Sashe 39
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
subuce wajen fa in "Na bar miki daga yau kin zama Mimin Aji." Cikin jin da ta ce" Thank you kai ma daga yau ka zama Ajin Mimi." Yadda take dariya sai ya ga fuskarta cikin fara'a da annushuwa mai kyau ne sannan ta fi kyau in tana mirmishi ko dariya. Al'amarin ala ar Mimi da Aji wani al'amari ne na Ubangiji shi dai kawai ya samu kansa da jin yarinyar a cikin rjinsa sannan saboda ita baya fashin zuwa ya taho da Inna Meri alhalin a baya ba ko da yaushe ya ke zuwa su koma gida tare ba, saboda haka ya ya ye zuwa islamiya ko da yaushe yana hanyar GRA in an yi mgana sai ya ce ya je tahowa da Inna Meri ne. ita kanta Mimi za ta iya cewa Allah ne ya ha zukatan su waje aya tunda ga ranar Hajiya har gajiya take yi da labarin Ajin Mimi. Tun Hajiya na aukan abun shirme har dai ranar ta ce"Wai waye ne wannan Ajin ni Binta? Mimi ta ce"Laa wai hajiya ba ki san shi ba? an Inna Meri ne fa ? me dafa miki abinci." Hajiya ta ce"Au shi ne wani Aji? To ai bari Merin ta zo na ji waye wani Aji acikin a'yanta ya na nemen ya wacemin gwamnatina wajen Binta ba ta da magana sai ta shi." Haka ko akayi inna Meri na zuwa bayan sun gaisa Hajiya ta ce"Meri wai ni cikin anki waye wani Aji da Binta ke yawan mganan shi, na ce ina ta san shi ta ce ni bansan shi ba ai yana zuwa gidan nan." Inna Meri na dariya ta ce" Mansoor ne Hajiya Baban Inna, bai taba shigowa ya gaishe ki ba ne shi ya sa ba ki san shi ba." Hajiya na yar dariya ta ce"To ni dai na ce waye kuma wani Aji? Sai ace masa ya shigo mu gaisa ya daina taremin yar jikata a waje bai zo ciki ya fara ganina ba." A lokacin ita Hajiya a wasa take yin maganarta Inna Meri na taya ta da dariya ta ce" Zan gaya masa Hajiya, ai sunan Aji abokansa ne ke kiran shi da shi.". Hajiya tace"Sunan banza ba, ga sunan shi mai da i." Mimi na zaune a gefe ta cee"Hajiya Ajin ya fi da wallahi." Hajiya tac e"To daman ke me kika sani? Har yanzu yarinya ce ke Binta.". Inna Meri na ta dariya Mimi ta tura baki tana in"Ni ba yarinya ba ce." Hajiya ta kalleta tana dariya yarinyar da ko nono ba ta da shi sai kirgan dangi da ta fara har kuma yau ba ta fara Jinin al'ada ba, Murja har damuwa ta fara yi Hajiya ta ce ta kwantar da hankalinta wasu matan ba sa farawa sai sun kai sha bakwai kila Binta ta na daga cikin su ne. A ranar Mansoor bai zo ba, ya je filin ball sun je buga wasa da yan anguwan Tudun wada, Mimi ta ri a le e ba ta ganshi ba Inna Meri na mata dariya ta ce"Baban Inna ba zai zo ba tunda kika ga har yanzu bai zo ba." Mimi ta fara fushi har ta na cewa in yazo gobe ba za ta yi masa mgana ba tunda ya ce yau zai zo za ta ba sa wani labari mai da Hajiya aka bari da lallashi abun ma sai ya koma ba ma Hajiya mamaki ko abinci ta i ci a daran wai ta yi fushi da Aji. Da safe da Inna Meri tazo hajiya ta ce"Meri maza ki aika Yaron nan naki yazo ya sakar min jika da warin da ya yi mata tun jiya nan da kika barta take fushi saboda bai zoaa tun jiya ba ta ci abinci ba.". Inna Meri ta rike baki tana fa in"Ikon Allah. Sai da Inna Meri ta lallasheta da cewa zai zo sannan Mimi taci abinci ta yi wanka da Hajiya ta so ta saka a kaita gidan Daddy Mimi tace ba inda za ta je sai ta kyaleta. Hajiya ta yi tagumi kafin ta ce"Ni dai yau ina ganin ikon Allah ni Binta." Inna Meri na taya ta da dariya saboda su a tunaninsu yarinta ke damun Mimi a lokacin ba su ta a tunanin Ubangiji ya oye wani abu a tsakanin su ba. Kamar ko Mansoor ya sani da Yamma sai ga shi tare suka zo da Mu'azzam saboda ba makarantan islamiya daga filin wallo suke yau Mu'azzam ne ya buga wallo shi bai yi ra'ayi ba. Daman ta yini le en waje tana ganinsu ta fita da gudu kamar ta kifa shi dai Aji sai dai ya ganta a gabansu tana haki da sauri yace"Bi a sannu kar ki fa i ki ji ma kanki rauni." Sai kawai ta harare shi da fararen idanuwanta Dariya ma ta bashi da sauri ya ce"Me na yi ni kuma yau" Cikin yarinyarta ta ce"Ba kai ne ba kai ne jiya ka ce za ka zo ba ka zo ba, sai jiran ka nake ba" Ta na fa a sai hawaye sai ya ji ya damu da sauri ya durkusa a gabanta yana fa in"Afuwan Mimin Aji na je wasa ne jiyan nan." Tana sharan wallah ta ce"Jiya ma ban ci abinci ba, ko Hajiya ma yau ban yi ma mgana ba saboda ina fushi da kai." Mu'azzam na tsaye na kallon wani abu na faruwa kamar a shirin film sai gani ya yi yayansa ya kama kunni yana fa in "I am so sorry Mimi Mimin Ajii.." "Kin ha ura? Sai ta gya a kanta tana mirmishi kafin ta ce"Yau ka zo mu je Hajiya ta ganka sai da ta tambayi Inna Meri wai ba ta san ka ba." Dariyan maganarta ya yi sosai ya na shirin mikewa ya ce"Haka za'ayi ranki ya da e tunda Hajiya ta ce ba ta sanni ba, ya zama wajibi ta ganni yau tunda haka Mimi take so." "Barkan mu da Yamma Anty Mami." Mu'azzam ya fa a bayan ya duka shima har asa, sai ta fashe da dariya tana rufe baki kafin ta ce"Laa ka girmeni kana ce min Anty? Yana dariya ya ce"Ai abun ba daga nan take ba, girman ne Allah ya baki kar ki damu da ananun shekarun ki." Ya fa a yana kallon an uwansa dake masa kallon mamaki. Mimi kuma ta samu abun yi sai cewa take yi ya maimaita sunan da ya kirata shi kuma ya na ta maimaita Anty Mami, ta saka dariya ta rufe bakinta da tafukan hannunta kafin Ta ce"Aji abokin ka ne? Kai tsaye ya ce" anina ne Mu'azzam." Da sauri ta ce"Laa shima yaron Inna Meri ne?. Sai ya jinjina mata kai sai ta fara tafa hannu tana fa in"Kuma ba ku kama, kai ba i shi kuma fari, kai dogo shi kuma gajere." Yadda take lissafin ne tana kwantance ne ya sa dole suka yi dariya gaba ayan su. A ranar dai dole Mimi ta yi musu Jagora suka Shiga har falon Hajiya suka iske Inna Meri na yi ma Hajiya kitso tunda ita kan tsefe mata ta yi mata wani in ya tsufa. Sai Ranar Hajiya ta ga Ajin Mimi, Mu'azzam daman ya sha shigowa wani lokacin ma acan shi kan rako inna Merin da safe kuma ya shiga har cikin falon ya gaida Hajiya. Hajiya ta kalli Mansoor dake duke gabanta bayan sun gaisa ta kuma kalli jikarta da Mirmishin ya ki barin fuskarta Kawai sai ta ka a kai kafin ta ce"Ai shike nan Aji ko? To ni dai wani warin ka yi ma jika ta, yau fushinka har shafa ta ya yi aka i yi min mgana." Kansa na kasa bai yi mgana ba Hajiya ta cigaba da fa in "Binta kullum L labarinta na Aji ne, to ni dai na lura jikata na yi da kai Allah ya ha a jininku gata nan a kular min da ita Amana domin ina ji da ita ahto, in kuma kana sonta ne sai ka fara biyana kudin toshi har da kudin zence." Mansoor a lokacin da sauri ya kalli Hajiya. So? So kuma? Ita kuma Mimi fuska ta rufe ta kalli Hajiya tana yar dariya Hajiya ta kalli Meri tana yar dariya ta ce"To ke fa Meri kin samu shagwa iyar Suruka Allah ya tayaki riko." Abun da ya fallasa abin da ke zuciyar Mimi shi ne sai ta tashi da gudu ta shige akin Hajiya wai ta na jin kunya..Hajiya kuma tun tana aukan abun wasa har dai ta fahimci jikarta da gaske take yi. Kai Tsaye ta kalli Aji kafin ta ce"Kai Mansoor to jikata da gaske take yi, maza ka fara kawo ku in toshi in kana son na shige maka gaba lokacin auran" Mu'azzam da Inna Meri na ta dariya shi kuma gogan sai mirmishi yake yi abun mamaki. Ba su jima ba suka yi ma Hajiya sallama suka tafi, Mimi kuma ta ki fitowa alamun dai ta na jin kunya Hajiya na dariya tace "Meri ina jin dai Binta kunyar surukanta ya hana ta fitowa." Inna Meri tace"Bari naje na lallasota." arshe Inna Meri aka bari da lallaso Mimi sannan ta fito, Shike nan Hajiya ta samu tsokanar Mimi da Binta surukar Meri, Meri na fa in bakomai itama ai tayi dacen Suruka. Wani abu ne da ake kira magana daga arami sai ya girmama a zuciyar Mimi da gaske tana son Aji shima acikin zuciyarsa Mimi ce aciki ba tare da tunanin me gobe za ta haifar ba suka kamu da tsananin kaunar juna da ananun shekarun su, Saboda Aji Mimi ta buga tsalle lokacin da Abi ya zo da kansa ya dauketa domin ta koma Abuja ta shiga matakin Sakandiri ta saka kuka da rigiman wajen Hajiya za ta zauna, ba za ta iya tafiya ta bar Ajinta a nan ba. Hajiya kuma ganin yadda Mimi ke kuka ta ce ba inda za ta je ya barta anan Hamza ya saka ta a makarantan da ya'yansa ke zuwa. Bai so hakan ba amman Hajiya ta ce in har ya matsa sai ya tafi da Mimi za ta ce ba ta bashi har Abada kalaman Hajiya su saka sanya a ka bar mata Mimi a hannunta Alhaji Hamza ya saka