← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 208

Sashe 49

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta hakuri Mommy ma na ba ma Hajiya hakuri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce"Bakomai Murja wata rana Kabiru zai yi nadama, sai dai ina fatan Lokacin da zai yi nadamar lokaci bai kure masa ba. Alhaji Hamza a lokacin ya nema musu jirgi suka juya zuwa Gombe kuma har suka bar gidan Major bai fito daga aki ba, Mimi dai kuka ta yi kamar zata ba ma uku lada domin ta so ta bi Hajiya su koma gombe Hajiya ta girgiza kai kafin ta ve"A'a ki zauna ki yi ma mahaifinki biyayya shi ya haife ki ya fini iko da ke, ina miki fatan Allah ya sanya hakan ya zama alheri a rayuwar ki Binta ki yi Hakuri kin ji ko? Mimi tana ji tana gani Hajiya ta tafi ta barta daga nan ta fahimci ta rasa wani hop, domin Mommy ba ta isa da ja da hukuncin Abi abunda ya fa a tabbas haka din ne zai kasance. Tun daga wannan daran Mimi ta ke kukan Rashin Aji a rayuwarta kukan da har tsawon shekaru goma ba ta ta a dainawa ba. Kuma wannan zafin da kirjinta ya soma tun daga ranar ne, to shi ya haifar mata da ciwon da har gobe bai warke ba. ****** Labarin abin da ya faru da Mansoor ya za ga gari ba wanda bai sani ba. Wani tarihi ne da shi kanshi ba zai ta a mantawa da shi a rayuwarsa ba, sannan tarihin dafin soyayyar da ba shi da magani. A ranar kwanan hanya suka yi zuwa Gombe tunda Mota ce ga Mansoor ba lafiya kafin su isa duk jikinss ya kara tsami, Allah ya sa Baba anjuma ya riko ku i a Hannunsa Inna Meri na cikin tashin hankali ba ta tuna da wannan ba. Motar da su hayo ma daga tasha Sai da Baba sani ya biya, suna ta fa a da masifan yaro ya jawo musu bala'i, sai dai suna ganin halittar da Mansoor ya koma sai suka yi shuru domin su kansu sun san yaron ya kai kanshi in da ya kusa mutuwa. Jinya ce sosai Mansoor ya yi domin ya samu targade da gocewar kashi sama da hu u a jikinsa ga raunika a saman kansa ga tsamin jiki ga raunin dake cikin zuciya wanda ido ba ya iya gani. Shi ka ai yasan irin unar da zuciyarsa take ciki, ciwo dai idanuwana ba sa iya gani sai shi ka ai da zuciyarsa ke cikin kirjinsa ya san halin da ya ke ciki. Makota haka suka yi ta tururuwan zuwa ganinsa wasu duk saboda gulma ne, wasu kuma domin ganin abunda ya faru mata kuma suna ta zuwa yi ma Inna Meri barka da arziki. Su Baba Sani ke kara ma lamarin magi da gishiri suna ara abunda bai faru, har suna cewa shi kanshi Yaya anjuma da Merin dakyar suka sha domin yaron ya je ya jawo Yar soja an kusa kashe shi fitinarsa ya sa yau ya kusa janyo abin da zai saka har su a kashe su a banza. Nasir da makama kullum suna gidan wajen Mansoor dake kwance ya na jinya, Ahmad kuma sai da ya dawo garin ya zo ya ga yadda Mansoor ya koma shuru shuru ba ya mgana kamar an sauya shi. Baya cin abinci baya mgana ba ya fara'a ko da yaushe ya na kwance yana fama da kuncin zuciya. Kullim mganar Inna Meri shi ne" Baban Inna ka mike ga kanka wannan kwanciyar ba zai yi maka kyau ba" Sai kuma ta saka masa kuka, Baba anjuma shima ko da yaushe cikin yi masa nasiha yake yi. Su Nasir ma koda wani lokacin cikin fa in " Aji ba fa karshen rayuwarka ba ne ya zo, Mimi ba ita ka ai bace mace a duniya ka mike ka gina rayuwarka zaka samu wacce ta fita a gaba." Mu'azzam kuma kamar yafi kowa damuwa maganar kenan" Ka manta da abin da ya faru ka tashi ka kula dani kamar yadda ka saba, ba na jin da in ganinka a haka" Haka su Yaya Amina suna tafe zuwa duba shi kowa na bashi mgana Har can mallam Sidi inna ta aika Yalwa da ya'yanta sun zo har Baban shi Karimu sai da ya zo duba shi. Inna Meri ba ta oye musu abunda ya faru ba ta gayamusu komai. Yalwa na kuka ta ce"Allah ya isar masa ba mu yafe ba." Karimu kuma cikin fusata ya ce"Ke sakarai mi ga kanka, ubanka har ya bar duniya ba lusarin namiji ba ne ka tashi ka zauna da kafafunka domin gina ma kanka kyakkyawan rayuwa anan gaba." Ya san duk abin da su ke fa a gaskiya ne, amman shi a cikin Kirjinsa wutar iyayya ke bayyana, daddare haka zai kwana bai yi barci ba yana kukan zucci, Auwalu bai taba tausaya masa ba sai dai ya ri a dariya yana fa in"Maganin ma su janye janye kenan in ban da karfin hali ina kai ina wannan yarinyar? Tabbas gaskiya ya fada soyayya ta rufe mishi ido da ya sa ya kai kansa inda bai dace ba. Yana so shima ya manta amman ya kasa ji yayi ya tsani duk abunda ya danganci wani aiki mai kaki burinsa na zama Soja tuni ya za ma mattace acikin zuciyarsa. So yake yi ya zauna ya yi kuka amman kuma ya kasa sai ranar da Mu'azzam ke masa mgana ya samu ya riko hannunsa ya danna a kirjinsa yana fa in "Ta nan ne,a nan na ke jin ciwo da zafin abun. Ina so na manta amman na kasa." Kawai sai ya fashe da kuka ya dun ule a jikin Mu'azzam ya na kuka kamar ransa zai fita Mu'azzam bai hana shi ba domin yana so ya samu sukuni. Tun daga wannan kukan da ya samu sararin yi ya samu sauki acikin zuciyarsa, wannan abin da ya faru Shine silar sauya rayuwar Mansoor ya koma rayuwa shi ka ai ya koma Shuru Shuru sannan mai riko sannan bakar zuciyarsa ta kara ninkuwa sama da sau goma. Daga lokacin Inna Meri ba ta kara takawa gidan Hajiya ba, Hajiya ma ba ta kara nemanta ba alaqar ta are. Ana ta masa mganar ya koma makaranta shima sai ya yi tunanin gwara hakan zaman ya ishesa. Da taimakon gonakinsa na gado aka saida ya samu ya fara karatu a gurbin Jami'ar Gombe state University. Sun ba shi Agric kuma bai sauya ba saboda shi ya riga ya gama sarewa da duk wani burin shi. Da farko tare da Mu'azzam za su shiga sai kuma Alhaji Mustapha ya kawo maganar zuwa Police Acadmy Wudil a matsayin Mansoor ya je tunda shi ke son aikin Kaki, amman ina ya ce har Abada da ya zama an sanda gwara ya mutu. Sai ko Mu'azzam ya ce zai je tunda Aminin Alhaji Mustpaha ke shugabantar makaranta Kuma shi ya bashi Upper ta mutum aya. A lokacin tuni shima Mu'azzam ya watsar da mafarkinsa yace shi zai tafi Wudil Mansoor kuma ya ce aninsa ba zai yi aikin kaki ba. Inna Meri tace bai isa ba sai Mu'azzam ya tafi, Mu'azzam in ma ya nuna ya na son ya je. Kawai sai Mansoor ya ce"Ka je ka je, ka za ma duk abin da kake son zama Mu'azzam amman ka sani har Abada bazan ta a kaunar wani aikin kaki ba." Mu'azzam ya auka zuwa gaba Yayan nashi zai rage wannan kiyayyar sai dai kash kiyayyar ta shi mai girma ce har Mu'azzam ya tafi Wudil bai kaunaci wannan karatun na shi ba, Tafiyar Mu'azzam ta kara saka ya zama ya na son ka aici, Saboda zaman shuru in ba shi da karatu sai yake zuwa ya na tsaren wani shago a kasuwa yana samun kudin abun hawa zuwa makaranta, ya daina neman kowa hatta su Nasir ya Guje su. Ko sun neme shi ba ya zama in da za su gan shi, su ma sun gaji da nemansa sun kyale shi a tunaninsu nan gaba zai dawo dai dai. Yana Aji biyu a jami'a Coach na Team insu na Nasara tare da na Tudun wada Team suka zo nemansa akan suna bukatar wani yaro matashi wanda ya iya buga kwallo za'a bashi horo na shekara biyu wata kungiya zata auke shi. Mansoor suka nema tunda daman tare da shi suka rika bin shugabannin manyan Team in su na yan wallo daga na manyan anguwanni har na ananu. A lokacin sai ya ga ya mu su Mu'azzam ne kuma ya tafi Police Acadmy baya nan, Coach in su na Nasara Team yasan Aji ya iya taka kwallo shi ya matsa akan cewa shi Ajin ya zo a matsayin Mu'azzam in mana. Da farko ya i amincewa sai daga baya ya ga to miye aciki? daman shi tuni mafarkinsa ya da e da sauyawa amman bai amince ba sai da ya yi mgana da Inna Meri da Baba Danjuma suka sanya ma lamarin albarka. Sannan ya amince ba zai ta a mantawa da Coach din su na nasara Team ba wato Shehu Master Allah ya jikan sa ya rasu shi ya auke shi ya kai shi wajen Coach in su na Gombe United a lokaci suka yi mgana sosai ya jaraba shi ya gani sai ya ce za'a bashi horo na shekara biyu, shi kuma sai ya ga ya masa yana karatu sai ya nuna masa hakan bazai shafi karatunsa ba. Kwatsam ne fuskar Aji da sunan shi ya bayyana acikin yan kwallon kafa, Ya yi horan shekara biyu sannan aka gabatar da shi a Kungiyar kwallon kafa ta Gombe United lokacin kontiragin Captain in kungiyar saura shekara aya ya kare, tare suka arisa wannan shekaran ayan da Aji bayan kuma ya bar Club okarin Aji ya saka ya samu matsayin Captain saboda daman dalilin da ya sa a ka kawo shi kenan. Shi ne sanadin da ya sa ya zama duk abin da ya zama a wallon kafa, kuma tunda ya riga ya hakura da mafarkinsa sai ya maida kansa ga karatunsa sannan ga wasan kwallon kafa. Shima ya yi singing kontiragin na shekara goma ne da Gombe United sun kuma fara biyan shi albashi bayan alawun da yake samu in suka fita wasa, da haka ya gama
Chapter 49 · 0% Book details