan da nake son aura ni da shi ba bambamci ya yi ta wani abu kamar ba namiji ba, ko maganarsa irin na mata ne fa ba ki ji ba?. Ta fa aa cikin marairacewa, Baaba Uwani ta ce" kuma fa hakane yana abu shima kamar na mata." Hajiya na dariya ta ce"Ai na matan ne, ko ba ku ga yadda yake nane da uwarsa ba." Daga Mimin har Baaba Uwani sai da suka saka ma mganar Hajiya dariya. Ita kuma ta ce"To ina mamakin yaran zamanin nan, kamar sun fi kowa sanin darajan aya mu namu an ba a ba ne." Mimi na dariya ta ce" Hajiya ta kenan." Hajiya ta yi mirmishi ba ta dai yi mgana ba. Suna tafe suna hira har suka isa gida, ammh sai da suka tsaya a hanya Mimi ta siya kayan marmari saboda na su ya are kuma mai kawo cefanan wannan watan ya yi nu usa ni, daga gidan Daddy ne kila gobe ko Jibi za'a kawo kayan abinci da cefane. Washegari kafin Mimi ta je wajen aiki Rukky ta dameta da kira dole ta shirya ta fita gaba aya, ta fara biyawa ta gidan su Rukky sannan da la'asar ta tafi wajen aiki, rigimar Rukky ce da ba ta karewa. Dole wai sun shiga bikin anwarsu sun yi kane kane, to ya ta iya? In bata saka kanta ba, nacin Rukky ka ai ya isa ya hanata barci cikin salama. ***** *7rd March, 2022* 11:40pm akin Inna Meri cike yake da ba i mutanen Kano ne suka zo garin tn jiya Mu'azzam da matarsa Hibba da ansu mai sunan Baba Danjuma suna kiran shi Junoir. Anty Amina itama tun safe ta zo ita da nata gayyar an, sai kuma Bintu tare da an biyunta. Sai Anty Halima itama da nata gayyar ayan. Sai Hibba da Walida sai Mariya a akin Inna Meri ya cika da hayaniya, ita kuma daman abin da take so kenan..ta yi nan ta yi nan duk domin ta ga ta farantama anta da jikokinta da suke tafe bin ta wannan ya ce Inna zan sha tea sai wannan ya ce Inna zan sha ruwa. Uwayensu na zaune ita ke tsaye kan kafafunta a kansu. Iyaye nasu na zaune suna hira suna dariya. Magajiya na tsakar gida tana shanyan yan kayanta da ta wanke sai kwafa take yi, bakin ciki ya kusa kasheta in ta jiyo shewan an Inna Meri daga bangarenta. Gaje ce ta shigo daga bangaransu da botiki a hannunta duk da an raba ofa amma itama jin hayaniya ya sa ta wanke wasu kaya ta shigo shanya domin ta ji gulma. Tana ganin Magajiya na shanya sai ta wayance da cewa"Au ke ma wanki kika yi, nima tun safe na ke wanki igiyan can ya cika sai na ce bari nazo na shanya anan." Magajiya ta ta e baki kafin ta ce"Nawa ba su da yawa, ki shanya daga gefe." Daga haka ta cigaba da shanyanta tana tsaki ita ka ai. Gaje ta zo ta fara shanyanta lokaci aaya ta na nazarin Magajiya kafin tace" Hala mariya ba ta gidan ne? Magajiya kamar ta na jira ta fara fa in" Ta na nan, ammh ta na akin uwarta Meri tunda taji zuwan su Amina da safe.". Gaje ta rike ha a kafin ta ce"ashe su ne su ka zo shi ya sa na yi ta jin hayaniya, ke ko dan'uwansu ya zo mana jiya mun