← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 208

Sashe 108

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sauke su a kayattacen hotel. shima sakon ya tura mata kamar yadda ta tura masa. "Mun sauka lafiya yanzu." Misalin uku na dare, sai kuma da asuba ta ga sakon a ranar Alhamis kenan, gidan daman tun a jiya ya fara samun ba i yan biki. Da Safen Mimin ke sanar da Inna cewa sun sauka lafiya sai Inna Meri ta ce da safe ya kira ta sun yi mgana. Jiya ma daman Mimi ba ta yini gidan ba tana wajen Hajiya yau kuma sai da ta je wajen aiki daga can ta sauka Hajiya ta ji sau i, Mommy ta zo jiya ta duba Hajiya ba ta kwana ba ta koma a ranar. Inna Meri da su Bintu har da su Yaya Halima sun je har gidan Daddy sun duba Hajiya kuma taji da i kwarai.. To a ranar Jumma'a da safe ma Hajiya ta koma gidan ta, tunda ta ji sauki sosai a ranar ma Mimi bayan ta dawo wajen aiki ta fara sauka nan ta duba Hajiya anan ta iske Jaheed ya zo garin da safe nan shi ne ya zo duba Hajiya. Sai ranar suka ta a ha uwa tun bayan auran ta, su ka gaisa kamar ba in juna a gaban shi Hajiya ta ce"Ina megidan naki? Ko bai dawo daga tafiyar da ya yi ba ne? Mimi tace" Bai dawo ba Hajiya, ya ce kila su yi sati a can" Hajiya ta ce" Allah ya sa a dawo lafiya" Ta amsa da Amin ganin Jaheed ya sa ba ta wani sake ba, ta na yin sallar laa'asar ta ce ma Hajiya za ta tafi. Hajiya tace gwara ta tafin tun da suna da sha'ani a gidan na su. Ta yi musu sallama Jaheed na gefe ya na ga danna wayarsa amman kuma rabin hankalinsa na kan Mimi daurewa kawai yake yi sai bayan fitan ta ne ya tambayi Hajiya Mijin Mimi ya yi tafiya ne? Hajiya ta ce" Eh tace min wai ko ya tafi ina ne, can ne sana'arsa ta kwallo ne." Sai kawai ya ra usayar da kai bai kara mgana ba ita kuma Hajiya sai ta ce" Wai ni yaushe za'a ka kawo min kishiyar tawa ne? Kai tsaye ya ce" Ba yanzu ba, tunda kika hana ni Mimi kin yi ma kanki kuma." Hajiya ba ta samu damar mgana ba Sai ga Yaddiko da zuwan ga anta har da Megidan ta, Shi ya sa mganar da Jaheed in ya yi ta tsaya anan shima dai ganin su Yaddikon bai da e ba ya yi ma Hajiya sallama ya ce zai dawo da daddare. Lokacin da Mimi ta koma gidan nan ya cika da mutane, haka ta tsallake mutane a bangaren Magajiya ta wuce zuwa bangaren Inna amman ta yi musu sannu da aiki..sai nuna ta ake yi ana cewa Matar mansoor ne wannan yar gayun da ake gani a Talabijin, Itama Inna shashenta ya cika da su Yaya Halima sai Mimi ta ji da i, Inna Meri wai suna gidansu Gaje ana gyaran shinkafa su kuna suna aki suna shewa Bintu uwar labarai kenan, da ya ke ba ta da yunwa sai kawai ta sauya kayan jikinta ta shiga cikin su itama. Dawowar Inna ce ta fattake su ta ce su je su kama aiki tunda ana ta gyaran kayan miya da yanke yanke, Mansoor ya turama Auwalu ku i an siya shinkafa da masara da ta tuwo da sauran Cafane, da Bintu ta ce wlh yadda ba su saka su ba, ba za su tusa kansu ba aiko Inna Meri ta ce to sai dai ta zo ta koma gidan ta, jin haka yasa ta fito itama aka zo akama kama aikace aikace ita Jummai ba ruwanta ita yar kowa da kowa ce, amman Zuwaira ce kamar uwar ta yi kaki har mugun halin, tana gidanta tare da su ayan su Gaje suna soyan nama kada azo nan wasu su gani. Walida ma suna gidan matar Auwalu tare da mariya, Magajiya sai shiga ta fita take yi ta na ba da umarni, Inna Meri dai ba ta da wani matsayi makota ma sun fita daraja ita da matar abokin Baba Danjuma Malam hashimu Dije kamar sun irin shigo aiki haka aka ware su. Gabda mangariba yara su ka fara Ihu ga Mu'azzam nan, an shigo da wasu kaya tunda daman akwai kayan Hibba da ya taho mata da shi, ya shigo cikin gida ya gaggaisa da mutane dagan ya fita tare da Junior ba da ewa sai ga Ango shima ya sauka da tawagan abokansa irin sa sai gida ya tu e da gu an ga Ango ga Ango. Daman Mimi ba ta ta a ganinsa ba sai ranar, ta ganshi duk a tsotse sai uban gashin da ya tara a saman kai abokan na shi ma irin shi ne. Har dai sai da ta are ta tambayi Hibba ko shine Angon? Hibba na dariya ta ce" kwarai da gaske." Mimi ta jinjina kai kawai ba ta yi mgana ba, haka yan'uwansa su ka rufe shi suna masa murnan Ango ana sakin gu a amman Bintu ko kusa da wajen ba su je ba suna gefe. Har wajen bayan isha'i sannan a ka gama aikin Bintu daman tun da taje sallar mangariba ba ta dawo ba, wai ta gaji bayanta na ciwo. Mimi da Hibba daman yanka albasa suka yi, gwara Hibba ta yi gyaran tumatur itama Mimi cewa ta yi ta gaji. Daga nan suka koma shashen su, Hibba ta ma mijinta girki har Mimi ta ci ita da Bintu, bayan ta gama yi ma su Yaya Haliman tsiyan su kam tuwon da su Inna ke can gidansu Gaje suna takawa za su ci. Su ka ce sun ji bakomai tunda har da Innar su a masu yin girkin. Mu'azzam bai shigo ba ya aiko aka kar an ma sa abincin sa, a gidan kuma yayansa ya kwana tun da daman yana da key din, sun yi mgana tun safe tunda shima ba zaune su suke ba, sai gobe ne za su buga wasan suma. ****** *Saturdaay, 25, December 2023* A ranar ashirin da biiyar ga watan December aka aura auran Saddiqu da Amaryan sa mai suna Maeesha. An ce Aisha ne sunan ta amman awayenta da iyayenta Maeesha kowa ke kiranta da shi. Sai kuma a safiya ranar aurin aure suka zo su kawo kayan jere , yan'uwan ta sai a hankali suna ta yamutsan fuska tun daga ganin gidan sannan Kujeru suka ki shiga aki sai da aka balla kofa sanna. An yi mata kaya kamar na hauka kila ko bai sanar musu in da zai ijiye ta ba ne, kaya wajen rabi sai dai aka maida su in da suka fito, kuma wai a haka suke alfaharin har sai dai aka maida kaya gida saboda ba waje. Walida da suka kwana gidan Auwalu ita ta zo da labarin da ta dawo gida wanka, ta ce Yaya Auwalu ya zo ya na fa an cewan Saddiqu ya je ya yi aryan bai sanar musu in dai zai ijiye amarya ba, yanzu sun zo sun ga waje sun koma suna ta mganganu Amarya ta kira Saddiqu ta ce ba ta yarda ba, gwara ya sama mata inda duka kayan ta za su shige, Walida ta ce acan dai ana ta rufa rufa da mgana amman kamar su iyayen yarinyar ba su san anan gidan arsu za ta zauna ba. Yaya Halima ta ce" Ikon Allah! To meye na arya? Bintu ta kwashe da dariya kafin ta ce"Ko ke Yaya Halima ai yawa ne ya ce mata a gidan Wanzamai za ta zauna." Yaya Amina ta ce" To yanzu ai gashi karya ta are.," Walida ta ce" Wai Magajiya ita nan dole tunda Yaya Mansoor ya zauna a gidan nan anta ma sai sun zauna." Bintu ta ce" Ai ita a wajen hassada za ta mutu, ita sai ta ha a saddiqu da Baban Inna? Wanda ko yau ya ga dama zai siya gidan da sai an sha kallon shi bayan ma wanda ya gina" Hibba ta ce" To wanda ke da gidan shi, ba domin ea'ayi irin na shi ba, me zai kawo shi zama a gidan nan? Haka suka ri a tattaunawar su Mimi na wajen amnan ba ta yi mgana ba, tunda ba ruwanta a ciki, Inna dai suna can gidan su Gaje suna tuwo da miya nan gidan kuma shinkafa aka dafa. Gwara ma su Yaya Halima da su aka saka shinkafa amman Bintu fita kawai ta yi ta tsaya Mimi da Hibba dai sun taimaka an wanke shinkafa. Bintu har Zuwaira sai da ta yi mata habaici wai su Bintu ci aka iya ba aiki ba. Bintu ta karkace baki Ta ce" To naga duk manyan mu sun famshe mu, mu yan kucakucai ba sai mu koma gefe ku dafa mu ci ba." Wasu daga cikin anuwansu na cikin gari su kace hakane. Ita Bintiu daman yar fitina ce, ba ta i taron bikin ma ya tsarwatse ba. Da wuri aka gama aiki aka yi wanka Bintu tace su bari sai sun su Zuwaira sun gama saka kayansu sannan su za su saka nasu, Mimi tace za ta kira mai makeup ta yi musu kwalliya Bintu tace da ta biya ta. Nan da nan ta aga waya ta kira wata Zubby mai yi mata makeup ta yi mata kwatance ta ce tana wani gidan bikin amman daga nan za ta wuto nan, su Zuwaira an sha Leshi ana ta agawa a tsakar gida itama magajiya an dinka mata leshin, tare da sauran ya'yan su da can gidan su Gaje Inna Kuma Super wax inta ta saka Bintu ta ce ki fita a kalleki a kara uwar Mu'azzamar Inna Mansoor, Maman Halima da Amina, Uwar Bintu da Walida surukar Hibba da Mimi. Sai da ta ba ma Inna dariya ai ko da ta fita an sha kallo domin dai an san Inna ta wuce reni yanzu ta Haifa kuma ko wa anda ba ta haifan ba suna yi mata. Wajen karfe biyu mai kwalliya ta zo, walida taje bakin titi ta auko ta. Su Yaya Halima su ka ce ba sa su yi ba sai Mimi aka yi mawa da Bintu sai Walida sai
Chapter 108 · 0% Book details