Sashe 110
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tittle in ma GOMBE UNITED AT IBADAN. Dukkansu ne, su Aji da an Tean in su sanye da kaya masu kalan blue da fari, yawan cin hotunan a filin wasa ne amman akwai wa anda suka yi kamar a haraban dotel da wani kuma da suka auka gaba aya tare da an kwallon kafa na garin Ibadan in da yan wasan da manyan manyan su ga adaya. Haka ta yi ta zooming in hoton Aji sai kuma ta ga da gaskiyan Khadi ba ta ga in da ya yi fara'a ba duk da kowa ka gani cikin hoton farinciki ne, an tashi wasan 2 da 3 ne, kuma su Aji su suka yi nasara sun kar i kanbun girmamawa ko a wajen kar an kambun Aji ne amman bai yi fara'a ba har sanda suka ha a hannu da Couch nasu suka ka aga Kambun sama kowa ya gani bai yi mirmishi ba, Kuma ta san gaskiya ne Aji ba i ne amman har da arin sharrin da su Khadi ke yi masa ba in sa bai yi yawan da su ke fa in shaharansa ba. Har shiga ta yi wajen Comment in da mutane ke ta jinjina suna wasa shi, itama ta ce" Dakyau Aji, ka koya kuma ka iya. AJI IS A GOAL." Ta na shirin fita daga Account in ne sai ga Hibba ta shigo amman sai da ta yi saviing in wasu hotunan, ta kuma kai su ta oye su cikin yan'uwan su. Hibba ta shigo tana fa in" Ba ki yi barci ba? Mimi ta ijiye wayarta a gefen ta lokaci aya tana fa in"A'a ban yi ba, tunda kika ce za ki zo min hira." Hibba ta kariso ta zauna a gefen Mimi tana fa in" Ko kin ji zafi? yau garin ya tsaya cak ba iska kuma ga shi Nepa yau sun hana mu wutar ballantana mu sha iska." Mimi ta ce" Wallahi yau garin ba Iskar nan da za ki ji ta na hurowa, amman nasan ila zuwa anjuma za su kawo wutar in sha Allahu." Sun an ta a hiran zafin garin kafin Mimi ta tambayi Junior Hibba ta ce ya yi barci. Hibba ce ta gyara zama tana fa in" Gobe sammako za mu yi, ga shi ba mu shiga akin Amarya mun gaisa ba." Mimi ta ce" Oh na manta ne, to sai mu shiga da dafe kafin ku tafin." Hibba na dariya ta ce" Da Sassafan? Ai ba su tashi ba sai dai ke tunda ki nan nan sai ki shiga ku gaisa ni kuma sai in na sake dawowa in sha Allahu.". Mimi ta ce Uhm ba ta yi mgana ba. Domin ba lalle ba ne ta shiga ila sai dai in Inna Meri ta matsa sai ta yi ma Walida mgana ta raka ta. Kamar daga Sama kawai Mimi ta ji Hibba na fa in" Wai ni ko Anty Mimi kuna waya da Yayan namu? Kai Tsaye Mimi ta ce" A'a bai kirani ba tun da ya tafi, nima kuma gaskiya ban kira shi ba." Sai Hibba ta ri e baki tama fa in" Kuma shike nan tun da bai kira ki ba, ke ba za ki ki ra shi ba? Mimi ta jinginar da kanta jikin Kujera lokaci aya tana fa in" Wani lokacin ko na kira shi ba ya aukan wayata Hibba shi ya sa ban tusa kaina ba gaskiya." Hibba a ranta ta ce dankari!ai sai ta gyara zama tana kallon Mimi lokaci aya tana fa in" Ni daman tuntuni na lura zaman ku akwai gyara ni kuma na yi al warin zan yi miki magana na baki wasu sharwarin da za su yi miki amfani in sha Allahu." Mimi sai ta natsu ta maida hankalinta kan Hibba lokaci aya tana fa in" Ina sauraran ki." Hibba ta fara da cewa" Duk da nasan kin girmeni kuma kin fini ilmi da sanin komai na matakin rayuwa, amman ni na fiki sanin aure da abubuwan da aure ya unsa, ki yi hakuri in dan har kin ga na yi miki katsalandan." Da sauri Mimi ta ce" Haba! wallahi bakomai ai wanda yace maka gyara mai sonka ne." Jin haka ya sa Hibba ta cigaba da fa in" Maganar gaskiya Mimi na san labarin duk abin da ya faru tsakanin ki da Yaya Mansoor a farko kafin abin da ya faru ya zo ya faru wanda ya yi sanadi yar rushewar wannan danganta da alaqarku a wancan lokacin." Sai ta an dakata tana kallon yadda Mimi ta kar i mganar sai ta ga ta yi shuru tana sauraranta Sai ta cigaba da fa in" Na kuma san wasu abubuwan da su ka faru bayan faruwan haka, na ji wasu da yawa a bakin mijina Mu'azzan tunda an'uwansa ne ya fi kowa sanin shi da yanayin shi. Wallahi Tallahi Allah ne aya Mimi ki sani Yaya Mansoor na sonki a nan duniya ba wata macen da take cikin zuciyarsa koma akwai to a bayan take Mimi." Mimi ta kalle ta cikin mamaki kafin ta ce" Ikon Allah! Me ya sa kika ce haka? Sai Hibba ta gyara zama tana fa in" Ai kowa ya san da haka sannan hujjar a bayyane take , na san a baya kin fi ni sanin shi amman a yanzu da kika da e baki zauna da shi ba, akwai wasu hallayarsa da suka sauya, daman can kin ga yana da zuciya da rashin manta duk wanda ya yi masa ba dai dai ba, amman tun bayan rabuwarku sai zuciyarsa ta ara girman da ta fi ta baya, sannan ya koma wani mutum mai tsananin ri o sosai kuma saboda ke ne ya koma haka, sabo da ke ya daina dariya ya daina Mirmishi ya daina zama cikin mutane sabo da ke ya sauya mafarkin sa na zama soja Sabo da ke ya daina kaunar duk wani mai aikin kaki ciki har da anin sa da Duk duniya ba shi da kamar sa. Wlh sabo da abin da ya faru bai ta a kai ma Mu'azzan ziyara a office in sa ba kuma shi kan shi Mu'azzam ba ya iya nuna kansa da kakin sa na aiki a gaban an'uwansa saboda abin da ya faru yasa ya tsani duk wani aiki da ya shafi ma su saka kaki." Mimi ta zaro ido kafin ta ce" Har da Mu'azzam Hibba ta ce" warai ko hoton shi ya tura masa in dai ya na sanye da Uniform ne in dai ya bu e bisa kuskure to ina baki tabbacin zai goge shi a cikin wayarsa, ko makarantar yan Sanda da ya tafi ba da amincewar Yaya Mansoor ba ne, domin ya ce ba zai je ba Inna ta ce sai ya je, to kuma tun daga lokacin wannan haushin na abin da ya faru ya shafi Mu'azzan saboda yana saka kaki, kuma duk abubuwan da suka faru kin zama sila aciki." Mimu ta yi tagumi kafin ta ce" Ni kuma? ni ma ai ba a son raina komai ya faru ba Hibba, na san kin san komai ba ni da mafita ne ni kaina a lokacin." Hibba ta ce" Na sani abin da ya sa kika ji na ce ke ce sila shi ne na farko tun bayan abin da ya faru har tsawon shekaru goma Yaya Mansoor bai ara ganin wata mace ya ce yana so ba, sai da a ka zo da maganar auran ki sannan ya amince bayan har an gaji da yi masa mganar aure." Mimi da idanuwanta suka ciko da kwalla ta ce" Eh ila saboda Hajiya da Mommy ne, amman a yadda ya ke tafiyar dani ba ya sona ne shi ya sa ya kasa manta abin da ya faru a baya yake kuma tafiyar dani kamar zai rama abinda ya faru in, alhalin kar ya manta Abi ya rasu ya tafi ya bar duniyan nan,ni kuma sabod a na goge wannan tabon a cikin zuciyarsa ya saka na amince da komai na yarda da duka Sharu ansa na aure shi, amman duk da haka ban fita ba na auka yana sona har yanzu amman na fara fahimtar ni ka ai nake tunanin haka shi ba wannan tunanin acikun ranshi." arishe fa a cikin kuka, Hibba ta dafa kafa anta tana fa in" Wlh tallahi yana sonki, duk abunda kika ga yana miki yana yi ne sabod a ba ki yi kokarin wanke masa wannan dattin da e cikin zuciyarsa ba, Ki sani ke ce silar faruwan komai kuma za ki iya zama silan gyaruwan komai. Domin na rantse da Allah in da ace ba ya son ki ba zai ta a amincewa da auran ki ba, in da baya sonki ba zai ta a auran ki ba, ko da kuwa sama da asa za su taru a kansa. Domin da zai yi auran da tuni ya yi kafin ma ki dawo cikin rayuwarsa." Mimi ta yi shuru kafin ta share hawayennta lokaci aya tana fa in" To in har yanzu yana na sona me ya sa bai ta a nuna min ba? Ba shi da aiki sai gaggayamin mganganu yana kiran Babana cikin Izgili." Da sauri Hibba ta ce" Ke ce ba ki auki hanyar da za ki saka ya manta baya ya fuskanci rayuwarsa ta gaba ba, ke ce za ki saka ya daraja sunan mahaifinki, ke ce za ki yi silan da zuciyarsa ta goge abubuwan da suka faru a baya." Cikin mamaki Mimi ta ce" To ta wata hanya zan iya saka shi duk ya manta abunda ya faru? Sai Hibba ta gyara zama suna fuskantar juna da Mimi kafin ta ce" Ba iya auran da kuka yi ne mafita ba Mimi, akwai sauran matakan sai kin bi su sannan za ki kai ga gaci wata rana amman fa kafin nan sai kin fara saka hakuri a kan gaba, komai na rayuwar nan sai mun saka ja uri muke ganin dai dai, sannan shi gaggawa aikin she an ne kuma ki sani Yaya Mansoor ya sauya da yadda kikan san shi yanzu wani mutum ne dabam da za ki fara kokarin jawo shi a jikin ki, domin mu samu sirin da yake oyewa a cikin ransa ya bayyana shi da kanshi." Da Sauri