← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 208

Sashe 178

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan bar shi ma," Yadda ta yi mganar ne ya sa dole ya shiga Kitchen in ya na fa in" Ina albasan? Tana mirmishi ta nuna masa ya auka sannan ya dauki wu a, ta nuna masa wani aramin vol ya auka ya fara yankawa a ciki yana uni ta na jin sa sai ta kanne ba ta yi magana ba sai da ta ga ya na ta yankawa manya manya sai ta kalle sa kafin Ta ce. "Haba Aji, sun yi girma yankan" Hararanta ya yi har ya fara ance ido kamar yajin ya fara tasowa. Haka nan ya gama yanka mata sannan ya tace ruwan tea in ya juye cikin flaks in ruwan zafi, ita kuma ta fara soya kwan shi kuma ta ce ya duba buredin a oven, ya cire ya nuna mata ta ce sun gasu ta kar a ta ara sakaa wasu buredin da butter ta maida, ita kuma tana cigaba da soyan wan suna hira sama sama. A tare suka gama sannan Mimi ta gyara kitchen in dakyar Aji ya taya ta aukan Kayan karyawan nasu zuwa Dinning suka zauna saman karyawa, a lokacin ne yake ce mata mganar zuwan su kwami ba ta sai dai zuwa gaba. Cikin mamaki ta kalle shi lokacin tana tura Buredi da wai bakinta sai da ta kur i Tea sannan ta ce"Me ya sa? Kai tsaye ya ce" Nima tafiya ce ta dole ta kamani zuwa Abuja." Sai Mimi ta washe baki kafin ta ce"Gaske? Me za ka je yi?. Nan ya ke gaya kata yadda suka yi da Coach ita kuma ta ce"Gaskiya bai kyautu kace ba za ka je ba. To ya kenan? Ya na kallonta kai tsaye ya ce" Tare za mu tafi Abujan sai ki je gida ki yi adadin kwanakin da zan yi, domin ba zan barki can ba tare za mu dawo." Cikin gamsuwa ta ce" To can Bauchin fa? Sai da ya kurbi Tea shima kafin ya ce"Sai dai zuwa bayan sallah tunda kinga yau sallah bai fi saura kwanaki goma ba." Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Allah ya kaimu da rai da lafiya." Ya amsa mata da Amin Amin, suka cigaba dahiiran su, ba kasafai ya cika fa a mata wasu abubuwan da suka danganci aikinsa ko iyayensa ba, sai in yan hiran na shi suna kusa. Kamar daga sama ta ji ya ce"Fatima kinsan burika na guda uku ne anan duniya? Sai ta girgiza kanta amman ta maida hankalinta a kansa tunda dukkansu sun gama aryawan. "Burina na farko shine Inna ta kasance cikin farincikin da kowacce uwa ke fata, Sannan burina shi ne na kai ta kasa mai tsarki ta sauke farali, na biyun kuma na mallakeki shi na cika wannan burin tunda na same ki, sannan na cika burin inganta rayuwar Inna abu aya ya ragemin na kaita kasa mai tsarki ta sauke farali, ayan kuma zan fa a miki daga baya." Mimi ta yi shuru tana kallonsa kafin ta ce"In sha Allahu za ka cika burin ka, inna za ta je ta sauke fqrali ila ma ba sau aya ba." Mirmishi ya yi kafin ya ce"Ba ni da ku i yanzu duk na yi amfani da su Wajen hidindimu, ga kuma sallah na matsowa akwai sauran hidima amman ina so a wannan shekaran Inna ta je ta sauke farali In sha Allahu." Mimi cikin jin da i ta ce"Allah ya amince,in kana bukatar ku i, akwai ku i a hannuna sai ka yi amfani dashi in ka samu sai ka maida min." Bai ce mata komai ba, sai ta cigaba da fa in" Kuma ga shi ma za ka je wannan taron na ji ana ta zuzuta ka iya taka leda nasan za ka iya kaiwa matakin kaiwa A kungiyar kwallon kafa ta Nageria." Sai a lokacin ya ce"Ni fa ba ruwana da wannan, in da na ke ma ya isheni Fatima a baya ban ta a tunanin zan kai haka ba, Shi ya sa ban cika son tusa kaina ba, matsayin da na kai a yanzu ma Ubangiji ne ya kai ni, ina kuma gode masa ban sani ba ko nan gaba Ubangiji ya ara dagani amman yanzu ni dai ba zan tusa kaina ba. A hakan ma Alhamdulillah." Mimi ta na so ta kara mgana amman sai ya dakatar da ita mi ewa ya yi lokaci aya yana na fa in" Zan yi wanka Fatima." Sai ta mi e suka jera zuwa cikin Bedroom in su kowanne na sake sake a cikin ransa. Yinin ranar yana gida bai fita ko'ina ba sai dai waya kawai.Sai bayan mangariba ya fita ya je gidan Inna suka gaisa, ta yi masa mganar zuwa Kwami nan ya ke gaya mata cewa sai dai bayan sallah tafiya Abuja ta kama shi daman kuma ya yi ma Mimi al wari za su tafi tare ita sai ta sauka a gida Inna tace hakan ma ba laifi, yana gida har a ka yi sallar isha'i kuma sai da ya ci yuwo da miyar ku ewa, da su ka yi waya da Mimi ya gaya mata ga shi ya na cin tuwo sai ta ce itama don Allah ya ce ma Inna za ta ci, kai tsaye ya ce"Ni an aiken ki ne? Ba zan iya daukan tuwo ba." Ta san halin shi ya sa ta kira wayar Inna ta gaya mata tana son tuwo nan da nan inna ta ce a saka mata a Kula Baban Inna ya wuce mata da shi, ya na zaune kai tsaye ya ce"Ni kuma Inna? Daga nan ba gida zan je ba fa." Inna ta harareshi kafin ta ce"Ko ba gida za ka je ba sai ka auka ba na son iyayin banza." Shuru ya yi bai kara mgana ba har Walida ta zubo tuwo da miya a kula sai yake mata mganar yaushe za ta gama Traning in ta? Kai tsaye ta ce"Wata mai kamawa yayanmu., Amman mai shagon ya ce zai rikeni na ri a zama masa kafin lokacin zana jamb in ya yi." Da sauri ya ce"A'a ba za ki zauna ba, ki dawo gida ki cigaba da taya Inna zama." Inna ba ta yi mgana ba daman itama tunda ta gaya mata ta ce ba ta amince kuma daman tasan shima Baban inna bazai amince ba. Inna ce ta ga Walidan ta ata rai sai ta ce"Nima na ce mata ta yi hakuri ita mace ce, ko wannan in ma da ta yi saboda Kun matsa ne. Ni da har shawaran ta fara zuwa can anguwan da muka taso wajen Bahijja yar wajen Dije ta fara koyon inki kada ta yi ta zama ba ta wani abun." Mansoor ya mike lokaci aya yana fa in" To gwara ma can in, ki yi mata mgana Inna abin da a ke bukata sai a sanar da ni." Shike nan ma har ya zartar da Hukunci Dole Walida ta yi shuru, amman ita har ga Allah ba ta son koyon inki yana da wahala, Inna kuma Daman shawara ce nata abin da Baban Inna ya ce shike nan ballantana Baba da duk abin da ya zartar sai ya ce mata ya yi, gwara Mariya auranta za ta yi, itama ta na da samarim amman kuma tunda ta ce karatu za ta yi ba ta da ikon sauya wata mgana daga baya. Tana ji ta na gani Baban Inna ya bar gida bayan inna ta ce za ta kira Dijen su yi mgana ko ita Walidan ta je ta samu Bahijja su yi mgana. Abu kamar wasa aramar mgana ta zama Baba Inna ta kira Dije ta ce ai bakomai an zama aya, ta ce Walida ta fara zuwa gidan Bahijja ita a Tunferre take zaune kuma babbar Tela ce gidanta cike da yaran mata har da matan aure ma ba'a bar su a baya ba, Walida ba ta da ra'ayi amman tunda mai gayya mai aiki ya zartar shikenan Kuma duk abin da ake bukata Aji ya ba ma walida ku i ta siya, kenan ba ta da iko da ta ce ba za ta je ba, an gama mgana da cewa da zaran an yayeta a computer Traning za ta fara zuwa, da ta gayama mariya abin da Yaya Mansoor ya ce itama ta ce ta na so za ta yi kafin auran ta ya zo, tunda wani Lokacin Walida na biyawa ta gidan Magajiya ta yi laushi kamar ba ita ba wani ookacin har cewa ta ke yi, Walida ta gai da Inna amman kunya ya hana ta zuwa gidan innar da kanta. Mariya Auwalu ta yi ma mganar itama tana son koyon inki tunda ga Walida ma za ta fara zuwa da ta ce za ta yi ma Yaya Mu'azzam magana sai ya ce ta bari shi zai ba ta ku in abin da za ta bukata, ba zai zama lalle sai komai Mu'azzam ko Mansoor sun yi musu ba, suma ya kamata su ri a taimakawa da wani abun, Saddiqu dai lagos in ta gagare shi ya koma yana zaman shago, gida duk ya lalace ga dai akin nan Inna ta bar musu amman ba kowa ciki sai tara tarkace Maeesha ke yi, can ma bangaren da Maeeshan ta tashi shima Mariya ce ke tara tarkacenta a ciki, tabbas dai Inna ita ce gida ko shiga da fitan jama'a babu kamar baya. Shi kuma Baba tunda bayan abin da ya fqru ya daina ata bakin shi, ya bar Magajiya da anta duniya ta koya musu hankali daman an ce indan an ciza a hura Saboda gudun ranar nadama kuma ga dukkan alamu nadamar ta fara shigar su. ***** Ana sallah saura kwana shidda Mimi da Aji suka tafi a Abuja jirgi suka bi, ana gobe taron da Mansoor zai hallata. Har gida ya rakani Mimi sai da Mommy ma ta saka baki ya tsaya ya sauka nan ya yi sallah ya ci abimci kwana kuma ya ce ba zai kwana ba, Mimi ta san halin yan kayanta shi ya sa ba ta matsa masa ba, hotel ya kama ya kwana washegari kuma a ka yi taron a Eagless Squeare, An san da zuwan shi tunda ya na wakiltan Gombe United ne ya ha u da shugabbanin Kungiyoyin
Chapter 178 · 0% Book details