Sashe 192
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana nuna sufar jiki ko za ki saka hijabi ne Mimi? Sai ta kalle shi ta ce"Sai in saka in in kana tunanin har yanzu ba ka yarda da ni ba." Da ta ce haka sai ya ce Allah ya ba ta hakuri, In she an ya saka masa wani tunani sai ya yi saurin yin ta'awizi ya kuma tuna cewa ba yadda zai hana Mimu fita to saboda haka sai ya yi hakuri da wasu abubuwam Mimi kuma sai harabasa take yi ta ga ko zai kara yin wani abun amman sai ta ga da gasken ya gyara halinsa. Kuma har a lokacin ba ta gaya masa Alaqar Jaheed da Rukayya ba har manya sun shiga mgana abu ne daman me za'a jira? Har an saka rana wattani shida amman dole Rukky za ta bar aiki da karamci Jaheed ya ce a can zai nema mata aiki. Sai dai Mimi ta ba ma Aji mintin saka ranar Rukayya da Jaheed Baki sake y ace"Mimi abokin nawa fa?. Kai tsaye ta ce"Ya tsaya wasa. Ga an gaske nan ya zo ya auka." Nasir kam da kanta Rukayya ta gaya masa, Ya damu tunda shi a tunaninsa ta na jiransa ya daidaita da iyayensa ne. Jin ga wanda za ta aura ya sa Nasir ya ce"Ni miye laifina da zai huce a kaina ya kwace min dudurwa." Aji ya yi masa rantsuwan Mimi ba ta fa a masa. Kuma saboda ta kure shi har gidan ta sake gayyato Jaheed, tare da Rukayya ba tare da ta gaya masa ba domin ta ara jaraba nadamarsa. Ko da ya dawo ya gansu bai nuna mata wani abu ko a fuska ba, sun yi masabaha da Jaheed har ya bashi hakuri kan abunda ya faru a baya shi kuma ya ce komai ya wuce shima ya na mai bashi hakuri. Rukayya sai a lokacin ma ta san an samu rashin fahimta ba ta yi mamaki ba, ita kawar Mimi ce ta san kishin Aji a kanta. Ita kam har ya na zolayanta da cewa ta yaudare su ta ce su ne suka yaudare ta. Sai yamma suka tafi, Aji bai yi ma Mimi mgana sai da daddare bayan sun kwanta ya kalleta yana fa in"Fatima, wai ke nan har gobe ba ki yarda da nadama ba! Ba ki amince da na ce bazan ara ba? Sai ta yi shuru ba ta yi mgana Mirmishi ya yi ya na rumgumeta lokaci aya yana Fa in"Abin da nake so ki gane har abada ba zan daina kishin ki ba Fatima, ina sonki ba na so kuma ki kasance abun burgewa a idanuwan wasu mazan, gwajin ki a kaina ba shi zai saka ki gane nadamata ba, in na ce zan bar abu to kokari na ke yi na yi ya i da zuciyata a kan haka, na fahimci yarda shi ne kan gaba akan kishi shi ya sa na aminta da ke, ina son ki kuma ba zan daina kishin ki ba kema ina rokon ki aminta da ni kin san ina sonki ina kishin ki. Don Allah ki kiyayewar motsawar zuciyata Mimi" ara shigewa jikinsa ta yi lokaci aya tana fa in" In sha Allahu Merapyaar.." Ya na mirmishi ya ce"Sunan Indiya kuma a ka saka min? A kunnensa ta msa ra a da cewa"Eh My love(Merapayaar) da yaren hindi." Sunan ya yi masa da i ya sa ya yi kyakyawan mirmishi kafin ya ce"Ke kuma kin koma My jan, domin ke ce rayuwata amman Ina son sunan ki, ina jin in kiran ki FATIMA.." Suka kara amkame juna cikin soyayya da muradi, shike nan zaman lafiya ya ore musu kamar yadda ya roketa ta manta baya sannan ta na kiyayewa motsawar zuciyarsa. Tana masa abin a yake so, tana kiyaye abin da baya so,shima kuma ya daina takura mata amman fa mganar kishi, sai da ya rage shi duk da kuma hakan in ya ga abunda baya so zai yi mgana kuma za ta gyara,. Da gaske ne ya yarda da ita, itama ta aminta da shi sai suka samu kyakyawan fahimtar juna, Hankalin Inna ya kwanta tana fatan daga yanzu su rika fahimtar matsalan junansu suna magancewa da kansu. Cikin Mimi na da wata hu u Hibba ta haihu, kuma lafiya lau a gida ta haihu a hannun mijinta.Sai washegari ne suka je asibiti a ka duba ta an samu mace tun a daran Mu'azzamu ya ra a mata suna MARYAMA." *Janafty* *INZB3018* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* Tunda Mimi ta ji labarin haihuwan Hibba shike nan ta fara murnan tafiya kano suna. Ba ma ita ka ai ba hatta su Bintu kowa na ta shiri saboda haihuwanta na fari a gida nan Gombe ta zo ta haihu. Wannan karon ne za'a sha shagalin suna a gidansu da ke kano, Kuma uwa uba kuma Maryama sunan yarinya Inna Meri a ka yi ma takwara sai ya kasance sunan ma na musamman ne. Tun sanda labarin haihuwan ya zo Gombe anwar mamanta ta shirya ta tafi wajen Maijego su kuma nan duk suna shirin tafiya ana gobe suna ne gaba ayan su. In da Allah ya taimaki Mimi haihuwan ranar Jumma'a ce kenan tana da lokaci a weekend sannan kuma daman tana so in ta je ta le a har kofar Soro ta gaida dangin Mommy sannan ta le a har gidan Dr ma so take yi Mera ya bar ta ta yi ko da sati ne sannan ta dawo. Ita ka ai take shirin yin sati ba tare da ta yi mgana da megidan ba. Bangaren Inna kuma tace an yi mata takwara ba za ta zauna ba ta saka a ka yi ma Hibba yajin Jego da kuma garin kuni mai yawa wanda zai taimaka wajen ciko mata da ruwan mamanta. Sannan kuma ta saka su Halima kowa ya kawo abin da yake da shi, a ha a na kayan suna, su ma suka ce za su yi kan jiki kan karfin su in dai a kan Mu'azzam ne. Anty Halima turmi biyu ta kawo da kayan jaririya da sabulai, Yaya Amina ma haka Bintu kuma wani less ne mai tsada wanda ta siye shi da ku in adashen da ta yi, Inna Meri kuma da an kuda en dake hannunta itama ta sa ka aka siya turmin Atamfa da kayan jaririya masu kyau guda biyu. Ba ta yi ma Mansoor mgana ba sanin ko ba ta yi masa ba zai iya bakin okarinsa. Maganar kawai ma su zuwa suna suka yi tunda akwai masu zuwa da yawa sai yace gwara a auki tashar mota kawai tunda da Magajiya ta zo mata barka ta ma ta mganar zuwa sai ta ce baza'a bar gida ba kowa ba ga Zuwaira ta ce za ta je, to fa tunda a ka ji Mansoor zai yi tashan mota sai kowa ya mi e yace zai je Harda Jummai da matar Auwalu ga matar Saddiqu ma Walida da Mariya ma sun ce za su je. Sannan a gidan su Baba anlami Inna ta ce ko Gaje ko Harira ga kuma can gidansu Hibba ko mutame biyu ne za'a auka. Ranar Alhamis daga camp Mansoor gidan Inna ya sauka kan mganar motar, dama sun yi mgana da aron Baba anlami mai jan motar sharon, shi zai kai su sannan ya koma in an gama suna ya auko su tunda daman yana zuwa kano kaduna ne daga nan Gombe. Mansoor ya sha mamaki da Inna ke yi masa lissafin masu zuwa cikin nuna mamakin sa ya ce"To ai motar ma ta cika Inna? Haba abu sai kace biki? Sun yi yawa ya kamata komai a yi shi da tsari ne. Inna ta gyara zama ta na fa Bakomai arzi i ne, kuma dukkansu ba su san gidan ba. In ba domin haihuwan ba wa zai ta shi yace zai je Baban Inna? Kuma wa kake ganin a cikin su bai cancanci zuwa ba? Daga an'uwanss sai yan uwan matarsa sai annensa a ciki wa kake ganin za'a ce ba zai je ba?. Tun da ya ji Inna ta fara magana ya yi shuru ya san daman karatun za ta ora masa kenan amman sai da ya ka a kai kafin ya ce" Duk da haka dai Inna a yi abin hankali mana, shima Mu'azzam in wata awainiyar za a ara ora masa kada ki manta haihuwa a ka yi masa ya yi hidima Inna." Inna ta na mirmishi ta ce"To duka duka kwana nawa ne? In sun da e fa kwana hu Da sauri ya ce"A'a kwana biyu za su yi Inna, zan ma gaya ma su Yaya Halima kada wacce ta fi haka." Inna sai kawai ta ka a kafin ta ce"Allah ya sa su je lafiya su dawo lafiya." Ya amsa mata da Amin, suna zaune ne daman dukkansu a saman kujerun falon, ita ta na daga gefe shi kuma ya na zaune saman kujera mai zaman mutum biyu yana danna wayarsa suke wannan mganar da Inna.. "To ita Bintar za ta samu zuwa ko? Kai tsaye ya ce" Eh za ta je, amman Inna kina ganin ya kamata Walida ta tafi? Sai a bar ki ke ka Inna ta balla masa harara kafin ta ce" Yarinya ce ni da za ka ce a barni ni ka ai? Ta je abun ta Allah ya dawo su lafiya kafin na haife ku ai ni ka ai nake zaune miye a ciki? Sai kawai ya ka a kai kafin ya mike yana mata sallama sai ta ce ya tsaya ya ga kayan da suka tara dole ya koma ya zauna Walida ta kwaso masa kayan, bai ko aga ba amman ya kallah kafin ya yi mgana Inna Meri ta yi masa bayanin abin da suka hada sannan ta ce azu da yamma Matar Auwalu ta kawo turmi da omo da sabulai ta ce na ta da na Magajiya Auwalu kuma dubi biyar ya ba da gasu a hannu. Kai tsaye ya ce Allah ya saka albarka. Sai a lokacin ya tuna da ana ma fa wani abun in an haihu duk da ya turama Mu'azzam in 100k ya kara amman sam hankalinsa