← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 208

Sashe 59

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin farashi mai sau i, ku yi min magana ta wannan lambar* *09069067488* *NA GODE.* *Janafty* *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA* *BONANZA* Kana naka 500. Ta fita zakka 500. Gidanmu 300 Sadaukarwar so 200 Malika malik 200. Zaman gidanmu 200 Ra'ayi ne ko buri? 300. Tsaka mai wuya 500 Mr bello 200. Sillar Hallaci 200. Saifudden 500. Zainazain 300. *Bonanza za ta are a gobe in sha Allahu, in ba ki karanta ba, wannan wata dama ce* Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi kamar haka. *Zumar Matsi Guarantee 3500* *Maganin sanyi komai nacinsa 4k* *Zumar kacha kacha 2500* *Zumar kiba 4k* *Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki* *Dahuwar kaza ta manyan mata 8k* Zaku sameta a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani arin jin da in ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0 *Page 19* *Bayan Wata aya* Bayan wata aya da ya yi dai dai da kimamin wattani biyu da kwanaki da rasuwar Abi, kuma wata aya tsakani da zencen da Hajiya ta yi da Inna Meri sai dai tun bayan lokacin ba su ara ha uwa ba, Inna Meri ba ta koma ba itama Hajiyan ba ta dawo ba saboda sun kara komawa Abuja da aka yi arba'in ita da Mimi suka kwana biyu suka dawo. Gidan can na Abuja ya rage daga Mommy sai Inna Ladidi ita Inna Zainaba bayan arba'in ta koma gida, sai kuma yan aikin Mommy na amana, duk da gidan ya yi rashin megidan amman Dr. Sulaiman da Alhaji Hamza ba su bar shi ya yi kewa ba komai da ake bukata har da wanda ba'a bukata ma suna tana dar da shi. Mommy dai duk wannan bai dame ta ba, ita dai kukanta ta yi rashi rashin da har da har abada ba za ta mai da makwafinsa ba. Sannan ta kuduri niyar cika wasiyyan mijinta shi ya sa zuwan da su Hajiya suka yi ta yi mata mganar Mimi da Mansoor Hajiya ta zayyane mata abunda ya gudana a tattaunawar da suka yi da Inna Meri, Mommy cikin wani yanayi ta ce" Hajiya ni zan je da kaina mu yi mgana, ba zan iya sukuni ba tare da na cika wasiyar Habibi ba, ya rasu da Mimi a bakinsa da kuma udurin nemansa ya nemi gafaransa tunda shi bai samu wannan damar ba, ni ina raye Hajiya in sha Allahu da zaran na fita takaba batun zan fara tunkara in sha Allahu." Hajiya tace"Shike nan Allah ya fitar dake lafiya." Ta amsa mata da Amin suka cigaba da tattaunawa, duk akan mganar Mimin ne wacce duk ta yi sanyi ta koma wata iri, sannan kowa ya gan ta ya san tana da damuwa ga rashin mahaifi ga ciwon da ya jima a zuciyarta. Har su Khadija sun zo addu'an arba'in su kan su, suna ta korafin ganin Mimi ta rame kuma wani abu da kowa bai sani ba tun daga ranar da Aji ya saka mata wannan rigar da ita take kwana da ita take ta shi, in ta na jin kewarsa sai ta rumgume rigar ta yi ta kuka. Ba kowa ba ne zai iya fahimtar Halin da ta ke ciki ba sai ita kanta da ubangijin da ya halliceta. Kwanansu biyar suka dawo gombe lokacin tuni daman Mimi ta koma bakin aikinta ko a can ma ana ta orafin ta sauya sai dai ana tausaya mata sanin ta yi rashin uba musamman ma Rukky da suke tare ta fi kowa sanin Mimi ta rage karsaahi da fara'a ko labarai take karantawa za'a ganta irin so cool haka kamar wata mara lafiya. Sai dai ana yi mata uziri saboda ta yi rashi kuma dole daman sai a hankali. Hajiya ba ta ta a mganar da kowa ba amman Mommy ta yi mgana da Dr Sulaiman shi kuma sai yake ganin abun wani iri har yana cewa"Mommy to tunda Hajiya ta ce ta yi mgana da mahaifiyar shi ta kuma ba ta tabbacin sun yafe ai ina ga shike nan ba lalle sai kin je da kanki ba." Mommy ta ce a lokacin"A'a ai shi yaron aka sa amawa kuma shi Habibi ya jadadda neman gafaransa sannan kuma ya ce ya janye kalamansa kan Mimi in har tana son shi har yanzu da amincewarsa mu aura mata shi." Kai tsaye ya ce"Haba Mommy wannan fa wani abu ne da ya shu e shekaru sama da takwas, ki yale wannan mganar." Sai ta ga kamar bai fahimceta ba, sai da Alhaji Hamza ya zo shima ta yi masa mganar shima dai irin ta Sulaiman in ne ya ce tunda Hajiya ta yi mgana da Inna Meri ta ce komai ya wuce ba kuma amfanin kara nemansu wanda ma ya yi abun nan yau ba shi a duniya kowa sai ya yi hakuri. Da ta yi masa mganar ita Mimi har gobe ta na son yaron tunda har ya amince kafin ya rasu me zai hana a nemi shi yaron a dai dai ta a ji in har har yanzu yana ra'ayin Mimi sai a yi mgana saboda farincikin Mimin. Kai Tsaye Alhaji Hamza ya ce"Wannan maganar banza ce, muke da mace in har ya na sonta har yanzu shi zai neme mu ba mu za mu neme sa ba, mganar Mimi na son shi har yanzu ba magana ba ce tunda ta iya rabuwa da shi a baya a yanzu ma ba wata tsiya ba ce ta samu miji ta yi auranta ta manta da shi lokaci ne kawai bai yi ba.". daga nan sai ta fahimci dukkansu ba su gane in da ta dosa ba, ita kuma wasiyyan mijinta take son tabbatarwa shi ya sa ta kara kiran Hajiya ta fa a mata yadda suka yi da su sai Hajiya ta ce"Rabu da su ba za su gane ba ne, ina son na je har gida na samu Meri da megidan nata amman kafin nan zan aika Binta gidan ta amso lambar wayarta mu yi mgana kafin na je." Da haka su ka rabu da Mommy wacce ta ce ita fa al awari ta yi ma Habibi na cewa In sha Allahu za ta yi kokarin ganin Mimi ta samu abin da take so itama ta yi farinciki kamar kowa nan kuma duniya yaro nan shine cikon farincikin Mimi kuma dalilin shi ne har yau ta kasa ba ma wani namiji dama ciki har da an uwanta Jaheed. Duk kuma bikin da a ke yi Mimi ba ta sani ba har ta su Khadi ba wanda Mommy ta yi mgana da shi Saboda kamar Sulaiman suma suna ganin ba wani soyayyar da ta hana Mimi aure kawai dai kila na ta ra'ayin ne amman su a ganinsu tunda sun rabu tun a baya kowa ya kama gaban shi ina abun cewa mutum na nan yana fama da dakon wahala. Hajiya kuma ta na goyon bayan Murja Saboda ita take zaune da Binta ita ka ai ta san yanayin da yarinyar take ciki so take kafin ta bar duniya ta ga Mimi na cikin farinciki a kuma akin auranta kamar ko wata mace. ******* _Tuesday 04 May, 2022_ Mimi na wajen aiki ta samu wayar Hajiya sai dai in da ta aiken ta ne ya ba ta mamaki, cikin arin mamaki a muryanta da fuskarta ta ce"Hajiya wai gidan su Aji kike nufi na je?. Kai tsaye Hajiya ta ce"Eh don Allah ki je ki kar on min lambar wayar Meri ina son na yi mgana da ita, ga shi ni kuma ban samu zuwa ba." Cikin wani mamakin ta ce" Hajiya zan iya gane gidan kuwa? Kuma in kina son zuwa direba ba sai ya kai ki ba, ai ba sai kin aike ni ba" Da sauri Hajiya ta ce"Kafin na samu lokacin zuwa ina bukatar lambar wayarta ne da gaggawa." Ba ta kawo komai a ranta ba ta amsa ma Hajiya, sai dai ta na tunanin me ya sa Hajiya ta ce sai ita ta je da kanta. Alhalin in tana son zuwa ba wahala ba ne hakan. Tunanin hanyar gidan ma take yi shekarun da ya wa rabonta da gidan nan, ta so ma ta kira Rukky ta rakata sai dai ta na da aiki shi ya sa kawai ta kyaleta ba ta yi mata mgana ba. News in da za ta karanta gobe da safe na wajen Editer in ya gama dubawa zai kai ma Manaja ya duba shima, shi ya sa sai kawai ta yi musu sallama ta wuce da cewar sai gobe da safe. Ta baro gidan Talabijin in cik in zullumi da misalin biyar na yamma a can ta yi yininta yau saboda in ta koma gidan ma sai dai ta yi ta zaman tunani kuma ita kanta ta gaji da tunanin, tana tafe a motar ta har anguwan Arawa a ranta tana tunanin ashe za ta gane anguwan, sai dai anguwan ta samu sauye sauyen gine gine sai ga ta har kofar makaranta mallam ahiru ta kalli makaranta abubuwan da suka faru a baya suna gilma mata sai da ta yi mirmishi a saman lebenta kafin ta furta a fili" Allah Sarki ashe makaranta Mallam ahiru ta nan nan" Makaranta ba kowa tunda ranar alhamis ne ba islamiya daga nan tana tafe a sannu sannu tana kallon gidajen har wajen kofar gidan Wanzamai sai dai abun ya ba ta mamaki Saboda a yadda ta san gidan ba haka ta gan shi ba wannan ya koma na zamani sannan ya samu bangare biyu kuma kowanne da kofar shigarsa, ta jima a cikin mota tana kallon gidajen har gaba ta yi ta kuma dawo baya in da ta tabbatar da kanta nan ne,saboda masallacin dake kallon gidan da ta sani har gobe ya na nan, Sannan akwai wasu gidajen da ba su sauya ba suna nan a yadda ta san su tun da farko. Kofar gidan ba
Chapter 59 · 0% Book details