← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 208

Sashe 152

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

duka tana lallashinta Harira kuma ta arisa kusa da Inma ta ri o ta tana fa in" Ki tashi daga kasan nan Innar Mu'azzam, ki koma cikin aki." Amman Inna ta kasa tashi. Hawaye take yi amman tana saka hannunta guda aya ta na gogewa, Mansoor ji ya yi kamar ya mutu saboda Ba in cikin dake cin ransa Inna suka saka kuka lalle nema. Shi fa kafin ya fara aiwatar da komai sai ya fara cin uban Saddiqu wlh, Auwalu ma lamarin bai yi mishi da i ba haka ya duka yana ba ma Inna da Walida ha uri, Baba Sani ya juya ya na kallon Mansoor dake tsaye har lokacin hannunsa goye a bayansa yana cije le ensa na asa Ya ce"Kai kuma tsayuwar me kake yi, ka zo ka lallashi ita Merin ta koma aki lamarin bai yi da i ba sai hakuri." "Akwai wanda na ke jira ne." Amsar da Mansor ya bashi kenan a kausashe kafin kuma ya kalli Walida kukan ta ma ata masa rai ya ke tsawa ya daka mata kafin ya ce"Ki yi min shuru anan wajen," haka ya fa a yana kokarin saisaita fushinsa a lokacin ji yake yi kamar ya mutu sai wajen ya yi shuru har mai kukan aryan ta natsu Bintu ya kallah daga baya yana fa in"Bintu kama Inna ku koma aki." Yana gama fa in haka dai dai da shigowar Saddiqu da sauri yana fa in" Magajiya ki kamota ga mai adaidaitan na samo." Gadan gadan kawai ya nufo bangaren shi kuma Mansoor daman shi yake jira Kawai sai suka ha e. Ya saka hannu ya ture Saddiqu sai da ya kusa fa uwa kasa ya dago cikin mamaki domin ya ga waye ya yi masa haka kawai Mansoor ya daddage iya karfinsa ya tsinke Saddiqu da lafiyayyan marin da sai da ya ga hasken taurari, bai gama dawowa hayyacinsa ba ya ara masa wani, da sai da ya fa i kasa ya bi shi ya saka hannu ya dam walan rigan shi ya ago shi sannan ya ara masa wani marin mai shiga jiki sannan lokaci aya ya ture shi da arfin da sai da ya fa i kasa. Kowa sai ya bu e baki yana kallon ikon Allah Baba anjuma kuwa saboda jin da i da karfi ya ce"Na gode maka mansoor, kayi masa dukan tsiya." Harira ma ta ji da in hukuncin Gaje dai ba wanda ya gane yanayin ta, Baba Sani da Baba Danlami sai faman subhanallahi suke fa i kawai domin Saddiqu ya maru lokaci aya har shacin hannu ya bayyana a dama da haunin fuskarsa sannan jini na bin hancinsa kenan ha o ya yi. Zuwaira ta kira sunan Mansoor cikin tsawa tana fa in kada ya kara ta a mata kaninta Auwalu na gefe ya ce"Wlh ya yi min dai dai gwara ya kara masa tunda ba shi da mutumci." Bintu ko kamar an sakata a Ajannah har Walida mai kuka ta ji da i, yau kam Inna na zaune amman ba ta hana ba. Lalle tura ta kai vango magajiya kuma tsaabar ru ewa ba ta san ma ta saki mai ciki ba tana mamakin wai Agola ne ya kama anta da duka ita kuma Maeesha ba ta san ma ta tsaya da kafafunta ba jikinta ba inda bai rawa ganin Mijin nata da take ta ama da shi a gabanta ya maru, to ita fa? Tuni ta manta da an dake ta a ciki ta mike ga jikinta tana wani fi i fi i da idanuwa. Saddiqu kuma cikin orin kunya ya lakato jinin dake saman hancinsa ya gani. Sai kawai ya taso yana fa un" Ni ka mara. Wallahi sai na rama." Ya nufi Mansoor gadan gadan sai Auwalu ya ri e shi amman yana fizge fizge kamar zai iya wani abun, Mansoor ya kalle shi cikin fushi kafin ya nuna shi da yatsa lokaci aya yana fa in" Mari na farko na Junior ne, mari na biyu na Walida ne mari na uku saboda Inna ne. Kai har ka isa uwar tamu kake son ka kashe mana?. Wallahi ka ci darajan Baba da yau sai ka raina kanka banza kawai sakarai wanda ba namiji ba." Ya gama fa a lokaci aya har yana hambari sa shi da kafafunsa shi kuma Saddiqu tana hakilon nanza. Juyawa mansoor ya yi ya isa ga Inna ya saka hannu ya ta da ta tsaye lokaci aya yana fa in" Ki yi hakuri Inna komai yau ya zo karshe." Bintu ya kallah kafin ya ce" auko ma Inna hijabi ta saka, ke ma ki shirya Walida ta auko mayafinta mu je mota ki riko hannun Junior." Ya fa a Lokaci aya yana rumgume Inna ta gefren kafa anshi da sauri ko Bintu ta shiga aki ta auko masa hijabin Inna ya taimaka ya saka mata, Inna hawayenta sun i tsayawa abin da ya faru yau ya ba ta tsoro matuka da mamaki. Walida ma ta sako hijabinta ita da Bintu, Inna Mero kuma Mansoor ya saka mata takalmi da kansa sannan ya Juya yana kallon Baba lokaci aya yana fa in" Baba ka yi hakuri amman Inna ba za ta cigaba da zama a gidan nan ba tunda har oamarin ya kai ga duka bamu san abib da zai faru a gaba ba kuma, kada ka ji a ranka kamar ka gaza kawai dai ba zan iya hakurin na barta ba ne gwara ta bar gidan sai wa anda basu san zamanta a gidan su ha a da akinta suyi ta zama zauna." Baba anjuma ya jinjina kai kafin ya ce"Bakomai Mansoor, nima a yau ina goyan bayan ka, Mahaifiyarka ce kana da Ikon kare martabanta tunda ni na kasa, ku je duk inda ta koma ni a matsayina na mijinta zan bita ko'ina ne." Sai a lokacin Magajiya ta samu bakin mgana sai ga ta, ta yi wani tsalle ta sha gaban Mansoor da Inna Meri lokaci aya tana fa in"Ina za ka?. Wallahi baka isa ka dokar min a kuma ka juya ka yi tafiyarka kamar ba abin da ya faru ba. Ba ka isa ba domin ban ta a ganin inda Agola ya daki an ma su gida ba, Ko ka auke ta daga baya kenan bayan kun gama zama kun gama more komai, nan gidan dai shi ya yi muku komai dangin uban naka me suka tsinana maka? tunda ka shigo rayuwarmu kai da mahaifiyarka kuka rugumin gidana a da ina zaune da gani sai a'yana da mijina amman zuwan wannan matan da zuwan wannan Agolan gidan nan komai ya sauya. Yanzu Danjuma ya fi fifita Agola sama da ayansa, in ba lalacewa ba a gaban idon ka a aki anka amman ka kasa mgana sai ma munawa da ka yi abin da aka yi dai dai ne to ni wallahi ban yarda ba sai an bi ma ana ha insa" Take fa a tana wani hura hanci, Mansoor ya yi niyar zagayeta su wuce ne amman Inna ta hana ta kalli Magajiya na wani lokaci kafin ta yi mirmishi ta ce" Kin ce wai dangin ubansa me suka yi masa ko? Ai ko sun yi masa komai tunda dai tun zuwan Baban Inna gidan nan abin naira biyar baki ta a taimakon shi da shi ba kin ga baki da ikon fa i wata mgana ba. Sannan na da e ina hakurin duk irin cin kashin da kike yi min a cikin gidan ki yi ta aibatana ana kina kiran shi da Agola Allah Sarki da ace Ibrahim ya yi tswon rai Magajiya na rantse ga Allah kila har ki koma ga Ubangiji ba za ki u da ni ba. Ba zan zo aure a wannan gidan har na zo da Baban Inna ba mutuwa ce ta yi ma shigar sauri ita ce ta maida shi mara uba amman ba Agolan da kake tunani ba, ni ce nan na matsa sai na taho da shi saboda ba na son ya yi nesa dani amman ke kam shaida ce ba domin dangin Babansa sun gaza da ga ri on sa ba. Na zauna da kowa bisa amana a wannan gidan ban ta a tunanin cutar da kowa ba, ban sani ba ko tun zamana na ta a yi miki wani abu na acin rai da ya sa kika tsane ni. To yau ta kare ki yi hakuri ki yafe min Magajiya, Allah ya baki hakuri in dai laifina auran Mallam da kuma ri on Yayan da ya bani to duk kiyi hakuri rayuwar nan duka duka nawa take? Wata rana ba ni ko ba ki a duniya nan? Ko kuma ba Mallam ko mu rasa wasu daga cikin yaran mu duka sanin gaibu sai Allah ki yafe min Allah ya kaddara saduwa." Inna Meri ta gama fa a tana mai fashewa da kuka sai jikin Magajiya ya yi sanyi duka masifanta ta kasa magana, Inna Meri na kuka ta kalli su Gaje tana fa in" Saboda zama da rayuwa in na ta a sa a muku ku yafe min, ni dai wlh ban ta a rike kowa a cikin ku ba na yafe muku duniya da lahira, Sani da anlami ku ma ku yafe min ila zama na tare da ku na yi muku wani abu ni dai ba ku min komai ba wlh, ina rokon ku da yafe min saboda rayuwa." Tana magana tana kuka Gaje da Harira jikinsu duk a sanyaye su ka ce wlh ba ta yi musu komai ba ita ce ma suka yi ma laifi ta yafe musu ta ce bakomai su baba Sani sun kasa mgana anlami ne ya ce su kam ba ta yi musu komai ba. Magajiya na ji da gani Mansoor na rike da inna Meri su k fice daga gidan su Gaje suka raka su har da Baba Danjuma aka bar mata gidan gaba aya amman kuma ta kasa farinciki Har Auwalu da shi a masu rakiya, tuni makota sun fara taruwa, su Gaje ke fa in Inna Meri ne za ta bar gidan sai ga shi an fara cika wajen tuni Dije matan Mallam Hashimu ta garzayo, ta lna kuka tana fa in Ina Inna za ta tafi ta barta Inna ta ce ba inda
Chapter 152 · 0% Book details