← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 208

Sashe 181

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mimi ta yi kamar za ta yi kuka har ga Allah ita ba ta saka ran komawa a ranar ba, Kawai sai ta ji ya na rage murya har ya na fa in" kin manta ma jibi za ki koma wajen aiki? Gwara ki zo mu tafi kin ji ko? Cikin shagwaba ta ce"Su Bintu fa da Anty Halima? Kai tsaye ya ce" Ina ruwan ki da su? Sun fi ki sanin hanya in sun gama bikinsu za su dawo ke dai ki je ki auko jakarki mu ta fi kada mu yi dare a hanya." Mimi ba ta da wata mafita dole, ta juya za ta koma cikin gida amman kuma sai ta rasa abin da za ta ce musu kawai sai ta ce za ta bi miji su koma gida? Sai ta dawo ta na ce masa" To ni me zan ce musu? kawai sai nace musu zan bika? Kallon sama da asa ya yi mata kafin ya bu e mota ya shiga lokaci aya yana fa in" To shike nan sai ki zauna." Ya fa a a fusace dole ya sa ta koma cikin gida ta samu Yaya Halima ta gaya mata ita kuma sai ta yi dariya kafin ta ce"Ki bi mijin ki Mimi ai an gama biki, mu za mu zauna har zuwa jibi kada ki damu." Yaya Haliman ce ta sanar ma mutane tafiyar Mimi ba wanda ya damu da tafiyarta Maman Bauchi har waje ta raka Mimi da abun arzi i na jaka da kofunan biki da za su raba, ko Bintu ba ta samu komawa ta yi ma sallama ba suka auki hanya. Aji ke tuki Nasir na gefen bangaren mai zaman banza, ita kuma Mimi tana baya ta na ata rai. Shi ko Aji sai ya basar da ita ya koma suna ta hiran su shi da Nasir. Suna hanyar Rukky ta kirata cikin damuwa tana tambayanta ina ta je ta zo gidan ta bata nan? Mimi tace ba ta nan ta je Bauchi amman yanzu tana kan hanyar dawowa. Yadda ta ji muryan Rukky a sanyaye ne ya sa ta ji jikinta itama ya yi sanyi har sai da ta ce" Me ya faru Rukky? Daga can bangaren Rukky ta ce"Bakomai sai dai kin dawo in." Daga haka sai ta katse wayar sai abun ya ba ma Mimi mamaki kamar ta yi ma Nasir mgana sai kuma ta fasa ta bari gwara sai ta koma sai ta kira Rukkyn su yi mgana. Wajen mangariba suka isa Gombe sun biya gida sun sauke Nasir, wani abun mamaki ita dai Mimi ba ta ga ko sau aya sun yi waya da Rukky ba ahalin kuma ta san a baya ba haka suke ba dole ta fara zargin akwai wani abu a asa. Haka suka isa gidansu Mimi na shan kamshi, Aji kuma sai ya nuna kamar bai gane ba ya na ta iban ta da mgana ita kuma ta na basar da shi, kuma duk gajiyan nan haka ya saka ta sai da ta yi musu girkin dare ya je ya siyo amman ya ce shi wlh ya daina siyan abinci yana magidanci har da cewa zai taya ta amman kuma ban da auko miko ba abin da ya yi mata. Sai juya kayan miya kawai ko greeting cewa ya yi baya son hannunsa ya ta a ya ji, ganin da ta yi duk fushin da ta ke yi bai gane ba dole ta saki fuska kamar komai bai faru ba. Daman ya gaya mata ranar litini zai yi tafiya shi ya sa a daran dai kamar in ya tafi ba zai dawo ba. Da kuma safiyar ranar suka tashi da wayar Inna da labarin rasuwar aninta Tanimu, saboda haka za ta jima tunda yanzu sai bayan an yi bakawai, duka dai yaran sun kirata sun yi mata gaisuwa ya yi nisa ba lalle ace sun tashi daganan zuwa can shiyar sakoto ba. Ranar lahadin a gida suka yini washegari litini kuma tun safe su Aji suka kama hanyar katsina tare da sauran team in su, Mimi dai ta sha dokoki kada ki yi kaza kada ki yi kaza, har sai da ta gaji da amsawa da To, shi dai ta kular masa da kanta da gidansa, itama ranar a wajen aiki ta yini ba kuma su ha u da Rukky ba an ce ta zo ta fi daga baya ta kuma kira wayarta ba ta same ta ba, Bintu ta kirata ta na masa tsiyan shike nan sai ta gudu ta bi mji tana ta dariya nan take gaya mata suma ba su da e da shigowa garin ba, an ba su kayan fulawanta gobe Bintun ta ce za ta zo ta kawo mata. Suna cikin wayar ne ra ga madiha na ta kiranta bayan sun gama sai ta kira ta wanda tun bayan tarewanta sau aya suka yi mgana nan ta ke gaya mata ta shigo garin tana gidan Hajiya ta na so ta zo ta ga gidanta amman Hajiya tace ta yi tafiya sai ta ce mata ta dawo tun shekaranjiya tana wajen aiki amman in ta ta shi za ta biyo ta gidan Hajiya. Haka ko a ka yi da gidan su Rukky ta so ta wuce amman zuwan Madiha ya sa ta fasa, o ta turama Aji kan cewa Anty Madiha ta zo za ta biya ta gidan Hajiya, da yamma ta je ta iske ta ko a gidan hajiya kamar ita ka ai ta zo ba yara ba mijin ta ce wasu kaya ne suka kawota za ta arisa Abuja ta ga kayan da ganan ta ga Mommy, sun gaisa sama sama kamar yadda suka saba Madiha sai wani are mata kallo ta ke yi asa asa ita dai a dole sai ta samun abun kushewa sai kuma ga shi ta kasa samu. Duk Mimi na kallonta a ranta tace mai hali dai baya fasa halinsa, amman sabo da ta kure Madihan ya sa ta ce mata ta zo su je gidanta ta kwana. Cikin mamaki ta ce"Gidan ki kuma? Shi mijin na ki fa? Mimi ta ce"Ko ya na nan akwai akuna, balle ma baya nan sun tafi katsina buga wasa." Hajiya na gefe ta ce" Ai ko dai ki je ki kwana gidan ar'uwan ki Madiha." Sai ba ta yi gaddama ba. Bayan sallar Isha'i Mimi ta auke ta a motar ta zuwa gidanta Madiha ta sha mamaki domin duk kyan gidan a hoto a fili ya zarce tunaninta. Acikin bedroom inta ta sauke Madiha ta kuma tu e tana ta hidima da ita abincin ta yi musu mai rai da lafiya suka ci suka sha ruwa. Vduk kushe irin na Madiha ta rasa abun kushewa sai bin ko'ina ta ke yi da kallo, ta na gani Mimi na waya da Aji bayan ya sanar da ita sun sauka lafiya, ita kuma sai take gaya masa ga Yayarta ta zo. Kai tsaye ya ce"Wacce daga ciki? Ta kaduna ko ta Lagos? Sai tace masa da ta Lagos abin mamaki sai ya ce ta bata wayar su gaisa, a karon farko Madiha da Mansoor Aji suka gaisa cikin girmama juna sannan suka yi sallamam Da dai Madiha ta rasa abun cewa sai ta bige da fa in" Ina fatan dai kuna nan zaune lafiya ko? Mimi ta ce mata suna nan lafiya kalau. Sai Madiha ta gyara zama lokaci aya tana fa in" To gwara dai haka, kar dai ki zauna soyayya a namiji ta rufe miki ido, duk da kina aiki ya kamata ki fara tunanin fara wani kasuwancin da ku in ki." Kai tsaye Mimi ta ce"To zan yi magana da mijina in sha Allahu." A karkace Madiha tace"Mijin ki? Au daman ku in shi ne? Mimi ta ce"Ku ina ai ku in shi ne tunda ina arkashinsa, ko Mommy ma ta ce duk abin da na gada nawa ne, kada na kuma zartan da wani abu ba tare da na shawarci mijina ba ko a addinmun hakan ba laifi ba ne, kada kuma ki manta ko yau na fa i na mutu abin da na tara rabi na shi ne." Sai Madiha ta kasa mgana saboda ta ga kamar Mimin ta fi ta gaskiya. Da yake ba wata sakewa tsakanin su ya sa ba su jima suna hira ba suka kwanta sai da eafe Khadi ta kira Mimin ita ke gaya mata Madiha a gidanta ta kwana kai tsaye Khadi ta ce"Mimi na ji kun fara yawon honneymoom ke da mijin ki, Kaduna ba ta zo muku a layi ba ne? Mimi na dariya ta ce"Ta kusa zuwa layi in sha Allahu." Khadi na dariya ta ce" Yauwa, don Allah ku zo mun nima muna da wajen kwana ko wata ne ma za ku iya yi." Da haka suka rabu bayan ta ce ta mi a ma Madiha wayar nan ta bar su suna waya ita kuma ta fita zuwa kitchen. Tare suka fita Mimin ta sauke Madiha a gidan Daddy za ta gaishe shi itama ba ta tsaya ba ta wuce wajen aiki, tana zuwa bayan ta gama karanta labaran safe ta karisa bangaren su Rukky ta same ta ta zo aiki amman duk ta fa a ta yi wani iri kamar Rukky ba, Mimi ta damu ta kalli Rukayya lokaci aya tana fa in"Me ke faruwa ne? Kin ga yadda kika wani lalace? Kuma kin ce za ki zo gida ki same ni kuma ban gan ki ba." Sai Rukky ta furzar da numfashi kafin ta ce" Ki bari in muka tashi mu je gidanki mu yi magana, nan ba wajen mganar nan ba ne." Da haka Rukky ta samu kan Mimi ta yarda sai sun ta shi aiki za su tafi gidanta su yi zauna su yi mgana. Da wuri suka baro ma'aikatan na su ita da Rukky suna tafe ne amman ba wani mganar da ke shiga tsakanin su, Rukky ta yi tagumi daga ganinta tana cikin dqmuwa Mimi dai ba ta ce mata komai ba amman tana tuki tana kallon Rukky cikin tausaya ba aramin abu ne zai saka Rukky ta zama haka ba, ta ma fita surutu fa amman ji ta ko mgana mai karfi ba ta son yi. Sun isa gidan amman ko ruwan da
Chapter 181 · 0% Book details