Sashe 52
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shake suna yi ma juna gaisuwan rashin da suka yi madiha ta ce yanzu za su taso ita kuma Khadija ta ce suma ga su nan a hanya. Khadi ce ta kira wayar Mimi sai dai tana ta ringing ba'a auka ba wayar Hajiya ma haka , sai ta kira wayar Mommy sara ta auka ta ce Mommy na cikin akin da Abi yake, Sai khadija ta kara rushewa da kuka ta kosa su isa Mommy ba za ta iya aukan wannan rashin ba ita ka ai ba. Ko kafin takwas na safe a kafafan Sada zumuta duk an saka rasuwar da sauran duk wanda ya kamata yaji rasuwar Major Kabir ya ji, musamman gidan Talabijin na Karamchi a Safiyar ranar suka tashi da wannan alhinin domin ko da Alhaji Hamza ya isa gidan Hajiya Mimi ta bar gida zuwa wajen aiki tunda labaran Safe gareta. Tana akin Labarai ana gyara mata fuskarta Wayar Daddy ta shigo mata sai da gabanta ya fa i a lokacin ba ta ji kamar za ta fa i ba sai da ya ce ta bar komai ta taho gida ita ta sadakar Hajiya ce ta rasu daman ta barta kwance ta na gayamata ba ta jin adin jikinta. Haka ta bar wajen aiki a afujajan sai dai abin da ta je ta ji ne yasa ta ru e ta kasa mallakan kanta Hajiya kuma sai ta yi dauriya ita ke lallashin Mimi Alhaji Hamza kuma ya na amsa wayoyin mutanen domin in za'a saka rasuwar Major Kabir sai an ce Yayan Alhaji Hamza tsohon Sanatan jihar Gombe. Rukky ne ta yi ta kiran wayar Mimi ba ta auka ba, saboda su san abin da ke faruwa sai Mimin ta rubuta sako ta tura mata. "Rukayya ki sanar da Manaja Abuja za mu wuce yanzu Allah ya yi ma Abi rasuwa." Allahu Akbar zukata sun raunana yawancin mutane ma sanarwa da gidan talabijin na karamci ta yi ne su kasan abunda ya faru ciki har da Inna Meri da ta na ma cikin aki lokacin suna cikin karanta labaran duniya na Safe bayan sun gama suka sanar Walida ce ta rugo aki da guda tana haki ta ce"Inna yanzu nagani a Tibi ana fa in Allah ya yi ma mahaifin mai karanta labaran na rasuwa Mimi." Da Sauri inna Meri ta mike ta fita falo Sai ta ci karo da hoton Major kabir cikin kakinsa Soja ana sanar da rasuwarsa jiya da Daddare za'ayi jana'izarsa yau Jumma'a bayan an sauko daga sallar Jumma'a a gidansa dake Gwarimpa a Abuja. Ba za ta manta da fuskarsa ba ta gane shi Allah Sarki rai bakon duniya daman ai arsa ta ce ba shi da lafiya duk sai jikin Inna Meri ya yi sanyi a fili ta ka a kai kafin ta ce"Allah ya ji an sa da Rahama mu kuma Allah ya kyautata ta mu bayan tasu." Walida ta amsa da Amin ita ba ta san shi ba amman ai ta san Mimi budurwan yayansu ne a baya kuma Inna Meri ta san su shiyasa ba ta yi mamakin ganin yadda jikin Inna Meri ya yi sanyi ba. Suna zaunen Baba anjuma ya shigo cikin shirin fita yana ga ya mata shima Jana'iza zai je anin Mallam Hashimu ne ya rasu. Ta yi salati kafin itama dire da fa in "Kai Jama'a ana ta tafiya nima yanzu nake ganin sanarwan rasuwan mahaifin yarinyar nan da Baban Inna ya so mai karanta labarai anan yanzu suke fa i jiya da dddare ya rasu." Baba anjuma ya ce"Innalillahi wannan Sojan? Inna Meri ta gya masa kai sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Allah ya ji an su da rahma Allah yasa Aljanna makoma" Shima yana tunawa da shekarun baya ne har an zo an gama jin adin duniya kuma an koma. Kai Allah yasa mu dace, Allah ya sa mu mutu muna masu Imani Amin. ****** Kamar yadda aka sanar an yi Jana'izar Marigayi Major Kabir Sulaiman Dabo a gidansa bayan sallar Jumma'a Alhamdulillah ya samu jama'a kama daga yan siyasa abokan hul ar Daddy tare da Abokan aikin Abi sojoji ritayas kamarsa har da masu kakin a lokacin sannan tare da mazajen yayan shi da kuma sai yan'uwa da abokan arzuka tare da dangin Mommy daga kano aka sallace shi zuwa gidansa na gaskiya. A ka bar mata acikin gida suna kuka sak abin da Mommy ta gani a mafarki shi ya faru ta ri e gawan mijinta tana wani irin kuka sai da anwarta Zainabu ta zo ta ri e tare da sauran yan'uwanta da su Mama ko da aka fita da shi sai ta fa i a sume ita da Mimi. Madiha da Khadi kuma sun kasa mallakan kansu ma. Alhaji Hamza da Sulaimam suka yi ma Major wanka suka ha ashi saboda nisan makabartan sai bayan la'asar suka dawo daga kaishi. A makabarta Sulaiman ya sha kuka shi da Alhaji Hamza Jaheed ma ya iso da shi akayi jana'iza. Shi ne ya rike sulaiman in ya tada shi daga gaban kabarin Abi likita ne mai dakiya amman ya yi rashin bangon da har abada ba zai iya maida kamarsa ba. Suna dawowa aka kafa tantuna a haraban gida domin zaman makoki. Hajiya kuma ta yi tawakkali tana zaune da hijabi da carbi ko hawayenta ba wanda ya gani Lokacin da aka tafi kai shi bayan Mommy ta farfa o ta fara surutai tana fa "Habibi yace na nema masa gafara wajen Hajiya, Hajiya ki yafe masa ya rasu da niyar a yau mu je Gombe ya durkusa ya nemi gafaran ki, ke ma Mimi da ke ya rasu kina bakin shi fa i yake yi Murjanatu ki yi min alkwarin yi ma Mimi duk abin da zai saka ta farinciki ciki har da neman yaron nan ku rokesa gafaran ya yafe min." Sai da Mama ta rufe mata baki sai sakin maganganu take yi kamar ba ta cikin hayyacinta. Sai a lokacin Hajiya ta yi hawaye cikin kuka ta ce"Na yafe masa duk laifin da ya ta amin da wanda ya sani da wanda bai sani ba, ina masa fatan salama da aminci da kuma dacewar wannan rana ta Jumma'a mai daraja Allah ya ji an ka Kabiru". Sai Hajiya ta fashe da kukan da take ta rikewa Mimi ta koma jikinta ta kwanta suka ha e suna ta gunjin kuka. Mommy fa i kawai take yi" Habibi ya rasu? Ni murja ina zan sa ka kaina a gabana fa ya rasu Allah ya ji an ka Habibi." anwarta Zainabu ta ce"Ki daina kiransa da wani suna in ba sunan shi ba mala'iku da sunan shi suka san shi ba Habibi ba, ai yanzu wani Habibi ya kare Murja gafaran Ubangiji zaki yi ta neman masa shi ne kawai gata da Soyayyar da za ki nuna masa" In ka kalli Ahalin nan sai ka tausaya musu, duk da yanayin Abi amman fa tsayayyen Uba ne mai yin komai saboda ayan shi, shi ya gina su har su ka kawo matsayin da suke a lokacin kowacce ka gani ido ya Kumbura murya ta dishe saboda kuka, Mutanen arziki daga ko'ina sun zo musu gaisuwa daga Gombe Rukky tare da Salim Bunza da Na Misau da wasu daga cikin ma'aikatansu da aka wakilta ranar biyu sun zo musu gaisuwa, Rukky ma nan ta kwana sai ranar uku ta koma Gombe ita ma Khadi abokan aikinta da na mijinta duk sun zo musu gaisuwa haka Dr. Sulaiman sannan Jawahir ma yan'uwanta suna ta zuwa.Haka dangin Mommy su ma sun yi mata kara kwarai da gaake. Ana ta zaman gaisuwa manyan manyan mutane nata zuwa gaisuwa su kuma shiga har cikin gida su yi ma Mommy gaisuwa wacce ta za ma abun tausayi. Mimi ta samu wayoyin mutanen da ba ta san wasu ba ma, a rana ba ta san adadin masu kira su yi mata gaisuwa ba, kaf ma'aikantan su har da masu Inten ba'a bar su a baya ba. Sannan ba ta yi tunanin za ta samu kiran wayar su Nasir ba. Sai ga shi Mu'azzam ne ya fara kiranta ya yi mata gaisuwa ya ce a kafafen sada zumunta ya gani sai kuma da ga baya Usman ke fa a masa, sannan Usman ya kirata Ahmad ma tare da Nasir sun yi mata gaisuwa kuma ta ji da ii kwarai. Sai dai Aji bai kirata ba kuma tana da tabbacin ya sani rashi fa ta yi rashin kuma na Mahaifi, tunda ta kar i lambarsa ba ta samun kwarin gwiwan kiransa ba. Sai ta ce bari ta gani zai iya yi mata gaisuwa?. Sai ta auki wayarta ta tura masa sako. "Aji Nah Abi ne ya rasu yau kwana biyar." Mimi ce Fatima" Ita kanta ta san bazai ta a mata gaisuwa ba, tunda ya kasa mantawa da abin da ya faru a baya, abunda ba ta sani ba tun a ranar yaji rasuwar domin a daren ya je gaida Inna take gaya masa a cikin ransa ko a fili bai ce Allah ya ji ansa ba. Sai da Inna ta ce"Kanin ma mallam Hashimu shima ya rasu yau. Allah ya ji an su da Rahma." Ba saboda shi ya amsa ba sai Saboda anin Mallam Hashimu amman yadda yake jin tsanar wannan mutumin ba zai iya nema masa jin ai wajen ubangiji ba, ba domin ya na musulmi ba da sai yace Allah ya kara nauyin kasa. Kuma Mu'azzam ya kira sa ya gaya masa ya ce to ina ruwan sa? Bayan nan har Makama sai da ya kirasa yana gaya masa ya yi tsaki ya kashe wayarsa ya rasa waye ne baban Mimi a wajensu da suka damu da Mutuwarsa. Nasir ne da ya kirasa sai da suka yi fa a kamar abun arziki Nasir ya ce"Ya arin ha urin mu kuma Aji? Aji ya ce"Ni babana ya ji ma da rasuwa, Innata kuma da ranta sannan Babana uban ri o na yana cikin koshin lafiya." Nasir ya yi dariya kafin ya ce" Gaisuwan Major mana baban Mimi, ya kamata ka kirata ka yi mata gaisuwa sanda na kirata sai da ta tambaye ni ka sani kuwa? A fusace Aji ya ce"Nasir ba domin kai ba ne wallahi da sai na zage ka,