Sashe 87
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sulale ta ra a ta gefensa ta fice daga akin zuwa nata akin amman zuciyarta na wani harbawa da karfin gaske. Shi kuma yana ganin ta fita sai ya duka ya fara okarin cire takalmin kafarsa da sauri Inna ta ce" A'a nagode da haisuwa yi tafiyar ka akin matar ka sai Allah ya kaimu." Sai ya yi ajiyar zuciya ya mi e yana fa in" Inna Baba ya shigo kuwa? Ta gya a kai kafin ta ce" Eh ya na akin sa, sai dai zuwa gobe da Safe kafin ya fita sai ka ra ka Bintar wajen sa ya ganta ko? Sai ya bu e baki yana fa in" To Inna." Kunya yake ji ya juya yace sai da dafe, Walida ya juya ya na nema wanda tun shigowarsa ta shige ciki sai ya wala mata kira ta amsa ta fito da sauri. Ledan hannunsa guda aya ya mika mata ta kar a cikin girmama sannan ta juya ta dire a gaban Inna Meri, ita kuma sai ta auka ta bu e ta ga kaza ce dagwaleliya aciki sai fura mai sanyu leda biyu a ciki, Sai kawai Inna ta gya a kai kafin ta ago tana kallonsa tun kafin ma ta yi mgana da sauri ya juya yana fa in" Sai da safe Inna." Sai kawai ta amsa da cewa" Allah ya tashe mu lafiya Baban Inna." Sai da ya fita sannan Walida ta dira kan leda tana fa in" Inna fura, wallahi furan ce wanda Yayanmu ke siyo miki mai shegen da in tsiya." Inna Meri sai ta sakar mata ledan lokaci aya tana fa in" Ni dai furan zaki juyemin leda aya." Da sauri Walida ta ce" Inna kazan fa? Ba za ki ci ba? Sai ta girgiza kai kafin ta ce"Ke dai ki ci iya cin ki walida." Ai sai Walida taji kamar an sakata acikin Aljannah yau ga ta ga Kaza ita ka ai ko da ya ke daman in dai ya siyo ma Inna kaza ko nama ko tsire ka an take ci, wani lokacin ma har ya kwana sai an yi baki ta auka ta ba su, da Walida ta fahimci haka sai ta ri aukewa tana cinye tun kafin ma a yi bakin Inna ta kyautar da shi, yanzu ma bayan ta samo kofi ta juye ma Inna furar ta, itama sai ta juye nata a wani aramin kofi ta juya baya ta fara yagar kazan tana yi tana kur an furan lokaci aya kuma ta na latsa waya har hoton kazan da furan sai ta auka aranta ta ce sai ta nuna ma Binta itama ta ci kazar amarcin Anty Mimi Inna na gefe ta na kallonta amman dai ba ta yi mata mgana ba, ita a lokacin addu'a ta ke yi acikin ranta Allah ya dauwamar da zaman lafiya a tsakanin Baban Inna da Binta ya kuma kauda fitina yasa ace gwara da aka yi. Koda ya tura kofar akin ya isketa a bu e shi ya sa ya saka kanshi kai tsaye a cikin akin, ko'ina fes ya na tashin kamshi sannan ga hasken wuta ya haske tsarin akin gaba aya, bai takura ma kansa sai ya are ma akin kallo ba iyaka ya arisa tsakiyar falon ya sauke ledan hannun sa, a saman center table in da ke tsakiyar Falon lokaci aya ya na zaman saman kujeran da ke fuskanta wajen. Sai a lokacin ya cire takalmin kafarsa ganin ya na taka cafet in da ke tsakiyar akin, mikewa ya yi zuwa bakin kofa ya ijiye takalmin sannan ya dawo in da ya tashi. Wayarsa da key in mashin in sa ya ara ijiyewa saman kujeran da ya zauna a kai sannan ya aga ido yana are ma falon kallo tsit sai aran fanka Mimi ba ta falon a lokacin da ya shigo shi kuma daman sallaman sa iya saman Le ensa ya yi ba lalle ta ji shi ba, amman ai ta na daga ciki zaune agefen gado taji motsin shigowarsa tun ta a saka ran ganinsa ya shigo har ta cire ran ba zai ta a shigowa ba. Sai ta mi e ta gyara mayafinta ta fita zuwa falo cikin takun sanyin ta a koda yaushe. Yana zaune ya har e hannayensa a saman irjinsa ya na kallon gabansa da alamu kamar ya na nazarin wani abu ne, ya ji shigowarta saboda tun a akin Inna ya ji kamshin turarenta da ya shigar masa hanci tun a lokacin, amman yanayin sa bai saka ya nuna yasan da wanzuwarta a cikin falon ba, har sai da ta tsaya daga can gefen ta kofar bedroom in ta cikin yanayin mganarta ta ce" Sannu da zuwa." agowa ya yi yana kallonta ita kuma kanta na asa ta na wasa da mayafin dake jikinta amman dai jikinta yana ta rawa ka an alamun kamar ta na jin tsoro ko fargaban wani abu. A saman le ensa ya amsa mata gaisuwarta daga haka kuwa tsawon mintina goma sai kawai ta juya za ta koma ciki sai ya yi gyaran murya da ya sa ta tsaya cak amman ba ta juyo ba sai ta ji yana fa in" ki zo ki auka ga sa o nan." Sai ta juyo a sanyaye tana fa in" Na'am" Da jannu ya nuna mata ledojin gabansa, sai kawai ya dau e kansa,ita kuma sai ta fara taku zuwa in da yake nuna mata, ta auki ledojin duka biyu ba ta bu e ba sai ta juya ta isa gaban aramin Fridge in dake falon nata, sai ta bu e domin ta saka acikin ranta tasan kila nama ce ko kaza, amman sai taji kamar wani abu mai ruwa ruwa sai ta le a cikin ledan ta ga fura ne mai sanyi nan da nan ranta sai ya biya daman tana son fura sosai amman cikin ta ya cika sai ta yi tunanin sai gobe da safe sai ta sha shi ya sa ta saka ledojin gaba aya ta sake rufe fridge in. Kai tsaye ta kama hanyar sake komawa cikin akinta sai ta ji muryansa. "Zo ma na." Abun sai ya bata mamaki, wai zo? kamar wata yarinyar da farko ta so ta yi wucewarta ne kamar bai san sunan ta ba, amman sai kuma ta yi wani tunani da ya sa ta juya ta koma ta zauna saman kujeran da yake kallon wacce ya ke zaune amman ba ta kallesa ba kanta na asa ta na ta wasa da zoben gold in dake hannunta na hagu, shima ba za a ce kallonta yake yi ba domin a fuskarsa ba za ka iya gane yanayin sa ba shi ba fara'a ba sannan shi ba dariya ba Kadahan kadahan dai, shuru har na tsawon mintina goma sannan ya muskuta kafin ya fara da fa in" An aura aure mana shekaranjiya tun ranar kika tashi daga budurwa ki ka koma matar aure ma'ana dukkan wani ha in ki ya na saman wuya ne, kula da tarbiyan ki da dukkan wani abunda ya shafi rayuwarki zan sani kafin wani ya sani, ki sani zaman ki a budurwa dabam zaman ki a matsayim mai aure dabam, to ki saka tunanin sabuwar rayuwa za ki fara, za ki zauna tare da mahaifiya ta, kin san ta kin san matsayinta a wajena ki girmama ta sannan ki yi mata biyayya , ban amince da ki shiga akin kowa ba sai na Inna sai dai in wani abu ya faru za ki iya shiga ki yi jaje, ba na son tashin hankali ki zauna da kowa lafiya, ga walida nan duk abunda kike bu ata ki yi mata mgana za ta taimaka miki, in wani abu ya shige miki duhu ga Inna nan na tabbata za ta iya miki komai sai dai in ya fi arfinta." Sai ya saurara yana kokarin ganin yadda ta kar i mganarsa, kanta na kasa mirmishi ta yi kafin ta jinjina kai lokaci aya tana fa in" In sha Allahu zan kiyaye." Kawai sai ji ta yi yana cigaba fa in" Ina da dalilin da ya sa na za i ki zauna anan gidan, kin kuma san yanayin gida akwai maza wa anda ba muharraman ki, ban amince ki rika fitowa ba mayafi ba, ba na son yawo daga akin nan sai akin inna na amince miki, ki sani nan ba kamar gidan talabijin in da kika saba bayyana surar jikin ki ba ne, nan gidan auran ki ne ankanin abu za ki yi ki zubar da daraja ki, nan gidan mahaifiyata ke zauna sannan tare da mahaifina ruwan ki ne ki kiyaye abin da na fa a miki ko kar ki kiyaye." Abun sai ya bata mamaki wai nan ba gidan Tibin da ta saba bayyana suran jikin ta ba ne, abun sai ya yi mata zafi a cikin ranta sai kawai ta ago tana kallon sa shi kuma sai ya maida hankalinsa wajen cire agogon fatan dake hannunsa daga alamu ya gama maganarsa. "Su ne cikon sharu an naka da ka ce sai bayan aure za ka fa e su? Kai tsaye ya ji muryanta, sai bai tsaya da abunda ya ke yi ba sai da ya cire agogon hannu nsa, sannan ya ora saman center table in da ke gabansa lokaci aya yana fa in" Ba su ba ne, abunda na gaya miki dokar Ubangiji ne, dokikin aure ne da ko wacce macen warai ke kiyayewa." Sai ta kasa mgana sai kawai ta bige da yin mirmishi sanin zai iya aikata abunda ya fi haka, duk da ya sauya amman akwai wasu murada un hallayarsa da har gobe ba su sauya ba. A saman la banta ta ce" Su sauran sharu dan sai yaushe za ka fa a min kenan? Mamakin yadda ta ke son jin sauran sharu an sa ya kama shi, shima sai kawai ya bige da yin mirmishin da ba kasafai yake yin shi ba. Kafin lokaci aya ya ce" Sai lokaci ya yi, suma wa anda ki ka fara ji lokacin fa ar su ne ya yi." Sai ta jinjina kai amman ba ta yi mgana ba, shima dai kamar ya gama magana amman sai bayan aukan tsawon lokaci kowa na sa a abunda ke zuciyarsa falon ya yi tsit