Sashe 32
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya zage ni ba za ka ji da i ba, duk duniya ba wanda ya isa ya ce Mu'azzamu ba anin ka ba ne ya fa a ne domin ya tunzara ka." Suna tafe ta na mgana kuma duk Nasiha take yi masa akan hakuri da kuma daina bakar zuciyan nan nasa nuna masa ta ke yi mai hakuri shi ke da ribar duniya kuma ya ke da ribar lahira. Suna shawo kwanar layin su suka ci karo da dandalin yara da matasa sun taso daga makarantar islamiyan Mallam ahiru, Mansoor ya hango Mu'azzam tare da su Nasir suna baya suna tafiya suna magana yana jin muryansu a sama gaddama ta sarke su kuma Mansoor na da tabbacin gardaman wallo ce. Su binta kuma suna gaba tare da su Zuwaira amman Bintu na kamkame da hannun Walida da ita ce karama a kaf gidan Wanzamai ita da Mariya. Bintu ta fara hango inna Meri sai ta saki hannun Walida ta nufi innar da gudu ta fa a jikinta har garin gudu tana watsa ma Mansoor kasa a kafarsa dake cikin bakin takalminsa. Ransa ya aci tsawa ya da ka mata yana fa in"Ke zan ba ki wahala, ba ki da natsuwa ko? Sai a lokacin ta ganshi da Sauri ta makale bayan Inna ta na tura baki, dukawa ya yi ya na kakkabe kafarsa itama Walida ta zo da gudu ita a lokacin ko shekara goma ba ta kai ba, Bintu ce ta haura sha amman kuma ba Hankali. Inna Mari ta tasa anta gaba Mariya da ke tare da su Jummai tana so ta je wajen Inna Meri Zuwaira ta riketa tana mata jan ido, Inna Meri ba ta damu ba ta kallesu tana fa an makaranta an dawo? Cikin su ba wanda ya kalleta har da sauran tawagan an su gaje kallonta suka yi suka watsar suka wuce gaba yan matan masu girma irin su Zuwaira suka tasa kannen su gaba sai gidan Wanzamai. Wanda kaf garin Gombe gidan wanzamai aya aka sani da ya yi shuru gidan da Inna Meri take aure a karo na biyu kenan. Ba ta damu kanta ba tunda ai ba yau aka fara sai ta rike hannun Bintu da Walida ta bi bayansu, Mansoor kuma ya wuce wajen su Mu'azzam da suka tsaya gaddaman wallon kafa sunan kuma sun dawo islamiya Mansoor na zuwa wajen ya tankwafi keyar Mu'azzam yana fa in"Wuce muje gida ka tsaya gaddaman tsiyanku na fama" Mu'azzam ya dafe kanshi yana yar dariya Nasir ya ce"To mai ani ai mu kuma sai mu kwana a hanya." Mansoor ya harare shi kafin ya ce"Nasir ka rika yin abubuwan ka cikin Aji don Allah." Makama ya ce"Gaya masa ya cika zubar da class." Ahmad dake gefe ya kwashe da dariya Nasir ya sha mur bai yi mgana ba suna ta hararan juna da Mansoor. Shi kuma bai damu ba ya tasa aninsa Mu'azzam a gaba yana rike da kwanon da ya kar a hannun Inna Meri suka wuce gaba su ka bar su Nasir a baya suna kallonsu. Duka yan nan tsukun anguwan ne, kuma tare suka taso tun suna an yara makaranta boko tare suka yi haka allo da islamiya. Cikinsu Mansoor da Nasir ne sa'anin juna sai Ahmad sai makama aramin sai Mu'azzam, kuma shima abin da ya sa ya zama tamkar abokinsu duk inda Mansoor ya saka kafa to a bayansa Mu'azzam ne ya na bala'in ji da aninsa, yana kuma kafa kafa da shi to saboda yana shiga cikin su ne ya sa suka ha gaba aya su biyar ma su mabambamtan hallaya. Kuma duka ana ru unun anguwa iyayensu suke sun san juna shiyasa abotan su ta yi tsawon da kowani lokaci suna tare. Gidansu Mansoor ne a gaba su kuma nasu Nasir sai an yi gaba shi ya sa su suka fara shigewa suka bar su Nasir ya yi tsaki kafin ya ce"Aji an renin wayau ne, ya cika zafi da masifa" sunan Aji da Mansoor ya samu acikin sunan shi su Nasir suka fara saka masa sunan saboda shi mgana aya biyu sai ya ce a ri a yin abu cikin Aji ko ya ce wane ba ka da Aji tun yana araminsa Mutun ne shi mai kamewa da son harkan girma ba ya son reni da kuma yin abu na marasa aji. Shiyasa da suka sanya masa sunan suna kiransa har a makaranta wasa wasa yau da gobe har sunan ya bishi acikin anguwa sai an ce Mansoor Aji a ke gane shi. Tun suna makaranta kuma sunan ya bishi Aji Aji, sannan a filin ball din su ma sunan shi kenan Aji mai Buga lamba goma tunda suna cikin group in matasa anguwan da suke buga kwallo har Team ma garesu mai Suna NASARA TEAM.! A lokacin da Inna Meri ta shiga cikin gida duka matan gidan suna tsakar gida, tunda gidan na a zamaninsa na baya kafin ya samu gyare gyare Gaje da Harira na tsakar gidan tunda a lokacin suna amfani da tsakar gida aya ne. Dakin Magajiya ne a farko na Inna Meri na daga an wani lungu ka an. Ta yi sallama ba wacce ta amsa mata kuma sun ji ta sai ta kada baki ta ara kwala sallama wannan karon Harira ce ta amsa sai Inna Meri ta ce"Ina ta sallama ba ku amsa ni ba." Sai ma suka yi kamar ba su ji ba kowacce ta na ji da anta suna ta kawo labaran abin da ya faru a makaranta. Bintu tuni ta warce hannunta ta wuce akin Inna Meri ta na tura baki yunwa take ji ta fara binciken neman abinci, Inna Meri aka bari tsaye da Walida kamar an da sa su. Magajiya na zaune saman kujera yar tauggono ta na tukin tuwo sai magana take yi da su Jummai kamar ba ta san da wanzuwar Inna Meri a wajen ba. Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce"Sannu da gida magajiya, ba ki ji ni ba ina ta sallama ba ne" Kawai sai Magajiya ta fara masifa tana fa in "To ina ruwana da sallaman ki da za ki zo kaina kina damuna, ni na tura ki gantalinki da sunan aiki da za ki dawo ki shaidamin kin dawo? nifa ba na son munafunci Meri ki yi ta kanki nima na yi ta kaina, ki yi harkarki na yi tawa tunda ba zaman juna muke yi acikin gidan nan ba" Ta fa a ta na wani kumfar baki dai dai lokacin da Mu'azzam da Mansor suka shigo gidan. Kuma tun a kofar gida suka fara jiyo jarabarta illai daman su san da uwar su ce tunda ta raina ta daman. Mansoor da ba shi da hakuri ya ariso yana in"Inna me ke faruwa ne? Tana ganinsu gudun wata fitinar sai ta ja hannun Walida tana fa in" kun ga ba wani abu ba ne. Mu je ku yi alwala ku tafi masallaci." Mu'azzam ya yi gaba shi da Walida Mansoor kuma ya tsaya yana kallon Magajiya kallon ki ki yayi kanki Itama ta kalleshi ta watsar Inna Meri ta turashi gaba ta na fa in muje Baban Inna an fara kiran salla. Da haka ta ja shi shashenta ta kar i kwanoon hannunsa ta ce Mu'azzam ya saka masa ruwa a buta su yi alwala. Bintu kuma na tsakar aki tana cin abinci Mansoor ya kalleta kafin ya ce"Ke kafira ce da baki sallah? Abincin ya kasa shiga cikinta ta damkesa a bakinta ta na girgiza kai, wani kallo yayi mata kafin ya ce"Ki bari na kara kifta idona na ganki a nan wajen sai na wahalar dake." Yana gama fa in haka ya shige aramin makewayin dake bangaren Inna Meri, Bintu kuma na tura baki ta mike Inna ta kar e kwanon abincin tana fa in"In ki ka yi sallar sai ki cigaba da ci tunda kin zama acici." Mu'azzam na alwala ya na mata dariya sai ta dauko murfin kwano zata je fe shi da shi ya sha mur ya na kallon kofar makewayin kafin Ya ce"Yayanmu ga Bintu..' Ai kafin ya rufe baki sai ga ta fito da gudu dai dai lokacin da yake fitowa daga makewayin. Tun kafin ma ya kalleta ta ce"Ba buta ne ina jiran Yaya Mu'azzam ya gama ya bani ne" Dariya ta kusa kama Inna dake duke ta na gyara ma Walida sikat in jikinta Mu'azzam dai sai da ya yi yar dariya yana yi ma Bintu gwalo. Sai da ya jira sa ya gama alwalan sannan suka fita masallacin tare suka bar Inna da su Bintu a gida suna yin nasu. A can masallaci suka sake ha uwa da su Nasir , Nasir har ya na ce ma Mansoor " Su Aji masu ani ka wani tasa shi gida, to mu ka ga ba mu je gidan ba." Yana jinsa ya yi masa banza daman ai basa zaman lafiya ba su da aiki sai fa a shi Aji taurin kai da saurin gusata shi kuma Nasir naci da neman mgana. A kofar masallacin su ka ha u da shamsu shima matashi ne kamar su ya kalli Masoor kafin ya ce"Ba dai ni ka zaga ba? Wlh sai naci uwarka." Mu'azzam na jin haka da sauri ya ce"Kai me yayi maka kake zaginsa? Nasir da Ahmad suka zagaye shamsu Aji na gefe ya har e hannaye a kirji yana jin wani irin zafin zuciya na taso masa wai shi shamsu zai ce zai ci uwarsa. Su a kokarin su Nasir shamsu ya gaya musu abin da ya faru duk ajinsu aya a islamiyan amman ba su san abin da ya faru ba tunda ba waje aya suke zama ba malaman suna raba musu wajen zama saboda in sun zauna waje aya ba sa karatu. Mu'azzam kuma ba ajinsu aya ba shi ya na Aji biyar ne su kuma shidda. Kuma dukkansu wannan shekaran za su gama babban sakandiri illah Mu'azzam da ke aji ayan babban sakandiri tunda shekarunsa iyakarsa sha bakwai cikin na takwas ne. Ko kafin shamsu ya gama maida ba'asi Aji ya dunkule hannu ya kai masa naushi saboda yana maida mganar yana ara fa in daga an ce Mu'azzam ba kaninsa ba ne shi ne zai zagar min uwa? Karya a