← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 208

Sashe 194

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rike hannunta ta fito daidai lokacin da ta ce"Amman ai da kunya tun da kowa ya san abin da muka yi a ka samu cikin ko? Aji ya kalli Mimi ganin har ta na wani ata fuska. Dariya ta kamashi ya kama yi tun da Mimi take da Aji a sanin da ta yi masa a baya da yanzu ba ta ta a ganin shi yana dariya haka ba. "Shekaran ki nawa wai? Ai daman kowa ya san sai da muka ha u a ka samar da saduwa sannan kika samu ciki, tunda ba a ruwa za ki sha ba." Haka yake fa a yana mata dariya, kamar za ta yi kuka ta dake shi a kirji shi kuma ya na riketa yana dariya dai dai lokacin sai ga mai motar tare da Auwalu da Gaje a ciki ita ce za ta je. Sai matar Auwalun da Maeesha da Mariya, da Jummai da Zuwaira kowa cikin shirinta, Auwalu ne ya sauko suka gaisa yana gaya masa yaron mai motar ne zai kai su kanon shi yana gida baya jin da i, Aji ya kalli direban kafin ya ce"Ka tabbata ya iya mota? matata ciki gare ta ban shirya aukan wannan kaddaran ba yanzu." Ai Mmi na jin haka ta ja jikinta zuwa wajen su Yaya zuwaira tana gaishesu domin in ta cigaba da tsayawa saita ji abin da zai saka ta ba za ta ara kallon Yaya Auwaln ba. Tare suka shiga gidan suka iske su Yaya Amina tun azu suna nan suna jiran su, nan a ka gaggaisa sannan sai ga su Auwalun sun shigo gidan tare da Mansoor suka gaida Inna sun shirya daman motan kawai suke jira, Yaya Halima ce ta kalli Aji kafin ta ce"Na ji ana zencen kwana biyu na ce mu fa hu u za mu yi." Kai tsaye ya ce"A'a kwana biyu za ku yi gaskiya." Ha e rai ya yi kada ma ta kara mgana, Ita daman zolayanshi take yi, Bintu ce ta ce a hankali ita sati mijinta ya barta ta yi. Hararanta Mansoor ya yi kafin ya ce" Duk wacce ta ga kwana biyu ya yi mata ka an za ta iya arawa amman litini da safe mota za ta koma wanda ya ga zai dawo shike nan. Haka ya fa a lokaci aya yana ficewa Bintu ta tura baki ta ce" An ya in Anty Mimi ta haihu za mu je mu yi sati muna suna kuwa? Yaya Amina ta ce" Kina da ko ari, in ma ya bari an yi sunan kenan tsab zai ce ba taron suna in dai Baban Inna ne." Mimi na gefe ta na jin su tana yar dariya, ba ta ce komai ba, Yaya Halima ta ce"Duk fa wannan muzurin saboda matarsa ne, kada mu kara kwana a barshi a gauro." Gaba aya suka saka dariya Bintu har suna tafawa da Yaya Amina. Mimi ta harare ta kafin ta ce" Har da ke ko? Zan gaya masa." Bintu ta tsuke baki tana fa in" Ni ban ce komai ba, ba ruwana." Suna cikin mganan ne Auwalu ya leko ya ce su fito su Yaya Zuwaira daman suna tsakar gida Maeesha ne kawai tare da su, Mariya da Walida yan zumu i suna kofar gida wajen mota su Auwalu suka fiffita da kayan a ka saka a booth, sannan a ka tsara tafiyan Aji shi ya saka Mimi a gaban mota ita da Mariya tunda ba ta da jiki, Yaya Jummai ta ka a baki tana fa in"To ai da baya ta dawo, ko ka saka Bintu madadin Mariya." Kai tsaye ya ce"A'a Bintu za ta matse ta, kuma ni ina so ku kula da ita ne, juna biyu gare ta fa" Kunya kamar Mimi ta nutse kanta ta sunkuyar Yaya Auwalu ne a ka bari da fa in" warai kuwa, ku kula da matar yalla ai dakyau." Gaje ce ta ce" Kada ka damu Baban inna zamu kular maka da matarka da abin da ke cikinta in sha Allahu." Suna ta masa dariya shi kuma ya ha e rai, Mimi ko kunya ta rufe ta wai har ya na ma direba warning cewa kada ya yi gudu ya bi a sannu matarsa juna biyu gare ta har yana cewa"Ita ce komai nawa, ka bi su a hankali don Allah ban da gudu.". Direba na dariya yace"In sha Allahu Yalla ai " Inna Meri ma har kofar gida ta rakosu, tana musu fatan Allah ya tsare, baya mutum hu u Gaje da Jummai da Zuwaira, sai Maeesha. Kujeran tsakiya kuma Yaya Amina da Yaya Halima sai Bintu, sai Walida da a ka gyara ma inji sauran kujeran za'a biya Tudun wada a auki mutum aya daga gidansu Hibba. Suna aga musu hannu tare da fatan su isa lafiya, Tudun suka biya su ka auko Zaliha iyar anwar Maman Hibba ne sai bayan sun dau hanyar kano Nafisan Nasir ta kira Mimi ta ce ba ta san sun shirya tafiya ba, Nasir ya barta da ta zo. Sai mimin ta bata hakurin itama ta sha'afa ne ba ta mata magana ba, amman wai Nasir in ya yi ma Aji mgana shi kuma wannan tuni ya manta ma. Direban ya ji mganar Oga Aji bai yi gudu ba amman sun isa wajajen uku ne na rana. Shi kan shi Aji ya yi mamakin saurin su haka yace ma Mimi da suka yi waya. Murna wajen Hibba da Mu'azzam ba'a mgana, suka rasa ina za su saka su saboda murna sun iske wasu daga cikin anen Hibba da yayenta sun riga su zuwa tun jiya suke. A ka rasa ina za'a saka su kawo wannan miko wannan Sun rasa bakin godiya ga zuwa ga abun alheri Mu'azzam sai da ya yi wallah domin Yayan nasa ya gana mishi komai bayan kudin da ya tura masa ya biya ku in mota sannan ga awaniyar kayan suna da ku i, ya kira shi zai masa godiya ya kashe wayarsa. Ba su zauna ba da yamma a ka fara aikin suna raguna biyu a ka yanka ma Maryama da safiyar suna. Sannan sun dafa shinkafa sun yi alale da Zo o an kuma soya kayan ciki bayan haka kuma ga nama ya siya anyen an yi girki da shi, a ranar Mimi ba ta samu fita ba sai washegari ranar lahadi Bintu da Walida tare da mariya suka rakata gidan Dr ta fara zuwa baya nan ma yana asibiti sai dai Jawahir nan suka yi sallar la'asar sannan suka wuce soron inki, Inna Zainaba sai da ta mata tsiyan ta auka za ta kwana ne amman sai ta ce washegari za su koma gaba aya, suna can har dare sannan a ka saka direba ya dawo da su gida. A ranar daman su Yaya Amina suka soya Nama a ka di ar musu na su a daran. Na Inna daban haka na Baba sai sauran kuma a ka ha a su gaba aya. Amman na Baban inna roba guda cike da nama in ji an'uwansa, misalin sha biyun rana direban yazo amman sai da suka yi azahar suka ci abinci shima yaci sannan suka auki hanya nan suka bar an'uwan Hibba su sai jibi za su koma anman anwar mamanta na nan sai ta yi arba'in. Sai mangariba suka iso gida, gidan Inna su ka yada zango, nan suka raba naman kowa ya auka na shi, sannan Mu'azzam ya ba su kwalin omo da sabulu yace su raba gaba aya. An raba amman Mimi ba ta amsa ba, Naman ma cewa ta yi su ha a ma Inna sabulun kuma ta ba ma Jummai omon kuma ta ba ma Yaya Zuwaira su sun fita bukata. Yaji jegon ma an ba su wanda an'uwanta su ka mata sun raba gaba aya. Zuwa bayan isha'i kowa ya yi gidanshi inna ta di ar ma Magajiya naman da Yaji ta ba Mariya ta kai mata, Gaje ma har na Harira an iba mata ita daman Inna an san rabar da shi za ta yi kila ma ko a bakinta sai an yi da gaske za ta ana. Mimi dai nan ta jira Aji ya zo ya aukota da daddare suka tafi gidansu, daman a daddafe ya yi kwana biyun nan. Washegari ma ba ta samu zuwa wajen aiki ba sai ranar laraba ta koma.Miyan ma da ta yi masa ko sau aya bai yi amfani da ita ba. Ya dai ci cake da samosa, itama ya ce domin ya na so ne yasa ya soya ya ci, da tace ina ya ke cin abinci ya ce gidan Inna da ta gama za ta kira shi ya je ya cika cikinsa, ina zai iya wani Dafa shinkafa bayan ta gama sangarta shi.. In da Allah ya so ta da rahama ba ta yi mugun laulayin da zai hana ta aikace aikacen da kuma biya ma mijinta bukata ba ko amai ba sosai take yi ba bar ta dai da cin goro sai kayan kwalama suma ba kasafai ba. Cikin fari ne amman Alhandulillah ta same shi da sauki fiye da tunaninta, fatan ta Allah yasa yadda ta samu laulayi da sauki ta samu haihuwan ma cikin sau ****** *BAYAN WATTANI BIYU..* Har Hibba ta yi arba'in ta zo gombe ta yi sati ta kawo ma Inna takwaranta wacce suke kira Ammi. Mu'azzam ya zo ya auke ta suka koma gida, cikin Mimi kuma watannin shi shida ne, har ta fara zuwa awo a wani asibitin ku i a cikin gari tana kuma cigaba da zuwa aikinta. Cikin ya bi jikinta tunda tana da tsawo sai da ya saka ta bu e daga kasanta saman ta kuma mamanta sun yi manya kumatunta ya kumbura sannan hancinta ya ara girma tuni dai halittar ya sauya. Hajiya ce ta gaya mata cikin jikinta ya bi shi ya sa ba'a ganin girmansa, shi kuma Aji ya ce ta zauna a haka ta fi masa kyau a koda yaushe ya kalleta ya na jin farincikin yau ita ce ke auke da cikinsa wannan ma abun alfahari ne. Zaman su suke yi lafiya cike da kauna sai an abun da ba'a rasa ba. Tun da daman shi zamantakewa zo mu zauna ne zo mu sa a ne, sai dai suna
Chapter 194 · 0% Book details