Sashe 196
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Mimi ba ta kwana a asibiti ba, ta dai yini zuwa dare bayan an tabbatar da lafiyanta da na abin da ta haifa a ka rubuta musu takardan sallama amman fa asibitin nan ta ga gayya kashi kashi kama daga an'uwanta zuwa an'uwan Abu Maryam in. Gidanta a ka maidata, saboda daman Aji ya ce ba ya son wankan gida matarsa a gidanta za ta zauna ta yi jegonta sai dai a samu mai zama da ita, Mommy tuni daman ta yi ma Inna Zainaba mgana ta na jin an haihu a ranar ta iso, amman a gida ta same su tunda ba ta taso a kan lokaci ba. Hajiya bakinta ya i rufuwa har da ita a asibiti har kuma suka dawo gida, ta auki Jaririyan ta saka albarka sannan ta kalli Mimi dake zaune gefen gado a cikin bedroom in ta, wani katon Jug ne a hannunta Inna Zainaba ta ha a mata tea bayan sun yi wanka ita da jaririyar. Sai ta ji kwallah ta tarun mata a cikin wayar ido, Allahu akbar yau ga shi Binta ta yi aure har ta kai ga ganin arta a duniya. Sai dai Kabiru baya raye. Burin shi kenan ya ga Binta ta samu kyakyawan rayuwa irin na kowa ta mace. Hawayen nata sai da suka zubo ta share lokaci aya tana fa in"Allah ya ji an kabiru. Allah ya cika maka burin ka Binta ta samu kyakyawan rayuwa mai cike da farinciki da kake yi mata fata." Mimi ba sai hawaye ta tuna da Abin ta amman a cikin ranta ta na yi masa addu'an rahama da dacewa. Su Mama da Anty duk suna gidan har da Mamansu Rukky da Bibi da Nafisan Nasir, Sai su Bintu da Walida da Mariya su Yaya Amina sun tafi kafin mangariba, Inna kuma daman tun a asibiti bayan an haihu lafiya isowar su Mama ta koma gida. Sai can bayan isha'i gidan ya watse a ka bar Inna Zainaba ka ai sai mai Jego ta kasa zama sai kai da kawo take yi domin kula da Mimin wacce ta samu ari sai da a ka yi mata inki tana bukatar shiga ruwan umi lokaci bayan lokaci, Aji bai shigo gidan ba sai wajen goma suna tare da Nasir da makama yau kam bakinsa ya i rufuwa bai ta a tunanin haka a ke jin farinciki in a ka zama uba ba sai yau wayar da ya amsa na barka bai san adadi ba, Mu'azzam daman shi ya fara kiran shi ya sanar da shi Fatima ta sauka an samu wata maryama Mu'azzam in ne ya rika gayama sauran mutane, har su Baba anjuma da rana sun je asibiti sun Duba Mimi da abin da ta haifa. Itama ta bangarenta har sai da ta gaji ta amsa wayoyin mutane, bayan ta dawo hayyacinta na natsu daga gumurzun Naguda ita ai sai dai ta yi ma Allah godiya domin ta samu ciki cikin sauki ba ta yi wahalan laulayi ba sannan wajen haihuwa ma Ubangiji ya sauka a mata, in a ka cire arin da ta samu suka yi mata inki sannan ba ta yi doguwar naguda ba, ko da yake Inna Zainaba tace irin Mommy ce itama haihuwan ta cikin sau i ne kafin ma a tafi asibiti wani lokacin ta haihu, har ita kanta Mimin a gida ta haifeta sai daga baya suka je asibiti a ka duba su. Rukky ce ta fara kiranta lokacin da ta fara amsa waya suka yi mgana bayan kuma sauran wayoyin da ta rasa ba ta amsa ba, ta yi mgana da duka an'uwanta har Mommy suna yi mata barka da arziki har da Madiha da megidanta domin ita kai tsaye ta ce"Congratulation Fatima Kabir Dabo, Za mo wa uwa ba abu ba ne mai sau i. Allah ya raya abin da kika samu ke kuma ya baki lafiya da warin jiki wajen shayarwa tare da tarbiya." Sai ta ji da i da abin da ya kai an'uwa da i a wannan duniya ko da kuwa kuna da tarin bambamcin hallaya ne a tsakanin ku. Haka ma Dr ya ce ya yi ta mata addu'a sannan da fa an ta kula da kanta, shi da Jawahir sau biyu suna kiranta haka ma Hibba da Mu'azzam ta samu wayarasu ita dai ba ma za ta iya kirga wa anda suka kirata ba amman dai abu mafi soyuwa shine babban kyauta ne na Ubangiji ace yau ka na amsa sunan uwa wani farinciki na dabam ne. Farincikin da take ciki ya sa ta kasa daina kallon jaririyar da Aji ya yi mata hu uba da Maryama ba. Mamaki take yi yau itace ta haihu? Haihuwan ma tare da Aji abin da ba ta ta a tsammani ba, har ta cire tsammani kuma sai Ubangiji ya kaddara za su zamo abu aya. Sanda ya shigo gidan akinsa ya wuce ya yi wanka ya sauya ya tsaya ya amsa wayar Coach na su in da ya ke yi masa barka, ya kira shi da safe suna asibiti sai ya tura masa sa on ba zai shigo Camp ba saboda mai akinsa ta sauka shi kuma Coach na jin haka ya gayama sauran an Team da cewa matar Capatin in su ce ta haihu so ranar shi ya jwgoranci morning traning in, abinci da komai da zai bukata Mimi ta fa a ma Inna Zainaba a ka tanadar mishi a saman Dining bai duba abincin ba sai da ya le akin Mimi ya gaida da Inna Zainaba sannan ta fice falo ta ba su waje, gefen gado ya zauna lokaci aya ya na fa in"Me jego." Mimi na mirmishi ta ara kishingi a lokaci aya tana fa in"Na'am Angon arni." Mirmishi suka yi ma juna, sannan ya le a jaririyar dake kwance gefenta tana tasharan barcinta na wani lokaci sannan ya dawo ya daidaita zaman shi. "Sannu da ko ari Matar Aji.." Mimi na mirmishi ta ce"Yauwa Mijin Mimi.". Hannunta ya kama ya ri e yana kallonta kafin ya ce"kin ara kyau, yau ka ai jego nan ya kar e ki." Dariya ta yi amman ba ta yi mgana ba sumbatar hannun nata ya yi kafin ya ce"Ina fatan komai lafiya ko? Ta fara shan nono? Haka ta fa a ya na rike da hannuwanta. Sai Mimi ta girgiza kanta kafin ta ce" Ruwan zamzam ka ai a ka bata, ruwan Nono dai ka an ya fara zuwa kila sai da zuwa gobe haka." "To ba matsala zuwa goben? Ba za ta ji yunwa ba? Mimi na dariya ta ce"Yunwa kuma? Ba za ta ji ba kada ka damu, na sha tea,kuma Inna Zainaba ta damamin kuni na sha zuwa Gobe ruwan nonon zai zo in sha Allahu " Sai ya jinjina kansa alamun gamsuwa, sai kallon Mimi yake yi itama ta na kallonsa ta na nasa mrmishi, ita ta auko yarinyar ta ora ta saman jikinsu dukkansu biyun a tare suka rike ta, sannan ayan hannun Mimi ta saka ta sakalo bayan Aji da shi, sun ha e yarsu waje aya sun rike. Ya ri e hannun jaririyar ya ha a da na Mimi ya damke kawai ya na mirmishi ya kasa mgana. "Ka ga Kyautar da ubangiji ya yi mana ko? Yau mun zamo iyaye ma'ana mun zamo uwa da uba daga yau, nauyi ya same mu mun zama iyaye akwai ha armu a kan mu na tarbiya da kula da ita." ura ma jaririyar ido ya yi ta na ta barcinta sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce" Allah ya raya ki Inna ta, " Haka kawai ya fa a ya na cigaba da kallonta In Mimi ta na mgana sai dai ya aga kai ya kalleta ya yi mirmishi kamar yau sauran kalaman bakinsa nasa sun auke. Ya dai kalleta cikin wani yanayi ya ce" Na gode sosai, na gode da kika yi dalilin jin wannan farinciki a matsayina na Uba na gode kwarai da kika kasance a cikin rayuwata Fatima kika kuma bani dukkan farincikin da gata a zamantakewar mu na aure. Na gode miki bisa yardan ki, ha urin ki, Ko arin ki a kaina Allah ya shirya mana Maryama ya ba mu ikon yi mata tarbiya ita da sauran an'uwanta da suke tafe nan gaba." Kanta ta ora saman kafa ansa lokaci aya tana fa in"Amin Amin Mera. Nima na gode da ka yi sillar zamowa ta Uwa. Allah ya bar mu tare Amin." Shima kansa ya jinginar saman kanta yana amsa mata da Amin Amin, sun auki lokaci a haka sannan Mimi ta ago da kanta tana fa in" Na manta ka ci abinci kuwa?. Sai ya girgiza mata kai da sauri ta kar i Jaririyar daga hannunsa lokaci aya tana fa in"Yana can saman dinning." "Me kuk dafa ne? "Jallop rice ne Bintu ta dafa azun nan kafin su tafi, sai na ce su saka maka Food Flaks kada ya yi sanyi kafin ka dawo" Kai ya jinjina kafin ya mi e lokaci aya yana fa in"Kuma sai da kika yi mgana na tuna ina jin yunwa tun tea da na sha da safe ban kara cin wani abu ba." Mimi na mirmishi ta ce"Na sani, na ga duk ka fara rama ne." "Zo ki rakani mana, ni ka ai za ki bari naci abincin? Ta na yar dariya ta ce"Jego fa na ke yi Mera, ba'a son na zauna wajen sanyi Inna ma ba za ta barni na fita falo na bar yarinyar nan ita ka ai ba. Da sauri ya ce"Tare da ita za ki taho, ina cin abinci ina kallon ku ina jin adi." Mirmishi ta yi masa kafin ta ce"Haihuwa fa na yi jego nake yi, in na fita Inna za ta min fa a sai ka yi hakuri fa." Dakuna fuska ya yi kafin ya ce"To shi ne me? Jegon dai ba a haihu a taru a yi suna aci abinci ba ne? Ina ce shike nan an gama jegon.? Ta na