← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 208

Sashe 143

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya ara fa in" Ki yi ha uri inna don Allah ki yafe min." Sai a lokacin ta juyo tana kallon shi kafin ta ce" Ha urin me kake ba ni? Ka min wani laifi ne? Ba ka min komai ba ta shi ka yi tafiyarka sabogiginka Allah ya yi albarka." Ta fa a lokaci aya tana kokarin aukan Junoir da ke kwance saman jikinta, Da sauri Baba Danjuma ya ce"Ki yi ha uri Meri ki tsaya ki saurare shi, tunda har ya gane kuskuren shi ya baki ha uri domin Allah ki daina fushi da shi" Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba, Baban Inna na ta ban hakuri Baba anjuma na tayasa sai kawai ta ce"Ni fa ban ri e shi ba. Har ga Allah na yafe masa Saboda acin raina zai iya jefasa cikin bala'i, hannuna ne na ce na cire a kan rayuwarsa ya je ya yi duk rayuwar da ta yi masa dai dai." Baba anjuma ya ce"To baki hakuran ba kenan? " Wlh na yafe masa tuntuni a cikin raina." "To in har kin yafe masa ina nema masa alfarman ki shirya ki je gidan Hajiya ki yi masa bikon matarsa." Dariyar nisha i inna ta saka kafin ta ce"Au an zo wajen kenan? Tana gama fa in haka ta mike ta sunkunci Junior lokaci aya tana fa in" Ai ya ce ba ya sonta shi ya sa ya ce ta tafi gidansu, in ya ga dama ya sake ta duk ban damu ba ni abu aya ya dame ni yadda ya atamin suna ya sakani jin Kunyar yarinyar nan da Iyayenta, Amman ni ban damu da duk abin da ya aikata ba wannan rayuwarsa ce abin da ya fi masa daidai shi zai yi." "Ki yi hakuri Inna." Abunda Kawai Mansoor ya ce kenan, Baba Danjuma a ka bar shi da cewa" ba ki dai yafen ba kenan? Inna Meri ta ce"Na yafe masa, amman wallahi tallahi kafata ba za ta taka gidan su Binta da sunan yi masa biko ba. Shi ne ke auran nan in har ya na son natarsa yana da Kafa kuma ya san in da zai sameta amman in ni yake Jira to ya daina jirana na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba, ba in da zan je" Tana gama fa in haka ta shige cikin uwar aka in da Walida ke kwance ta kasa kunne tana ganin Inna ta shigo sai ta yi barcin karya. A ranta ko da i ta ji wlh kada Inna ta je, shi da ya aikata barnansa ya je ya gyara da kansa. Ganin Inna ta shige ya sa Baba anjuma ya kallesa kafin ya ce"Tunda ta na ce to ba za ta je ba, ka shirya ka je ka yi bikon matarka ka ji ko? Cikin jinjina kai ya ce"In sha Allahu Baba., daman ai tsakanina da Mimi ba saki, amman za ta iya yin yaji wani lokacin in bukatar hakan ya ta so." Kai tsayen shi ya fa i haka, kuma har acikin zuciyansa haka yake nufi. Sai Baba Danjuma ya ara fa in" Ko kuma in za ka je ka min mgana sai mu tafi tare" Da sauri yac e"A'a Baba kada ka damu ba sai ka je ba." "Ka tabbata? Sai ya gya a masa kai, shi kuma sai ya dafa kaffa ansa kafin ya ce"Sannan ka yi hakuri akan abubuwan da suka faru, kasan halin magajiya ita ta saka rigimar dawowar Matar Saddiqu akin Fatima, yanzu in za ta dawo a ina za ka ijiye ta? Mirmishi ya yi kafin ya ce"Wajen zaman ta ba matsala ba ne Baba, bakomai na gode warai Allah ya ara girma." Baba Danjuma ya amsa da Amin bai da e ba ya ce zai tafi 30k ya ba ma Baba ya ce Auwalu zai kawo kayan abinci na wannan Watan Baba Danjuma nata godiya har ya tafi Inna Meri ba ta fito ba, ga shi ya na jin yunwa amman kuma yasan yau Inna ba za ta basa abincin ta ba. Da ya fito ya tsaya jim ya na kallon ofar akin Mimi, na wani lokaci sannan ya ka a kai ya fice, dole zai auko mataki daga Saddiqun har matarsa ba su isa su raina masa uwa ba. Bayan fitan sa ma Baba anjuma da kansa ya tsaya kofar akin ya yi ma Maaeesha mganar ta kashe wannan Sautin ba ta da yadda za ta yi dole ta kashe, Saddiqun baya nan ya koma Lagos daga nan ya shiga akin Magajiya ya ja mata kunne ya ce ta yi mata Surukarsa mgana wlh baya son di an albarka ta daina takura ma Meri da daddare da sautin banza in ba haka ba wlh za ta bar masa gida. Magajiya ta buga shewa ta ce saboda Meri zai kori matar ansa? To lalle kuwa sai dai itama Merin ta bar gidan. Shi dai bai biye mata ba ya fice zuwa akin sa ya barta tana Kumfar baki ko kunyar Mariya dake akin ba ta ji. Mansoor Aji kuwa yunwa ta saka sai da ya biya ya siya nama da lemu sannan ya koma gidansa, rabonsa da abinci tun eea in da ya sha da safe. Sai da ya yi wanka sannan ya zauna ya ci ya ora da lemu. Tunaninsa yadda zai tunkari Mimi ne, Dama tuni ya ke so kiran ta amman ba shi da dalili amma tunda yanzu Baba ya yi mgana ya samu abun fakewa. Yana kwance daga shi sai hajeren wando ba riga ya auki wayarsa ya lalu o Lambar Mimi da ya yi mata saving da LIFE PARTNER , Sunan ba iya rubuce ba ne har a gaske ma itace cikon rayuwarsa, ba wanda yasan ma sunan da ya saka mata wayarsa kenan hatta ko da ita kanta. Yana kiranta sau aya ya dauka da rawan jiki za ta auka sai ga shi sai da ya yi mata Missed call biyar ba ta auka ba, kuma shi ya san ba ta da abi'an barcin wuri yana da tabbacin Idanuwanta biyu. Nan da nan wata zuciyar ta harzu a shi, kamar shi Mimi za ta yi ma wannan wula ancin? Sai kawai ya shareta bai ara kira ba amman kuma ya kasa sukuni har ya kwanta amman ya kasa barci yana ta juye Juye. Sai kawai ya sake aukan wayan ya ara kiranta har sau uku ba ta auka ba. Saboda acin rai har wani duhu duhu ya fara gani kawai sai ya shiga wajen sa o ya rubuta mata haka. "Ni ne za ki wula anta Mimi? ni ko? To ya yi miki kyau." Ya gwada ne domin ya samu tabbacin tana ganin nashi ko ba ta gani ba? Hasaahen shi ya zama gaskiya domin ba da ewa, sai ga martanin sa on ta. "Maganar saki ne? Kada ka damu za ka iya turomin ta text nassages, ko kuma ka aiko min da takardata gidan Hajiya ko wajen Daddy." Idanuwansa har rawa suke yi da ya karanta akon Mimi, bai san lokacin da ya yi mirmishin takaici ba, lalle ma wannan yarinyar da shi za ta yi wasaa ko? "Ina jiran sammaci ne." Abin da ya aika mata da shi kenan, amman ha wajen bayan awa aya waya na hannunsa ya na gadi amman ba ta dawo masa da amsa ba. "Kin yi shuru? Ko kin fara karaya ne? Haka ya sake turamata nan ma shuru. Sai ya koma ya sake kiranta kawai sai ya ji ta danna masa lamba busy. Wayar ya bi da kallo a fili ya furta" Kan uba can!" Haka ya fa a, har ya na wani hararan wayarsa, wai shi ne Mimi ta kashe ma waya? Wasa wasa kasa sukuni ya yi yana kwance yana ta juye Juye ya kasa barci har cikin dare sai da ya tashi ya kara kiram Mimi ba ta auka ba har asuba ma sai da ya kara kiranta ta kuma ara danna masa busy Ransa ya kai kololuwar aci. Yana kiranta yana Hargagi shi ka "Mimi ki aga kiran kafin ranki ya aci." Amman ba ta aga ba Daga karshe ma wayarta a kashe ya ji. Haka nan ya shirya ya tafi camp suna da morning traning, amman kowa ya gansa yasan ran maza a ace ne daga can gida ya wuce ya gaida Inna Meri amman tunda ta ce lafiya lau ba ta ara masa mgana ba haka ya gama zamansa Shuru kuma ga shi ya na jin yunwa amman Inna Meri ba ta bashi Koko da Kosan da ta yi ba, har ya gaji ya yi mgana kaii tsaye Inna Meri ta ce ya kare kuma yana ganin shi ga shi a fulas tunda a gabansa ta juye. Daga nan yasan saamun Kwanciyar hankalinsa da kuma ganin farin cikin Inna shi ne ya je ya samu Mimi su yi mgana. Yana durkushe a gaban ta ya ce"Inna yau zan je na samu Mimi mu yi mgana za ta dawo in sha Allahu." In dutse na mgana to Inna Meri ta yi mgana haka ya kwashi sanyin jikinsa ya fice. A tsakar gida ya ga Maeesha kazama ce ta fito daga aki ta na tsintar da yawu nan kofar aki, kusan amai ya tashi yi kallo aya ya yi mata ya fice ganinta ma ya sa ya tuna da Maganar da ya ce zai yi ma Auwalu. Yana hanyar komawa gida ya kira shi ya gayamsa cewa ya ja ma aninsa kunni ya tsawatar ma matarsa domin Inna Meri ba sa'arta ba ne, in kuma bai iya ja mata ba to shi zai yi abin da rayuwaka za su aci, Auwalu ya ba shi hakuri ya ce zai yi mgana da Saddiqun. Shi daman yasan wannan zaman ai ba za'a wanye lafiya ba. A daran ya so zuwa gidan Hajiya da fakewar ba zuwan kanshi ba ne saboda Inna ne da Baba Ahalin zuwan kanshi ne, domin har a daran ya kirata a kashe, Bai samu zuwa ba saboda ya samu wayar Coach Team in kwallon kafa na Anguwan Jeka da Fari suna bukatar a shirya musu wasan sada zumunci da Team in Tudun wada, kuma a matsayin sa na Captain na Gombe united gaba aya yana kula da sauran
Chapter 143 · 0% Book details