← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 208

Sashe 30

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafin Ajali ya riske shi bakinsa ya yi nauyi amman kalaman Hajiya sun zaburar da shi lokaci ya yi da ya kamata ya gyara abunda ya ata shekaru goma da suka gabata. Tabbas Mimi zata samu farinciki ba zai zama uba mai hana arsa nata farincikin a saman na shi ba, kafin ya bar duniya zai yi ma Mimi abinda zata dauwama tana tunawa da shi ko bayan ransa. Mommy na sharan jawaye a fakaice ta zari tissue ta na goge masa hawayensa cikin karfin Hali ya rike mata jannu da hannunsa na hagu da ya ke motsawa ta kasa kallonsa shi kuma so ya ke ta kallesa amman ta kasa saboda kukan da ke cin ranta. Kowacce uwa tana son ganin duka rayuwan a'yanta ya inganta, amman ita a cikin anta akwai wacce ta ke cikin rayuwar rabi farinciki rabi damuwa. Ta san Mimi ba za ta manta da yaron nan cikin sauki haka ba, ta kuma san shi saboda shi ne ta ke zaune har yau ba ta yi aure ba tunda ba ta rasa manema ba ne. Tun a lokacin ta san ba'a kyauta ba, amman ba ta da wannan ikon na fa in haka mutumin da bai ji mganar mahaifiyarsa ba ita din banza ya ji nata. Cikin aryewan murya ya ce"Murjanatu ki ago ki kalleni don Allah." Dakyar ta dago ta kallesa sai sharr hawaye shima hawayen ya ke yi da karfi ya kamkame hannunta kafin ya ce"Ki yafe min nasan ke ma na cutar dake, amman ki sani na yi nadama tuntuni nauyi da kunya da rashin sanin ta inda zan fara suka hanani mgana amman tun da Hajiya ta nuna min hanya in sha Allahu zan gyara kuskurena Murja." Mommy ta kalleshi cikin mamaki kafin ta ce"Da gaske Habibi? Sai ya jinjina mata kai kafin ya ce"Ki kira Dr ki fa a masa ya zo ina son ganinshi, zan saka ya san yadda zai yi a tafi dani Gombe zan roki gafaran Hajiya da Mimi sannan zan saka a nemo wannan yaron na rokesa gafara na kuma roke shi ya auri Mimi saboda farincikinta, na kuma yi alkwarin yin azumi uku na kaffaran rantsuwan da na yi." Da sauri Mommy ta Rumgumeshi tana Fadin"Thank You Habibi Allah ya baka lafiya, yanzu kuwa zan kira Sulaiman Mimi za ta samu farinciki itama." Yadda ta ke murna ne yasa ya san ya jima ya na danne mata Hakkinta a matsayinta na uwa. Ashe abun na damunta acikin ranta ba taa ta a nuna masa ba. A gabansa ta kira Dr Sulaiman suka yi mgana ta kuma ha asu shima ya gayamasa ya yi musu bucking din jirgi zuwa Gombe. Cikin mamaki ya ce"Me ya faru Abi? Kai da ba ka da lafiya in Hajiya ce sai a kirata ta zo ta ganka." Cikin muryan ciwo yace"A a ni zan je da kaina gafaranta zan nema Dr. kuma ina son na gyara kurakuraina na baya." Ba shi da abun cewa illah ya amsa da zai yi musu bucking din jirgin Mommy ta ce kar ya damu ba sai yazo ba, ita za ta iya raka Abin har Gonbe kuma ta bashi duk kulawan da ya dace. Ba ta kuma yi maaganar da kowa ba har su Hajiya ba ta kira ta ce ga yadda suka yi da Abi in ba. Sun dai yi waya da Mimi da ta tashi barci ta ji muryanta duk ya dishe alamun kuka sai ba ta neme ta da mgana ba, ballantana ta nuna mata sun yi mgana da Hajiya Abi ta tambaya Mommy ta ce mata ya samu barci saboda ba ta so ta ha asu ya yi mata wata mgana. Farinciki ta ke ji acikin ranta yau ko da ba wani abu a kallah ya sauke nauyin cin zarafin mutanenan da ya yi abu sam bai yi da i ba. *****. *Washegari.* 8:45pm. Mu'azzam bai samu tafiya ranar lahadi saboda sanda suka koma gidan Aji a daran jiya baya gidan Allah ya sa Mu'azzan akwai key in gidan ajikinsa da shi suka yi amfani suka bu e gidan suka shiga suka kwanta.. Har safe suna ta kiran wayarsa bai auka ba sai da rana Mu'azzam ya je Studio in su ya same shi. A camp in su ya kwana sannan ya ki ba ma kowa damar da zai tattauna abin da ya faru jiya da daddare. Hakanan suka je suka raka Makama ango gidansa Nasir ya wuce gidansa Ahmad ma ya wuce gidansu gobe da Asuba zasu kama hanyar Mu'azzam zai rage masa hanya zuwa Kano daga nan ya samu motar kaduna. Mu'azzam ya zo ya na ba ma Inna labarin abin da ya faru ta ri e ha a tana fadin"Allah Sarki Bintar Hajiya ashe ba ta manta da ni ba" Mu'azzam yace"Wallahi Inna sai da ta tambaye ki." Inna ta yi mirmishi itama tausayin Mansoor da Binta na cika ranta. Kafin ta ce"Bakomai an Inna, komai ya yi zafi maganinsa Allah zai huce ka ga ya dawo da kanshi." Mu'azzam ya ce"Inna har yau Yaya Mansoor na son Anty Mami ni nake a miki haka." Inna ta ce" Har gobe ma Mu'azzamu, yana nuna cewa ba ya ta ita ne yanzu amman arya yake yi duk wannan abubuwan da ka yana yi saboda ita ce kuma ina mai rantse maka in ba ita ya aura ba da wahala Baban Inna ya yi aure saboda ba zai iya zama da kowacce mace ba sai ta." Mu'azzam yace"To inna ba za a iya yin wani abu ba? Haka za'a barshi ya karar da rayuwarsa cikin kunci? Inna Meri ta yarfa hannu kafin Ta ce"Me zan iya yi a kai Mu'azzamu ban da addu'a? A gaban ka mahaifin yarinyar nan ya ce mu yi masa tsakanina da iarsa, shima kuma kana ji ya rantse sai dai ya mutu bai yi aure da ya aureta , ni na rasa wannan bakar zuciya irin ta Baban Inna da kafiya da riko, rikon da yake ma abun a ranshi ne yasa ka ga duk ya koma haka" Mu'azzam kamar ya yi y kuka ya ce"Inna ni dai in har an'uwana zai yi rayuwar farinciki zan nemi Anty Mami mu yi magana , zan koma gidansu a Abuja na roki mahaifinta ya bari Yayana ya auri arsa ko da zan mallaka masa duk abin da na mallaka ne." Da sauri Inna Meri ta ce"Kul kar ma ka fara, ka san ai kun gwaada haka a baya komai ya lalace. Ko ka je ya amince ya janye maganarsa ya za ka yi da Baban Inna? kana tunanin shi taurin kansa da wannan bakar zuciyar zata barshi ya yafe ne ya amshe ta ko da ya na sonta? Ai ya gwammace ya mutu da wannan bakinciki akan dai ya yafe abunda ya faru ya nuna ya na son yarinyar nan har yanzu, ai gani zai yi kamar ya ragu bakar zuciyarsa ba ta kitsa masa abu mai kyau a kan rayuwarsa addu'ata kullum Allah ya saussauta masa wannan ba ar zuciyar." Inna Meri ta karishe tana fashewa da kuka Mu'azzam sai ya koma yana ta lallashinta amman shi kanshi kamar ya yi kuka. Allah yasa Walida ba ta nan tana Gidan Bintu can za ta kwana. Asuban ci zai yi na tafiya shi ya sa ma a gida ya kwana akin Saddiqu, saboda Mansoor dai ya yi ma gidansa ya ji ba zai ji da in kwana shi ka ai ba. Amman ya kwana tunanin mafita a daran kuma ya kira wayar Anty Mami ba ta auka shi dai zai kara kutsa kansa cikin wata kasadar a karo na biyu mai kamceceniya da kasadar da an'uwansa ya kutsa kanshi a karon farko a shekarun baya. Ko ka an ba su Bari Baba Danjuma ya fahimci akwai matsala ba Saboda kada su aga masa hankali. Amman fa ya fahimci daga Inna har Mu'azzamu yanayin su ba da i sai ya dauka saboda tafiyar Mu'azzamun gobe ne Tunda an inna ne in ya zo uwar tasa ba ta son ya tafi. Mu'azzam ya yi ta tufka ya na warwara, sai dai abu aya ya kashe masa gwiwa da ya tuna Nasir ya gayamasa an taba hira da ita acikin labarinta ta ce mahaifinta ya yi hatsari ba shi da lafiya? Abin da bai sani ba shin ya na nan a raye ko ya rasu? Amsar da ya kasa samu har suka bar garin a mota ma ya ke tambayan Ahmad yace shi ba'a garin ya ke ba wlh bai sani ba sai dai ya Kira Nasir din ya ji ta bakinsa tunda yana garin zai iya sanin wani abu. ***** 30 April 2022 Yasan Mu'azzam ya bar garin duk ba su yi waya ba, saboda yasan yanayin aikinsa ba zai jima ba. Sai da a daran ranar litini ya koma gidansa daman baya son lokacin da zai samu ka aicewa wani na gefensa. Tun ha uwarsa da Mimi bai ara barci cikin salama ba. Ya ji ya tsani kanshi ta yadda har gobe zuciyarsa ba ta daina son wannan yarinyar da yake ganin bakinta fiye da kowa a duniya ba. In da ya san yadda zai iya ciro zuciyarsa ya ciro son ta ya jefar ya maida zuciyarsa da ya yi haka domin ya cigaba da rayuwa cikin salama.. Tun da alaqan ta yanke bai ta a kwana ya tashi bai tuna da ita ba, Soyayarta da kishin ta suke kara wahalar da shi. saboda ita ya kasa kallon ko wa ta a mace da sunan so, saboda ita ya kashe maganar aure acikin zuciyarsa gaba aya rayuwarsa ta zama kamar mattaciya saboda cutar da zuciyarsa take ciki. Kwance ya ke a tsakiyar falon sa, a saman cafet ya y filo da hannayensa idanuwansa suna Rufe ne amman yana fuskantar POP n da ke falon. Bashi da riga daga shi sai aramin wando sannan babu nepa falon ya yi duhu Tunani yake yi, tunani mai zurfi kamar a lokacin haka ya ke ji amon kukanta na shiga ransa, shi ya yi mata tsawa ya saka ta kuka amman ba ta kaishi shiga bakinciki ba. Allah ka ai ne ya kaisa in da za shi lafiya a ranar yana tuna kukan da take yi da yadda ya ture ta.
Chapter 30 · 0% Book details