Sashe 18
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
duk ta tattare su a akinta ita sai abin da ta raba ta aiko mata da shi. Ai in da gaskiya acikin lamarinta Mu'azzam an Danjuma ne, ba ita ta haife shi ba in ta rike kayan da AGOLAN anta ya kawo mata tana kan daidanta, amman na wajen Mu'azzam ko na wajen Amina ko Halima ba ta da hakki a kansu tunda ba ita ce uwar su ba, Magajiya duk ta manta lokacin da uwarsu ta rasu da anjuma ya ce ta rike su tsalle ta da ka ta ce ba za ta iya rike an wata ba. Itama nata sun isheta duk ba ta duba wannan ba sai yau da suka zama wasu take tunanin ba a yi mata adalci ba. Tana tsakar gida tana jajjagen kayan miyan abincin dare da za ta ora Mu'azzam ya shigo gidan cikin shigan kananun kaya gefe aya key in motarsa wata bakar Jeep katuwa ne a hannunsa yana tafe yana ka awa shi fari ne sai dai bai kai Mansoor tsawo ba da ka ganshi ka ga Baba Danjuma saboda suna bala'in ibar kama da shi sosai. Cikin ladabinsa ya gaisheta kamar yadda ya saba shi dai ta na amsa masa cikin sakewa ba kamar an uwansa da ta ce gaisuwan reni yake yi mata. Har ya gota ta zuwa bangaren Inna Meri tana kallonsa ji be sa yadda ya zama kato ya yi kiba saboda ya samu duniya. Kwallah suka cika mata ido, kaf anta ba mai jin da i a gidan auran sa, har gwara ma Zuwaira akan Jummai ita Jummai ai kullum a gida a ke ba ta, ba ta kawo ma uwa ba. Sai dai ta bi ta kar e Auwalu ne Namiji babba shi kuma ya i karatu sai yanzu take jin haushin yadda ta zura masa ido ya i makaranta in da yau ya yi karatu da Meri ba ta isa ta rika mata famkama da kudin su Mu'azzam ba, su ma ai da karatun su ke takama, ba za ta manta yadda Danjuma ya rika fama da shi akan karatu ba ya ki yi, Ita kuma ta aure masa kugun yin abin da ya ga dama ga shi nan daga karshe sai buga bugan gini ga shi ya yi aure ya tara Iyalai shima fama yake yi da kansa. Saddiqu ne bai yi aure ba har yanzu ya na can garin Ikko ya na neman ku i amman sai ya shekara bai zo ganin gida ba sai dai a waya sai sako da ya ke yi musu wani lokacin, shima ba sosai ba tunda Auwalu ya fi shi tausayin iyaye shi kawai domin ba shi da shi ne. Mariya ce ta rage a gabanta ita kuma ai ba ta awainiyarta daga karatu har bangaren Surutu an Meri sun auke mata wannan bangaren kuma duk abin da take so suna yi mata ko jiyan ta ganta da hijabi sabo da takalmi ta zo ta na nuna mata da cewa matar Mu'azzam ta kawo mu su ita da Walida, ta san suna kokari amman bakin cikinta ace Meri ke taimaka mata to na yaushe kuma in taci ta sha su ne, tunda yanzu anjuma ba kasafai ya ke wanzanci nashi ba, ba kuma kamar a shekarun baya da ya yi suna tunda abun na su na gada ne ba haya ba. Duk da tuntuni bala'in magajiya ya sa aka raba girkin bangaren har yau har gobe kayan abinci biyu a ke rabawa, ita rabi Meri rabi ciki har ta san ma sauran anta Kuma har gobe komai in Inna Meri ta dafa sai ta aika mata da shi sai dai in taki ci, ta bar shi nan Mariya ta auka ta cinye. Har ta gama jajjagen ta tunanin yadda rayuwa ta zo mata ba yadda ta yi tsammani ba da gawayi yanzu suke amfani ta fito da murhun gawayin tana kakkabewa dagacan shashen ta jiyo muryan Inna Meri na fa an Inna ba za ka tsaya ka ci abinci ba? anwake Walida ta yi saboda kai." Ta na jinsa ya ce"Sai na dawo Inna, in na tsaya yamma za ta yi." aramin tsaki taja. Tana jin wani irin takaici a kasan ranta, Mariya ta ke jira sai ta mata bugun tsiya Jummai ma tunda ta shige har yanzu bata kara lekowa ba kyafci ta yi ita ka ai ta na girgiza jikinta daga gani za ka san Magajiya ta iya bala'i sannan cutar hassadan dake damunta ne ya sa har gobe ta kasa ganin alherin an Meri ne suka lullu rayuwarta. Ta koma aki kenan taji fitowarsu da mganarsu zuwa shashenta ta ji muryan Jummai na fa in " Mu'azzam ka taimaka min yara nan duk ba sa zuwa makaranta daga bokon har islamiyan an kore su." Ba ta ji dai me ya ce ba ta dai ji Jummai na ta godiya kamar zata kwanta masa, ba inciki ya kara cikata ita da ya kamata ya'yanta su ba da, su ne yau za su koma yan maula suna roko a na ba suna godiya. Muryan Hibba taji kamar za ta shigo akinta yasa zaraf ta aga labule ta fito sai suka ci karo da juna cikin shirinta ga Walida rike da aramar akwatinta sai Mariya dake dauke da Junoir, gaba ayan sune har da Bintu da su Amina suma cikin shirin fita kila duk tare za su tafi ko kafin ta samu damar mgana Hibba ta rankwafa cikin ladabi tana Fa in " Sai anjuma Magajiya yau a Tudun wada zan kwana sai jibi in sha Allahu." Kadahan kadahan ta ce"Allah ya kaimu, ku gaida gida." Mariya ta kallah cikin jin haushinta Mu'azzam kuma ya fice lokaci aya yana fadin"Ku fito mu tafi in na kai ku daga can zan biya wani waje ne." Amina ce ta bi shi tana fa in" Kai Mu'azzam ka ce mu zauna kenan ba za ka dawo da mu ba?. Sun fita can waje suna magana su ma su Binta sai suka rufama musu baya, Mariya ta kallah da ke shirin bin su a fusace ta ce"Ke ina za ki je? Cikin tura baki ta ce"Za mu raka Anty Hibba can ne, Yaya Mu'azzam zai dawo damu a motar sa." Wani irin harara magajiya ta sakar mata kafin ta ce"To ki fita ki gani,wlh sai na yi kasa kasa dake acikin gidan nan" Daga haka ta duka tana zuba gawayi acikin murhun dake gabanta lokaci aya tana kara sakin tsaki, Mariya ba ta da yadda za ta yi dole ta fita waje ta mika ma Bintu Junior ta ce Magajiya ta hana ta zuwa, ba wanda ya damu sanin halin Magajiya duk wanda ke rayuwa a gidan wanzamai ba ma acikin gidan ba har makota su san wacece ita a haka ma ta rage a shekarun baya in ta fara bala'i da masifa sai makota sun ji acikin gida kuma sai su Gaje sun cika tsakar gida suna bata hakuri, abin da ba a ta a ji ba shine nuryan Inna Meri tana tanka mata daga ita har Baba Danjuma masu hakuri ne da kau da kai daga sha'aninta. Da Mariya ta dawo haka ta rika jaraba tana zaginta, Inna Mari na cikin bangarenta ita da Jikokinta ansu Amina tunda za su dawo ta nan kafin su wuce gida sai suka bar mata yara a wajen ta, sai ta yi kamar ta leka ta yi mgana sai kuma ta fasa sanin Halin Magajiya yanzu nan sai cibi ya za ma kari, ta kuma san ta na zagin mariyan ne saboda ta zo bangaranta to ta isa ta raba ta da yan'uwanta ne? har an Jummai ta jii an zagi ubansu an ce su da uwarsu marasa zuciya, daga nan Jummai ta tarkata ya'yanta zuwa gida. Sai ta koma kan Mariya har su Mu'azzam suka dawo tana jarabarta. Inna Meri na bangarenta t na ba ma yan biyun Bintu da suka saka rigiman koko da za su sha, sai da ta mike ta dama musu sannan ta zauna ta a zaman ba su, sauran ma suna gani suka ce suma sai sun sha, gaba aya yaran sun zagayeta Sanda suka shigo Bintu da mgana a bakinta fa i take yi. "Innarmu wai me aka yi ma magajiya take ta bala'i haka? Inna Meri ta ce" Ina zan sani? Tun fitan ku ta ke ta yi ta gama zagin Jummai da Jummai ta tafi gida ta koma kan Mariya ina ga bai wuce dai yinin da ta yi a bangarena tare da ku." Mu'azzam ya samu waje ya zauna yana Fa in"Har yau dai Magajiya ba ta sauya ba? Wai bakin ta baya ciwo ne? Walida tace"Inna mariyan ma ta so bin mu Magajiyar ta hana ta zuwa." Inna Meri ta ce"Bakomai wata rana sai labari, zata daina." Yaya Halima ta zauna a kasa kusa da Inna Mari ta bangaren dama Amina ta zauna a bangaren hagu, Bintu kuma ta zauna kusa da Mu'azzam Walida kuma na kofar daki ta yi tsaye ba ta zauna ba. Yaya Amina ce ke fa in"Inna ai ban tunanin akwai ranar da Magajiya zata sauya. Har Baba dai ya gaji da halinta ya saka mata ido." Bintu ta ta baki kafin ta ce"Dan dai ta samu daga Baban har Innan salausalau ne da irin mu ne da tuni ta raina kanta" Inna Mari ta aika mata da dakuwa tana Fa in"Mungode ja'ira, ai Annabi cewa ya yi duk wawaye ya gani a Aljannah ba masu wayau ba, kum rayuwar nan duka nawa ta ke? hakuri ribar zaman duniya da na biye mata ai ba ta ta a biyo ni bangarena ta yi min wani abu ba, ai hausawa suka ce kulawa yabawa ni dai Allahu shi ne shaida na tunda aure ya kawo ni gidanan nake zaune da kowa lafiya, Alheri ne tsakanina da kowa acikin zuciya ta ba ni da niyar cutar da kowa, kuma ina so ku saka ranku a duk in da kuke ku rike gaskiya da amana sannan ku nufi wanda ma ya nufe ku da sharri ku saka masa da Alheri, ku ma sai ku cigaba da ganin Alheri a rayuwar ku har bayan ran ku." A yadda suka zagayeta za ka fahimci akwai kauna ta uwa da abin da ta