Sashe 36
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Meri ta shaida ta bangaran Miji ta gama dace sai dai ba za a ha a samun Ibrahimu da na Danjuma ba acan ita ka ai ne nan kuma ga magajiya da sauran yara to abubuwan dai sai godiyar Ubangiji kawai, sannan tun ranar farko da ta shigo gidan nan take hakuri da kowa kuma ta ko yi zaman lafiya da kowa in ka yi mata sharri sai ita ta saka maka da Alheri ba mai sonta a gidan hatta kannnen Danjuma su anlami kenan Mansoor kuma sai suka sanya masa suna Agola ba acikin gida ba har a waje shi kuma sarkin zuciya ko da yaushe cikin fada suke a dake shi kuma ya fara zuciya yana cika ya na batsewa bata mgana sai dai Danjuma duk wanda ya ta a Mansoor sai inda arfinsa ya are kalamansa kenan yaron nan amana ne a wajena don Allah ku tayani kula da amanarsa. Tun daga lokacin sai suke ganin kamar ya fifita Agola sama da an sa na cikinsa. Tunda sanda inna Meri ta zo gidan ya'yan magajiya uku ne, Auwalu ne babba sai Jummai sai Zuwaira ashe ma alokacin tana da wani aramin ciki amman cikin yara nan ba mai kallon Mansoor a komai sai a matsayin Agola, ko waje ya fita sunan da ake kiran shi kenan tunda sun gama gayama kowa shi ba an gidan su ba ne Agola ne. Ko ya dawo da kuka lallashinsa Inna Meri take yi sai taga ya damu ba shi da wani an uwa na kusa da shi, sai ta yi tunanin gwara ta yi ma Danjuma mgana ya dauko mata yaran marigayiya ta ha a su da yaronta ta rike kila su su kar esa a matsayin an uwa. Yana dawowa ta yi masa mgana sai ya ce daman suna ransa ita ya ke jira kada taga kamar daga zuwanta ya takura mata jin ita da kanta ta ke son a aukosu sai ya ce ta shirya su tafi tare su taho da yaran nan, Haka ko akayi tare su ka je can Bolari gidan su Habiba inda yaran suke, Amina ce babba sai Halima sai aramin yaron Mu'azzamu. Ganin kirkin Inna Meri da yadda ta nuna zata rike yaran sai Mahaifiyar Habiba ta amince ta ba su yaran tun acan gidan Mansoor ya rike hannun Mu'azzam a fuskarsa ka ai Inna Meri ta ga ya yi farinciki, sai taji da i acikin ranta saboda ita macece mai son yara. Ta dauko su Amina ta rumgumesu kamar itace uwarsu ba su ta a maraicin wani abu ba, Mu'azzam kuma ya ke ganin gata saboda karami ne shi Inna Mari ta rene shi har ta sanya masa suna wato n Inna shi kuma Mansoor tana kiran shi Baban inna. Tunda Magajiya ta ga Inna Meri na ri e su Amina kamar ita ta haife su sai ta fara bullo da rigima yau ta ce wannan gobe ta ce wannan a irin haka ne ta tada rigima sai da aka raba girki kowacce sai ta koma yin nata saboda a zauna lafiya, Ita a tunaninta kamar Baba anjuma na cutar da ita ba ta duba da cewa an uwan Habiba na yi ma yaranta sako itama daga su Yalwa tana samun alherai ma su yawa sai take rage ma Baba Danjuma wasu hidimdimun, sai da aka raba girkin Magajiya ta gane kuranta tunda a baya da girken ke ha komai Meri ta barshi a na su gabadaya da aka raba kuma sai ta ja bangarenta ita da ya'yanta. Ba ta shekara a gidan ba ta samu ciki lokacin Magajiya ta haihu an samu Namiji Saddiqu, ita kuma sai ta haifi mace aka saka mata suna Fatima suna kiranta Bintu, sai ta ha e kan anta gaba ya saboda ba ta nuna bambamci suma kuma yaran ba su da wata uwa da ta wuce Inna Meri. Ko can gidan kakkaninsu suka je ba su da labari sai Inna ta ma na kaza tana mana kaza sai iyayen Habiba suka samu salama da cewa su Amina sun samu wata uwar kamar Habiba sai su ma suka maida Inna Meri kamar a duk wani abunda za'a yi a gidan tare da ita a ke yi sannan in yaran suka samu hutu suna zuwa can su yi musu Hutu shima Mansoor tana tura shi can wajen su yalwa ya gaishe su. Tana da cikin walida Muftahu ya rasu har ya yi aure ba jimawa ciwon ciki shima daga dare zuwa Safe, Inna Meri ta yi kuka nata mutuwan mijin kawai take tunawa, duk da shekarun sun ja amman ta kasa mantawa, sannan ga halin rayuwar da suke ciki samun Baba anjuma ya ragu ga iyalai da hidimdumu Allah ma yasa su Amina suna samun taimako daga dangin Habiba shima Mansoor daga can mallam sidi ana yi masa sa o Yakubu dake bauchin in ya zo can kwami yana ba da sa on kayan sawa masu kyau sai Yalwa ta aiko yaronta da shi ko kuma ita ta zo ta kawo masa da kanta. In kuma aka kawo kayan Mansoor zai auki ka an sauran ya ba ma aninsa Mu'azzam in Inna Meri ta ce sun yi masa yawa sai ya ce"In ya ara girma sai ya saka Inna." Tun suna kananunsa kaunar junnasu yake cikin jininsu duk da Mansoor ya girmi Mu'azzam kusan da shekaru biyu da wani abu, amman ji yake yi da shi kamar abokinsa duk abin da ya samu sai ya raba shi biyu ko uku ya auki kashi aya kashi biyu kuma yace na Mu'azzam ne. Kuma ya na fa a da duk wanda yace Mu'azzam ba aninsa ba ne, Saboda su Jummai suna yawan gwaba masa magana da cewa Mu'azzam ba aninsa ba ne shi kuma sai ya ce" anina ne saboda innata take ke rike da shi, in anin ku ne me ya sa magajiya ba ta rike shi ba? Saboda fitinasarsa ya sa suke shayin masa mgana ya ga dama ka zage shi ya rama kuma ba wanda ya isa ya ta a Mu'azzam ko a makaranta yanzu sai aga tashin hankali. Yadda ya ke kafa kafa da shi ko su Bintu da ke mace baya yi musu irin haka Baba anjuma da i ya ke ji in ya ga haka sai ya ce ko bayan raina Meri Mu'azzamu da Baban Inna su ne za su rike mini iyalaina. A can waje kuma bangaren abokai in kana son abota da Mansoor sai ka yi abota da Mu'azzam shi ya sa Mu'azzam ya taso ba shi da abokai sai abokan Mansoor, Mansoor ma ba shi da abokai sai abokan Mu'azzam an sha fa a da tsiya sai an fara abota abu ka an zai ha asu Mansoor ya watse abotan su Nasir ne abokan gasken da ko an yi fa a bayan kwana biyu bayan an gama gaba za'a zo a shirya. Sannan islamiyar su aya kuma boko ma duk tare suke sai abotan su ta jima sannan ko an yi tsiya bayan wani lokaci za'a ha u ko da a filin kwallo ne, da farko Mu'azzam ne ya ke son wallo Mansoor kuma shi kwallo ba ta gabanshi, Saboda Mu'azzam ya fara zuwa kallon wallo har ya fara bugawa duk da shi ra'ayinsa in ya gama makaranta soja yake son zama shi kuma Mu'azzam ya ce yana son ya zama an kwallon kafa. Amman a fili Aji in yana buga balla sai ya baka mamaki ya ware in dai ya na fili sai ya buga kwallo a raga shi yasa lamba goma yake bugawa tun yana matashinsa Mu'azzam kuma dake son wallon har cikin jinin jikinsa bai iya taka kwallon haka ba Su Nasir su yi ta fa in "Aji da za ka sanya ra'ayin ka a kwallo da kila kai ma watarana ka iya zama Ahmad musa ko mu ji ka a turai ka koma buga kwallo da irin su Muhammad sala" in suka fa i haka sai ya gwasale su da cewa"Ina meye wani wallo kuma? Malamai ni fa Soja ne, Sojan kasata in sha Allahu." Kwatan kwacin yadda Mu'azzan ke son zama an kwallon kafa kwatan kwacin yadda Mansoor ke son zama Soja, kowanne bawa daman yana da na shi burin da mafarki sai dai daman ba duka mafarkan mu ke zama gaskiya ba wasu suna zama a raye wasu kuma har kuma ga Allah suna matsayin mattatu ne. A komai na Mansoor ya sha bambam da na Mu'azzam a ra'ayi da hallaya Mansoor yana da fa aa ga zuciya da naci sannan ga riko a cikin kwakwalwarsa har wani waje garesa na musammn kamar blacklist ko sau aya wani abu ya ta a ha a ku to ya kulla da kai kenan har gaban Abada. Sa aanin Mu'azzam ba ruwan shi mai hakuri ne sannan ba shi da fitina shi kuma mai son zaman lafiya ne amman Mansoor bai i gayyar duk ta watse ba, Allah ya sa ma kada a zauna lafiya tun yana araminsa yan gidan wanzamai suka sa ya fahimci ba nan ne asalinsa ba saboda tun baya gane kalmar agola har ya fara sanin ma'anarta. Yasan kan tsiyatu kala kala sannan komai na shi na daban ne, gaisawarsa ma ba irin ta kowa ba ce a cewarsa Ina yini ba gaisuwa ba ce sai dai barka da yamma ko barka da safiya in ya gaisheka a haka ruwanka ne ka amsa ko kar ka amsa shi dai ba zai ce ina yini ko ina kwana ba, shi ya sa ake ganinsa wani mara kunya kuma mara tarbiya. Da gaske ya ci sunan shi na Aji saboda mai Ajin ne ya na da kamewa a kan karan kansa yana yin komai cikin Aji ne da isa, gaye ne da ba ya son reni ko ankani. Shi y ssa koda yaushe maganarsa da su Nasir su zama masu aji su rika abun masu Aji duk da yana da son shiga mutane amnan kuma ya iya miskilanci za su yi ta abubuwan su ba ya saka musu baki sai ya ce su na abu kamar marasa aji, sannan shi mai ra'ayin ya yi aure da wuri ne saboda matarsa ta rika taimaka ma Inna sannan yana so ya ga ya taso da ya'yansa kamar