← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 208

Sashe 21

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI 08066726866 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z *Page 7* Kofar ya urama ido wasu shu un al'amura da suka wuce a baya suna gilma masa, in hasashen sa ya zama gaskiya Mansoor bai manta da Mimi ba har kwanan gobe tana cikin ransa kuma saboda ita ne har gobe ya kasa iya kula kowacce a mace. Shi da kuma ya yi rantsuwan ko zai mutu bai yi aure ba, ba zai ta a auranta ba kuma ga shi har gobe yana sonta shi kam ya rasa ta in da zai saka tunanin wannan al'amarin. Komawa ya yi ya kwanta yana wasu tunane tunane, shima tun bayan abin da ya faru ba su kara ha uwa ba shi daman ya bar Gombe ya koma Kano. Nasir dai kwanaki can da jimawa ya ce sun ta a ha uwa har ta kar i lambarsa to ba ta ta a kiransa ba shima kuma daman itace ta kar i Layin nashi shi bai kar i nata ba sai dai suna ganinta a akwatin talabijin in, tunda tana aiki a sananniyar gidan talabijin sannan ta yi suna kowa ya santa. Shima dai yana ganinta lokaci bayan Lokaci in yazo garin a tibin Inna in Walida ta kunna, Mansoor ne ba shi da wani masaniya a kanshi sanin shi fa ba ka gane gabansa ballantana bayansa to kila har gwara shi ya kan tsaya su yi magana mai tsawo, wasu tuni ya yanke wannan alaqar a tsakanin su. Bai ta a tunanin haka soyayya ke da zafi ba sai akan Mansoor a lokacin ma daga shi har Mimi suna da karancin shekaru shi ya auka a shekarun da suka auka ba sa tare soyayyarsu za ta disashe ashe ba haka ba ne, tana nan ta kara girma ne acikin zukatan su. Ba zai ta a man tawa da ciwon da Mansoor ya kwanta a lokacin ba, da kukan da ya ri irjinsa yana yi ba, bqasonta yake yi ba kaunarta yake yi sannan sun shaku sosai soyayya ta rufe musu idon da suka kasa gane bambamcin dake tsakaninsu har sai da komai ya kwa e sannan Mansoor ya fahimci abin da aka jima ana nuna masa. Tun Mu'azzam na zaman jiransa har barci ya aukesa Mansoor bai fito daga tiolet ba. Sama da awa aya sannan ya fito daga cikin tiolet in jikinsa na faman igan da ruwa. Tsaye kawai ya yi a tsakiyar falon ookaci aya yana mai har e hannayensa a saman irjinsa. Mu'azzam yake kallo yana barcin sa cikin salama da kwanciyar hankali ba shi da damuwan komai a cikin zuciyarsa. Yana jin dama shima haka yake ba shi da wata damuwa. Dama shima zuciyarsa ta sauke wannan nauyin abin da ya tokareta shekaru goma ya yi rayuwarsa cikin salama ba tare da damuwa da tunani ba. Duk lokacin da ya tuna abun sai ciwon da ke kirjinsa ya dawo sabo, saboda ita ne har gobe ya kasa kallon wata a mace da sunan kallon soyayya. Saboda ita ce ya ji aure ya fita kansa kwata kwata ya ji a duniyan nan ba zai iya zaman aure da wata mace ba. Saboda ita ne ya sauya rayuwarsa da ga mai yawan hira da son mutane zuwa wani mutum mai son ka aici da son zama shuru, Saboda ita ne ya ji ya tsani masu kaki gani ya ke yi dukkansu haka suke marasa adalci da sanin arajan an Adam. A lokacin baya da ita ya yi mafarkin kasancewa har karshen rayuwarsa. Shi fa mafarkansa gaba aya ko aya bai cika ba, duka ya rasa su sai wasu ya gina sabbi acikin duniyarsa. _*Bai tab'a tunanin Soyayyarsa da MIMI akwai wasu tarin bambamce bambancen da mutane ke hango masa wanda shi nashi hangen bai ta a kawo masa ba. Ya auka ita soyayya babu ruwanta da bambamcin jinsu ko hallita, ba ta kuma duba dukiya ko launin fata, ba ta kallon ilimin mutum ko kuma nasabarsa, ita ba za an chanchanta take yi ba, ba kuma ba tasan ya kamata ba, in da ace Soyayya ta san ya kamata da tun farko yin soyayya da FATIMA SULAIMAN DABO bai kamace sa ba*._ _*A iya hange hangensa bai ta a hango bingiren rayuwarsa ba tare da Mimi ba, sai ga shi rayuwar ta lula shi wata duniyar da babu Mimi a cikinta ta ace daga cikinta, shi ya saba mafarkan ga shi ga Mimi tare da kyakyawan ya'yansu da irin yadda suka gina kyakyawan rayuwarsu, ashe ashe matacaccen mafarki ne ba zai ta a tabbata ba.Hannunsa da ya kasa CIZAWA shi ya kai sa ga duniyar da ya zama sai shi ka ai babu MIMI a cikin ta. Ta yi nesa da duniyarsa domin tarin bambamci tare da tazara mai kimanin kilo tamanin da Ahalinta suka hango tsakaninsa da ita wanda shi nashi hangen ya kasa hango masa, saboda tarin soyayya da ta rufe masa jin sa da ganinsa a lokaci aya.*._ Kirjinsa ya fara tasawa yana faman sama da asa, yaji kamar iskar akin ya fara yi masa ka an sai kawai ya bu e kofa ya fita zuwa falo ya goya hannayensa a bayansa ya fara tafiya yana zagayen falon gaf gaf! ana jin karan takun sa da karfi kamar wani namijin zaki. Zuciyarsa ke zafi tana wani turiri daga ciki iskar bakinsa yake fitarwa ya na jin zafin har a saman fuskarsa. Ba zai ta a mantawa da tun a lokacin baya Nasir ya ta a so ya ankarar da shi bai saurareshi ba, ba laifin shi ba ne soyayya ce ta rufe masa ido da ya kasa hango wannan bambamcin dake tsakaninsa da Mimi sai daga baya. _Aji tsakani ga Allah yarinyar nan ta fi arfin ka, naga kana sonta da yawa kar nan gaba iyayenta su hana ka auranta_ A lokacin dambe ne ka ai ne ba su yi da Nasir ba sai da su Makama suka shiga tsakanin su, Shi a lokacin yana ganin ga Hajiya ta ba shi dama har cikin falon gidan yana shiga su yi hiran su da Mimi, ya manta ita kakarta ce sannan ya manta sanadin ha uwarsa da Mimi sanadin aikatau in da Inna Meri ke yi a gidan Hajiya ne. "Ni? Kamar ni major Kabir My daughter ta auri yalaka agolan da ubansu har ya mutu a can wani auyen kurmus, uban rikonsa wanzami uwarsa yar aiki? Over my dead body Mimi za ta yi wannan auran asakancin ba ta isa ba, ko za ta Mutu bazan aura mata wannan talakan ba, jinin takalawa wanda bashi da wata kyakyawam makoma ko anan gaba_ Sai da ya saka hannunsa guda aya ya daki bangon falon, yana ji kamar a lokacin ake gaya masa kalaman ta ya ya ake so ya manta da wannan cin mutumcin? a kira sunan mahaifin shi a kabari aci zarafinsa sannan aka kira mahaifiyarsa da yar aiki aka zage ta sannan shima a ka kirasa da mara kyakyawan makoma shi ko zuciyarsa ba ta yi masa adalci ba da har take tunawa da wannan yarinyar da aka gama kare ma zuru'ar sa tanadi a kanta. Shi ba dukan da aka yi masa ke damunsa ba, ya fi jin zafin irin kalaman da Mahaifin Mimi ya jefe shi da shi.wai shi ne mara kyakyawan makoma? Shi ne saboda shi Inna Meri ta duka ita da Baba anjuma suna kuka suna ro on a yi masa afuwa a sake shi. _Ku ja ma an ku kunne, naga alaman Tsageranci na damunsa sannan ku yi masa iyaka da ata domin ruwa ba sa'an kwando ba ne, zan sake shi na yanzu amman ko kallon Mimi ya sake yi sai na aure shi da kakin jikina.._ _Abi ka yi hakuri. Abi ina son shi don Allah kada ka rabamu da juna.._ _Sai dai ki mutu, amman ba za ki aure wannan talakan yaron ba, ba shi da makoma mai kyau, na tambayi Hajiya kwalin karatun shi tana gayamin iyakarsa Secondary school. Kuma shima soja yake son zama ire iren su ma ba su da wani rabo a duniya._ _Abi ina son shi._ _Ke yarinya ce Mimi, karatu nake so ki yi ba yanzu zan yi miki aure ba_ _Abi Ina son shiiiii...!_ _Murja ki auke min Mimi kar raina ya aci na fasa kanta da bindigata._ Ba zai manta da wannan kukan da ta ri a yi lokacin da mahaifiyarta ke riketa ba, har gobe yana jin sautin wannan kukan acikin irjinsa. Ya tuna ta na miko hannunta mahaifiyarta da yayarta suka rike ta suka tafi da ita zuwa cikin wani Kafafunsa sun kasa aukansa dole ya koma ya zauna Jagab a tssakiyar Falon yana sauke numfashi sama sama. Hawaye ya cika kwarmin Idanuwansa, Dakyar kuma siririn hawayen ya gangaro ta wajen idanuwansa hawayen so ne, Hawayen son abin da ka haramta ma kanka har Abada. Zafi ya ji jikinsa duka ya auka kuma yana zufa har ta saman goshinsa. Shi ya sa ya mi e yana jan kafa ya koma cikin akin cikin Tiolet ya ara komawa ya kara yin wanka. Yana fitowa nepa suka kawo wuta sai ya kure fanka sannan ya kara kunna ta kasa dai dai saitin Mu'azzam ganin kamar yana jin zafi. Gyara masa kwanciya ya yi yana tuna baya yadda ya ke kula da rayuwar aninsa kafa kafa kamar ba shi da wani kani a duniya sai shi. A fili ya furta" Bani da kamar Mu'azzam bani ni kuma da wami ani kamar sa." Shima gefensa ya koma ya kwanta bayan ya kashe hasken akin Ya kuma auki wayar Mu'azzam ya saka masa chaji da chager insa. Shi kuma wayarsa sai ya sauketa a kasan cafet din da ke cikin akin. Ya da e bai yi barci har biyu na dare barci ma barawo ne ya sace shi. Da asuba da suka dawo daga masallaci Mansoor ya shirya ya tafi camp yace
Chapter 21 · 0% Book details