← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 208

Sashe 165

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Hankalin Mimi ya yi bala'in ta shi. Jikinta sai rawa yake yi, ba ta ma san Jaheed ya ri e ta ba sai bayan da Aji ya bar gidan sannan ta juya da sauri ta koma cikin falon tana rawan jiki da na zuciya saboda tsabar firgita da Irin kallon da ta ga Aji na yi mata Kamar za ta fa i har da gudu take ha awa Jaheed ya bi bayanta yana kiran sunanta amman ina ko jin sa ma ba ta yi, wayar ta na cikin akinta a gaggauce ta shiga ta auko wayar ta fara lalu an lambar wayarsa ta fara kira amman tana ta ringing amman bai auka ba, da wayar ta tsinke sai ta ara kira wajen kira a jere ya fi sau goma amman bai aga ba. Haka ta fito falo a firgice sai suka ci karo da Hajiya da ta fito daga akinta amman yanayin da ta ga Mimi ne ya sa ta san ba lafiya saboda ba ta ma tsaya ba sauri sauri ta wuce ta, Sai Hajiya ta bi bayanta tana kiran sunanta. A falo Jaheed na zaune Baaba Uwani na zaune a kasa a gefensa ta na ta yi masa surutu amman da alamu baya sauraranta mamakin irin tashin hankalin da ya gani a tare da Mimi ne kan wannan Mijin nata da ta ce ba ta son auran yanzu. Kawai yana zaune sai gani ya yi ta dawo falon kamar za ta fita saboda tsabar ru ewa. Sai ya mi e da sauri yana kiran sunanta daidai hajiya ta kawo cikin falon, ta tsaya kawai tana bin su da kallo cikin mamaki, Mimi ta rasa ina za ta je ta ji da i, ha waya a hannunta tana sake kiran Aji amman tana ta ringing amman ba ya auka, Jaheed kuma ya ariso kusa da ita lokaci aya yana fa in" Mimi wai saboda ya ganmu ne kika ru e haka? To ba kin ce sakin ki zai yi ba? Tana jin shi sai ta yi kamar ba ta ji ba, Ta cigaba da kiran wayarsa tana matsawa daga gaba zuwa baya. Ganin ba ta tanka sa ba sai ya saka jannu ya ri o hannunta lokaci aya yana fa in" Zo ki zauna..' "Kar ka ara ta ani.." Haka Mimi ta fa a a fusace kamar za ta yi kuka tana yi ma Jaheed wani irin kallo, Hajiya ta karisowa tsakiyar falon lokaci aya tana fa in" Me ke faruwa ne? Ita kuma Baaba Uwani fa i take yi. "Subhanallah Binta me ya faru" Jaheed kuma sai ya tsaya sororo yana kallon Mimi wacce ta cigaba da danna wayar ta. Sai Hajiya ta juya tana kallon Jaheed lokaci aya tana fa in" Jaheedu me ke faruwa ne? Shi ne ya an yi bayanin ain da ke faruwa ya arishe da fa in" Ni ban san me ya faru ba kawai na ga duk ta ru e saboda ya zo ya ganmu tare ya fita a fusace ta bi shi tana masa magana ya yi banza da ita. Saura Ka an fa ya ture ta da mota Hajiya." Hajiya ta yi shuru ta na kallon Jaheed kafin ta ce"Dole za ta damu mana, mijinta ne fa kuma ba da i ya zo ya ganku tare." Cikin mamaki ya ce" Mijinta kuma? Ba ta ce ba ta son auran ba yanzu? Sai Hajiya ta kasa mgana Mimi kuma tana cikin tashin hankali amman sai da ta watsa ma Jaheed wani banzan kallo kafin ta ce"Da na ce zai sake ni ai ban ce maka ya sake ni ba. Wanda yake ma tunanin zai sake ni to ya daina bayan sallah zan koma gidan Mijina." Tana gama fa in haka ta wuce fuu,Sai ya bita ya na ara kiran sunanta kawai sai ta juyo a fusace cikin tsawa tana fa in" Don Allah ka kyaleni, wannan bala'in da me ya yi kama! Kai ba ka ga abin da ka ja min ba ne? In ba so kake yi ka kashemin aure ba ka fitar mana daga gida" Cikin mamakin kalamanta Jaheed ya nuna kansa yana fa in" Ni yau kike kora daga gidan nan Mimi?. Kai tsaye ta ce"Eh In dai alheri zai kawo ka ba. Ni ce kuma na gaya maka ina da aure kaai na bibitayata Allah ya baka wata wacce ta fini." Daga haka ta yi wucewarta ta bar sa nan tsaye baki bu e Baba Uwani ne ke ta jinjina kai, Hajiya kuma sai ta koma ta zauna ta yi shuru ba ta yi mgana ba. Jaheed ya ka a kai kamar ya yi kwallah kafin ya juya yana fa in" Sai da safe Hajiya.". Ba ta ma amsa masa ba, Baaba Uwani ce ke ce masa bai ko ci wani abu ba ya tsaya mana ya sha ruwa anan ko sauraranta bai yi ba ya fice daga falon da sauri. Baaba Uwani ta kalli Hajiya kafin ta ce"Hajiya ba ki tsaida shi ba? Hajiya ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" yale shi kawai." Baaba Uwani ta yi shuru kafin t a ce" Shike nan Hajiya" daga haka ta wuce ta shiga Kitchen ita dai har ga Allah tana tausayin jaheed sannan ya fi mijin Binta fara'a da son mutane, kuma ga na gida ai gwara na gida da wani bare. Hajiya ta ha o ma kayan shan ruwa ga abincin da a ka shiryama Aji nan a kamalle waje aya, Mimi kuma na cikin akinta ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta kira wayar Aji kamar ba gobe amman bai aga ba. Gajiya ta yi ta hakura ta koma ta zauna Gefen gado kamar ta yi kuka, kanta ta dafe lokaci aya tana fitar da huci daga bakinta. Wannan wani irin kishi ne. Wannan kishin na Aji ya na bata tsoro kada ya zame mata wata matsala anan gaba, tunanin kiran Mu'azzan ta yi, Sai ta ga ya na nesa ba amfanin kiran shi. Har Nasir ta yi tunanin kira sai ta fasa. Sai daga baya tunanin kiran wayar Inna Meri ya fa o mata amman kuma ta na jin Kunya tun bayan barowanta gidan ba ta ara kiranta ba sai yanzu ta kira ta ce ta na neman anta. Abun da kunya kamar ta fasa amman kuma ta kasa hakura ta ri a Allah yasa wayar tana hannun Walida Allah kuma ya amshi addu'arta, tana kiran wayar Inna Walida ta auka ita kuma damab wayar na hannunta, pokacin da ta ga Binta ta auka Bintu ne ba ta ma tsayawa dubawa ba ta auka sai ta ji muryan Mimi tana fa in" Walida ce? Sai walida ta sake ago wayar tana ganin mai Kiran sai kawai ta daga tsalle tana fa in" Anty Mimi". Ta fa a cikin tsananin murna. Daman wayar na hannunta a cikin akinta tana faman latse latse. "Walida Yayanki na gida? Haka kawai Mimi ta fa a.Sai walida ta ce"Anya? Ba ya nan me ya faru? Sai kawai Mimi ta ce"Bakomai ki gaida Inna." Sai kawai ta katse kiran, abin ya ba ma Walida mamaki ta bi wayar da kallo, to kuma me ya faru? har ta shi ta yi ta fita falo ta iske Inna na zaune daga kallo ta fara gyangya i haraban gidan ta leka ta ga motar ba sai mashin tabbacin Yaya Mansoor ba ya gidan kenan sai kawai ta koma akinta, Ita da Junoir wanda tun azu daman ya yi barci amman sai da ta kashe tibin dake ta yi shi ka ai, domin Inna na zaune sai faman gyangya i take yi. ***** Mimi na jin cewa Aji baya gida tunaninta ya ba ta yana Camp in su, duk da ba ta ta a zuwa ba amman tasan wajen yana cikin gari ne. Sai kawai ta auki mayafi ta yafa ta zura wani saukak un takalma ta fita falo ta iske Hajiya na shan kayan marmari ita da Baba Uwani ba ta ma tsaya ta kansu ba ta fa a Kitchen, ta kwashe abincin da ta yi ma Aji ta zuba acikin kwando mai zif ta zage sannan ta fito falon a gaggauce tana fa in" Hajiya zan je na dawo." Cikin mamaki Hajiya ta ce" Ina kuma za ki Binta? dare fa ya yi kuma kin yi Azumi amman komai ba ki ci ba." Kawai wucewa ta yi tana fa in" Hajiya sai na dawo zan iya cin wani abu." Kafin ma Hajiyar ta sake wata mgana ta fita, Sai da ta fita ta tuna ba ta auko Key in Mota ba sai ta dawo da gudu gudu ta koma aki ta auko Key in motar ta fice ta na jin Hajiya na fa in"Binta dare fa ya yi" Ita dai ta fice tana fa in" Hajiya ba zan da e ba. In sha Allahu" Ko ba ta fa a ba tunda Hajiya ta ga ta kwashi abinci ta san in da za ta je. Sai kawai ta ka a kai ta cigaba da shan kankanarta, Duk Binta ta jaa ma kanta da ba ta baro akinta ta zo gida ba da duk haka bai faru ba, Baaba Uwani ko mgana ce a bakinta amman yadda Hajiya ta kame fuskarta ya sa ta kasa furta wani abu. Megadi ma ya yi mamakin fitar Binta da daddare abin da ba ta yi, duk tsiya ana mangariba take dawowa gida. Amman yau bayan mangariba wajen takwas saura ta shiga mota ta fita sai dai ya bi ta da fatan dawowa Lafiya, ita kuma tana tuki amman hankalinta na kan wayarta tana ara kiran lambar Aji anman bai auka ba. Kusan acen hanya ta yi ma sai da ta sake komawa tunda ta manta wajen daga karshe sai da ta tsaya a bakin hanya ta yi tambaya sannan a ka yi mata kwatance kai tsaye sai ga ta a bakin get in Gombe United Camp. Akwai Security masu kula da shiga da fita domin tana zuwa sai suka hana ta shiga tun da ba su ta a ganinta ba. Sun tambayeta wa take nema? "Mansoor Aji.." Kai tsaye Mimi ta fa i sunansa. Security in
Chapter 165 · 0% Book details