← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 208

Sashe 80

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafin ya ce"Ni da anina na ke mgana" Nasir ya ce"To ma su kani, ai mu da ba mu da anne da mun shiga uku da gori wajen Aji." Bai fahimci ga abunda ke faruwa ba sai da ya ga bangaren Inna Meri cike da mutane su na yin sallama kowa ya juyo ya na kallonsu shi kuma ya na ganin haka ya yi sauri zai juya Nasir ya cakumo sa daga cikin aki Yalwa ta ce a bu a ma Ango ya shigo, kamar yan Nepa sun sani ya na shigowa falon na Inna su ka kawo wuta tuni hasken fararan wayayan da ke falon Inna Meri suka haske akin da fuskarsa gaba aya. Shaddar Jikinsa ce ta Angon ci sai dai ya cire babban rigan kansa ma ba hula duk suna can camp ya bar su. Gaba aya annensa da yayyensa suka saka masa ihun nepa sannan sai suka Ha a da kiran Ango. Mansoor ya ji kamar ya juya sai dai ba zai iya haka ba tunda Yalwa da kanta take kiran shi sai ya isa wajenta yana shirin zama Halima ta ba shi waje ta ce ya zauna kusa da Mimi abu kamar wasa sai ga shi an Ha a su waje aya da farko bai ma san ita ba ce a gefensa sai daga baya da kanta ya daki gefen kafa an sa. Khadi ta fi kowa ciwon baki itama ta ri a rattaba bayanin duk bayaninta dai Mimi ar gata ce saboda haka cikin gata ya aureta, su Mama dai suna ta dariya domin Yaya Amina itama ta yi zaraf ta ce suma aninsu an gata ne, Halima ta karisa mata da cewa" Kuma shi na dabam ne acikin maza dubu sai ta wahala kafin ta samu kamarsa" Khadi ta harare ta kamar da wasa kafin ta ce"Ita ma Mimin fa? sai ya wahala kafin ya samu kamarta domin duk in da ake neman mace ta cika kuma ta kai." Take fa a har ta na murgu a baki, su Nasir na tsaye suna dariya saboda lamarin ya yi da in kallo ainun. Sai shewa ake yi ana dariya su Amina na yabon anin su Khadi na kare anwarta ita da Rukky. Bintu na gefe ta karkata kanta kan Mimi tana na fa in"To Amarya kin iya gaisuwan Yayan na mu? Barka da safiya kada ki je ki na ina yini ki sa a lamba saboda haka ki kiyaye." Gaba ayan sai da suka ara saka dariya shi dai kansa na kasa fuskarsa ba ingon ma mirmishi ballantana a fahimci halin da yake ciki a wannan zaman da yake yi kusa da Mimi da ga shi sai ubangijinsa suka ka san halin da zuciyarsa take ciki ita kuma Mimi gani take yi kamar ba a wai ita ce kusa da Aji a matsayin miji da mata ba ta ta a tunanin fatan ta zai kasance gaskiya ba. Yalwa ce ta ce kowa ya yi hakuri sannan ta kalli Mansoor ta ce"Yarinyar nan amana ce a gare ka ku ri e maraicin ku duka ku yi ma juna uzuri sai ku zauna lafiya Allah ya yi muku albarka ya ba ku zaman lafiya." Aka amsa da amin masu hotuna a wayoyi suna ta auka wasu ma suna ta jera Video ko tarin Aji ba wanda ya ji acikin falon nan itama Inna Meri ta kara Ha a su ta saka albarka sannan akace a yi addu'a gaba aya Ko gama shafa addu'ar ba'ayi ba nepa suka auke wuta ko kafin a yi kaya kaya a kunna fitilan wayoyi Aji ya sulale ya Gudu sai dai nemansa a ka yi aka rasa. Inna Meri na yar dariya ta ce"Baban Inna ne fa, daman ina kallonsa ya kagara ya tashi.". Sukan su Nasir ba su gan shi ba, tuni ya sulale ya koma gida ya je ya yi wanka ya gaji kansa har sara masa yake yi su kuma sai da su ka jira aka shigar da Mimi akinta sannan suka maida wan anda suka auko can gidan su Mimi. Makama ya auki matarsa suka tafi gida tunda sauran da motocin su suka zo, Nasir ma gida ya tafi Mu'azzan kuma sai ya bi Ahmad zuwa gidan su a tunanin sa Mansoor wajen Mimi zai kwana shi kuma yace can ya yi masa nisa ya je ya kwana shi ka Gidan nan bai auke kafa ba har wajen sha biyun dare sannan an uwan Mimi suk tattafi a ka bar amarya daga ita sai halinta Rukky ma ta an tsaya daga baya kuma ta tafi domin ta ce tasan halin wanda Mimi ta aura sai ya zo ya yi mata rashin mutumci. Mimi ita Ka ai ne a akinta daga ita sai halinta har misalin aya na dare tana jin hayaniyar su Bintu daga akin Inna Meri, daman bayan Rukky ta tafi Bintu da Hibba sun shigo akin suna tambayanta ko tana bukatar cin wani abu? Ta ce ita ba ta bukatar komai duk da rabon ta da abincin tun da rana da sha wata Fura, sun an zauna ka an suna hiran su ba ta dai saka musu baki daga baya suka mata sallama suka fice bayan sun rufo mata kofa tana zaune a falo ne daga baya ta mi e tana zagaya falon nata tana gani ita sai taga wajen ya yi mata kyau fiye da Surutun su khadi akan akin nata, daman ita tafi san komai arami ba ta cika son ta ga katon gida ba to ita ina ruwanta tunda dai ta samu cikar burinta. Har bedroom in ta shiga gadon ya burgeta yadda yake arami gwanin ban sha'awa sai dai kowa yasan kayan da ke cikin akin nan yan waje ne masu kyau da tsada da yake tana fashin salla sai ta so ta yi wanka amman sai ta duba tiolet in ruwan ba shi da yawa sai kawai ta yi tsarki ta fito ta kara gyara jikinta, aramin akwatin ta jawo da Rukky ta sanya mata kayan da za ta bukata sauran kuma suna gida sai daga baya za'a kawo mata. Ita a ranta ta ji cewa Aji ba zai zo ya kwana a wajenta ba shiyasa ta yi shirin barcinta ta saka wata rigar barcinta doguwa kalan sararin samaniya, ta yi ai bisa gado gajiya na saukar mata ta fara jin zafi Allah ya cece ta suka dawo da nepa ai sai ta ara bajewa sai barci cikin salama da wani farinciki na ganinta yau kwance a kan gadon auranta auran ma ita da abun sonta Aji. Ta yi barci barcin da ta da e ba ta yi kamar sa ba, sai wajen arfe takwas na dare ta farka shima ofar akin ta ji ana ta bugawa sannan sai da ta tashi sannan ta ji hayaniyar yan gidan kamar acikin akinta a ke yi. Ta rasa ma mafita ga shi ba ta san ina aka ijiye mata Hijabi ba, sai layafan jiya ta na a sannan ta sako takalminta ta fito zuwa falo ta bu ofar sai ta ci karo da Bintu da Hibba karo na biyu auke da kwandon abinci ita kuma Hibba ta ri o fulas in ruwan zafi mirmishi suka yi mata, itama da yanayin barci a idanuwanta ta maida musu martanin mirmishin. Sannan ta bu e musu kofa su ka shigo sai da su ka shigo sannan ta maida ofar ta rufe ta bi bayan su anan saman centar table in da ke tsakiyar falon suka sauke komai ita kuma sai ta samu kujera mai zaman mutum aya ta zauna suna fuskantar juna. Bintu ta fara gaisheta ta amsa cikin fara'a sannan Hibba ta gaisheta ta amasa tana kallonta domin ba ta santa ba. Bintu ta ce"Ba ki santa ba ko? Matar Yaya Mu'azzam ce Hibba." Sai Mimi ta washe baki tana fa inn" Ayya sannun ku da okari" Suka amsa mata da yauwa kafin Mimi ta ce"Ya kwanan su Inna? Ina fatan sun kwana lafiya? Bintu ta amsa da kowa lafiya suna gaisheta Mimi ta lumshe ido domin har ga Allah barcin ne bai isheta ba. Hibba ta kalleta lokaci aya tana fa in"Bari mu tafi naga kamar mun tashe ki daga barcin gajiya." Ta na gama fa in haka sai Mimi ta fara Hamma Bintu ta yi dariya kafin ta ce" Ga shi nan ai gajiya ta fara nuna kanta." Mimi na yar dariya ta ce"Wlh jikina kamar an yi min dukan tsiya." Hibba ta amsa mata da cewa" ki yi wanka ki ci abinci sai ki koma ki huta ba wanda zai dame ki." Mirmishi kawai ta yi kafin Mimi ta Tambayi yan biyu Bintu ta ta e baki ta ce suna gida jiya da daddare babansu ya zo ya tafi da su, Hibba na gefe ta ce itama ta samu sauki annen saa da su ka zo jiya su ka tafi da su. Mimi na zaune ta na jinsu ba ta dai saka mu su baki, sun an jima sannan suka yi mata sallama sai bayan fitan su ne ta koma ta ciki ta kwanta domin barcin bai isheta ba, ba ita ta tashi ba sai ba wajen sha aya shima kiran waya ne ya ta she ta. Khadi ne ke damunta da kira tana auka ta ce"Mimi Allah ya sa an maido dai Nepa jiya? Cikin Mamaki Mimi ta ce" Eh an maido me ya faru ne? Khadi tace" Muna nan muna tunaninki zafin gidan nan ai na dabam ne jiya ai da zafi ya kashe ki naga arya so." Mimi sai da ta yi dariya kafin t ace" Ni barci ma nake yi ke kika tashe ni, bari na yi wanka na karya sai mu yi mgana.". Da sauri Khadi ta ce"To ya? ba in Angon naki ya angwance ne da sai yanzu kuka tashi? Mimi ta saka dariyanta mai kayatarwa kafin ta ce" Bai kwana ma a gidan ba, ai kinsan an uwan su duk ba su tafi ba." Khadi tace"Uhm! to sun kawo miki Breakfast ko mu aiko miki da shi? Da sauri ta ce"Laa wallahi tun safe ma suka kawo min yanzu dai in na yi wanka zan karya yaushe za ku zo? Khadi ta e sai zuwa anjuma dag anan ta ba ma Mommy wayar ashe
Chapter 80 · 0% Book details