← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 208

Sashe 54

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi yawa a falon ya sa Hajiya ta kalli Inna Meri lokaci daya tana fa in"Meri ko za ku shiga ciki ku jirani na sallami baki na? Daman ina neman ki kuma ko ke ba ki neme ni ba wannan karon ni zan neme ki." Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce"To bakomai Hajiya, Ina Binta ne? Ina so itama na yi mata gaisuwa su Bintu ma suna son su ma su yi mata gaisuwa." Hajiya ta ce bari ta saka a kaisu akin Binta Baaba Uwani da ke kitchen ta walama Kira ta na zuwa tace ta raka su Inna Meri akin Binta itama ga ta nan zuwa duk da ita Baaba Uwanin ba ta ta a ganin Inna Meri ba tunda lokacin da ta zo gidan tuni Inna Meri ta daina zuwa shi ya sa ba su san juna ba Amman da Hajiya ta ambaci Meri sai da ta so ta auki sauna tunda in dai suna hiira da Hajiya tana yawan ambaton sunan Meri din da kuma irin kyautatawar da ta yi mata lokacin da ta yi aiki a gidanta. Har akin Mimi Baaba Uwani ta raka su, Mimi na kwance saman gadonta da ya sha shimfi ar alfarma da kyakyawan zanin gado na kamfanin FHB CLOTHING Phone no 08034109622 Wtsapp no.08080266674 Zannuwan gadon su masu kyau ne da inganci ka da e kana mora kamar yau ka siye shi. Ta yi kwamciyar ruf da ciki Rukky ne ke zaune a gefen gadon tana laatsa wayarta jefi jefi suna hira da Mimin da ba'a jin muryanta sanda ma Baaba Uwani ta shigo ta ce ba i ne Hajiya ta ce a shigo da su Mimin ba ta iya tashi zaune ba a tunaninta tunda ta ji Hajiya ta ce a shigo da su har cikin akinta sai ta yi tunanin kila bakin na gida ne. Dukkansu a tsaye suka tsaya tunda mai akin ba ta ko tashi ba, Rukky ce ta kallesu lokaci aya tana fa in " Sannun ku, Mimi ki tashi an zo miki gaisuwa." Sai Mimi ta yunkura ta mike tana gyara zaman rigan jikinta wata doguwa mai ruwan hoda kanta ba ankwali tunda daman hula ce ta kuma sa ule kanta, har ga Allah ba ta gane Inna Meri da farko kamar Hajiya ba, ta ji sanda ta yi mata sannu sai ta ce cikin dashewar murya"Ku kariso ku zauna mana, Rukky hayo gadon ki ba su waje" Sai Inna Meri ta ce"Bari mu zauna anan ya isa." Ta fa a tana zama saman cafet din da ke makeken bedroom din Mimi. A cikin ran Inna Meri tana fa in an sauya komai na akin da ba haka ta san shi ba yanzu ko cike yake da kayan alatu na more rayuwa kamar ba akin budurwa ba, to budurwa ce yar gata wacce ta san kanta Dole akinta ya kasance abun kallo haka Bintu ke ta sakawa a cikin ranta nan da nan taji makeken gadon Mimi ya gama tafiya da Imaninta taji kamar ita ce ita, a cikin ranta taji in sha Allahu sai ta yi irin gadon nan itama. Inna Meri ta san Mimi ba ta gane ta ba har suka yi mata gaisuwa kuma har su Bintu ba ta gane ba, ta dai kallesu kamar tana so ta ji ta san fuskarsu amman halin da take ciki ya hana ta tsayawa ta gane su, sai ta koma ta kishigi a kawai tana jin Rukky na fa in"An zo miki gaisuwa kina ta kwanciya kuma? Cikin wani yanayi ta ce"Na amsa su Rukky ki barni kaina ke ciwo." Inna Meri ta bi Mimi da kallo wato a kwalban nan ta zamani ana rage mata ma kyau a fili tafi haka kyau da hasken fata. Inna Meri ganin kawar Mimi na ta kallonsu ga su Hassan sun fara kiriniya ya sa ta ce"Hajiya ta ce mu jira ta gata nan zuwa." Sai Mimi ta muskuta kafin ta ce"Laa bakomai ku jira ta in." Sai ta koma tana kallon yan biyun Bintu da suke neman yin wasa Walida ta yi musu jan ido, sai suka burgeta da ganinsu yan biyu ne kuma ma su kama sosai sannan sun ci gayunsu da kaya iri aya. Rukky ma su take kallo acikin ranta ta ji ta na sha'awar yan biyu, amman wahalansu ne ke ba ma mutane tsoro Walida kuma Bintu ta ke yi ma ra a da cewa"Gaskiya Anty Mimi ta fi kyau a fili." Bintu ta yi dariya kafin ta ce"Gaskiya kam." Dai dai Lokacin da Hassan ya ture Hussaini ya kusa fa uwa sai da Rukky ta mike ta rike shi da Sauri Bintu ta daka ma Hassan tsawa Lokaci daya tana in"Kai ba na son mugunta, in ka turesa ya ji rauni fa? Kawai sai ya saka kuka Inna Meri ta kirasa da hannu tana fa in "Taho nan kyale Mamanka kai da kake da ni ina kai ina kuka Megidana". Take fa a tana masa dariya jikinta ko ya zo ya lafe yana sharen kwallah Hussaini kuma na ganin haka shima sai ya kwace daga rikon Rukky ya dawo ya kwanto a jikin Inna Meri wai shima sai an auke shi. Rukky ta fashe da dariya Mimi na taya ta ganin Inna Meri ta ha a duka ta auka saman jikinta tana fa in "Ya na iya? Ni mai mazaje har guda biyu." Rukky ta koma ta zauna tana fa in "Ina jin ana yawan labarin suna da kishi sai yau na gani, wace ce mamansu hala.? Ta fa a ta na kallon su Bintu sai Walida ta nuna ta, Rukky ta ce"Ma sha Allah Allah ya raya miki su, Sun samu jikin kaka sun yi luf Allah dai ya kara tsawon kwana." Kafin Inna ta samu zarafin Magana Hajiya ta shigo dakin ganin su Inna Meri zaune a kasa ya sa ta kalli Mimi tana fa in"Ba ki gane su ba ne hala Binta? Mimi da kanta ke Sara mata ta dafe shi tana yamutsa fuska kafin ta yi mgana Hajiya ta yi saurin cewa"inna Meri ce fa, tare da Bintu da Walida fa, ni kaina ban ganeta da farko ba sai daga baya." Mimi ta yi kasa e tana kama sunan da Hajiya ta ambata ai sai ga ta ta zaro ido da sauri ta diro daga kan gadon ta tsaya kan kafafunta tana kallon Inna Meri da su Bintu sai a lokacin ta shaida su azun ba ta wani kallesu sosai ba duk da dai suka sauya mata gaskiya, kunya ta kamata Inna Meri na yar dariya ta ce"Shekarun da yawa Hajiya ba lalle ta shaidamu kai tsaye ba." Jikin Mimi sai ya fara rawa sai ta rarumi mayafin Rukky ta saka sai gata gaban Inna Meri ta durkusa tana fa in"Inna Meri ki yi hakuri wlh ban gane ki ba ne" Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce"Bakomai Binta ya arin hakuri kuma? Allah ya jikansa da Rahma.". Mimi ta amsa kanta na kasa tana jin wani irin kunya na kamata. Mamaki ya kama Rukky ta kalli Hajiya tana so ta yi mgana sai ta fasa jin Mimi na fa in"Bintu. lalle Bintu an zama uwa ke ce haka?. Bintu ta saka dariya kafin ta ce" Auran wuri su Inna su ka yi min, amman har gobe Bintu na nan da yan matan cinta." Ba Mimi ba har Hajiya da Rukky sai da su ka yi dariya, Mimi ta ce"Kai Bintu kina nan dai da halin ki" inna ta ce"Wannan ai ba za ta ta a sauyawa ba." Mimi tace"Walida an zama yan mata Eyee, Ina su Yaya Amina da Yaya Halima? Walida tace" Suna gidajen su, da Inna ta ce zata aika musu su zo mu zo nan gaisuwa tare sai kuma ta sha'afa." Mimi ta ka aa kai kafin ta ce"Allah Sarki ki ce don Allah ina gaishe su." Walida ta amsa ma ta da in sha Allahu za ta gaya musu , Yan biyun Bintu Mimi ta kira abun mamaki ba su yi mata kiyuwa ba, Hajiya kuma ta kara ficewa ta ce bari ta sallami bakin Kumo za su tafi. Rukky kuma ta ga Mimi ta manta da ita sai hiran ta ta ke yi, amman tun azu da ta zo kwance ta yi mata tana mgana dakyar ba ta kawo komai ba ta auka kila cikin yan'uwansu ne, ganin haka ya sa ta yi shirin tafiya tace Mimi ta ba ta mayafinta za ta wuce gida. Sai ta ba ta nata ta auko wani karamin hijabinta iya gwiwa ta saka ta ce ma su Inna Meri bari ta raka kawarta, su ma su ka yi sallama da Rukky har 500 500 hundred ta ba ma su Hassan su ka kar a suna fa in sun gode ko domin hararan da suke sha a wajen uwar ta su. Sai da su ka fito haraban gidan sannan Rukky ta kalli Mimi kafin ta ce"Wai su waye wa anan da kina ganinsu kika mike tsaye? Ko an'uwan ku ne? Mimi ta yi mirmishi kafin ta ce" Surukata ne da annen saurayina." Rukky ta saki baki tana kallonta kafin can ta ce"U Mean maman Aji ne da annensa? Mimi ta lumshe ido jin sunan rabin ranta da aka kira kafin ta bu e su akan na Rukky sannan ta jinjina mata kai alamun hakane. Rukky ta ri e baki ta ce"Ikon Allah dalilin mutuwa yau sai ga shi sun zo, ko da yake ai kin ce aninsa in nan ya yi miki gaisuwa da sauran abokan su Usman to shi ba in masifaffan Ajin ya kira ki ya yi miki gaisuwan kuwa? na ga mahaifiyarsa da annensa babu ruwansu amman shi kam wlh ba shi da mutumci ai ko Allah ma gafurin Rahimunun ballantana shi an Adam ba kowa ba." Mimi ta rausayar da kai kafin ta juya tana fa in" Sai anjuma Rukky ki gaida Mama." Rukky ta ta e baki tana fa in "Uhm Mimi Allah ya yaye miki wannan makahon son da kike yi ma wannan gayen." Mimi na jin ta amman ba ta tsaya ba ta yi shigewarta cikin gida, itama Rukky ta juya ta fice daga gidan ta na tunanin ita ba ta ga abulin da zai saka
Chapter 54 · 0% Book details