← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 208

Sashe 118

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya yi a gabanshi ta wani irin juyin da yasa sai da yaji wani Yarr!!!. Daga saman kansa har zuwa tafin kafarsa, idanuwansa daman sun ankance da barci sai suka ara shigewa ciki suka kuma sauya launi. Baya so ta fahimci yanayinsa shi ya sa ya kasa mgana kuma ya kasa auke idanuwansa daga kanta. "Na yi kyau? duba ka gani rigar ta yi min kyau? Ta ke fa a tana wannan dariyan nata ganin ya kafeta da ido bai ce komai ba ya da ta ariso gabansa ta ara juyawa lkaci aya tana fa in" Tsaraban da ka siyo min ne na saka duba ka gani sun yi min kyau? Kalli ka ga hulan." Ta fa a tana dukowa da kanta wajensa tuni amshinta ya fara shiga kofifin hancinsa, shi kuma okarinsa na kauce mata da wannan lamarin da ya kusa fallasa halin da yake ciki ya sa ya yi ko arin mikewa kawai sai Kanta ya daki kirjinsa yana mi ewa kuma jikinsu ya ha e waje aya. Dukkansu sai suka ji wani irin sanyi sanyi na ratsasu shi Aji da daman a ri e yake har wani jiri jiri ya ji, da baisan lokacin da ya saka hannu ya mai da Mimi gefensa ba ya wuce yana tanga i kamar zai fa i lokaci aya yana fa in" ki kyaleni Mimi ina jin barci ne." Bata yale shi ba sai da ta ara shan gabanshi kafin ta ce"To anan za ka kwana ko? Kai tsaye yace" A'a." Sai ta hade rai kafin ta ce" A'a kuma? wuce ta ya yi zuwa cikin akin domin ya auko jakarsa Mimi na ganin haka ta kwashi gudu ta riga shi shiga akin ta yi saurin isa wajen Wardrope ta rufe ta saka rike key in a hannunta lokaci aya tama fa in" Anan fa za ka kwana." Cikin ha e rai ya ce" To ai sai na bar miki kayan ba shike nan ba." Kawai sai ta ga ya juya zai fita, tana ganin haka ta ara saurin shan gabanshi lokaci aya tana mairaicewa kafin ma ta yi mgana da sauri a kausashe ya ce" Me ye kuma? Komai kika ce na yi miki, ki bar ni na tafi akwai abun zan yi ne a can." Kanta na kasa ta ce"To ka kwana anan gobe da safe sai ka tafin." Don Allah Kaji.." Ta fa a cikin muryan tausayi ba shi da za i illah kai da ya girgiza kai kafin y ace" Kin tabbatar gobe ba za ki yi rigima da ni ba ko? Cikin mirmshi ta ce" Eh da gaske nake.". Sai ya yi ajiyar rai kafin y ace" Shike nan" Sai ta ga yana shirin fita da sauri ta ce"A'a a gado fa za mu kwana." Waro ido ya yi yana kallonta kafin ya ce" Ke da wa? Ido ta sakar masa kafin ta age masa gira ta ce" Tare da ni za mu kwana." Baki ya saki ya na kallonta ita kuma sai ta shanye mamakinsa ta isa ga gadon tana ara gyarawa lokaci aya tama fa in" Daga yau ba za mu kara raba makwanci ba, In kuma can gidan kake so ka ri a kwana nima sai na tattara na tare a can tare dakai" Baisan ya harareta ba sai da ta yi dariya, kasa ma mgana ya yi, kuma ya kasa yi mata gaddama. akin ta bar mishi bayan ta bu e masa wardrope in sai da ya yi shirin barci ya cire kayan jikinsa ya saka na barci sannan ta dawo akin ta iske har ya kwanta a gefe ya rufe jikinsa da bargo amman rabin jikinsa zuwa kansa yana bu e ne amman ya juya baya sannan ya har e hannayensa a saman kirjinsa, ba abunda ya ba ta dariya sai na ganin ya jera filo guda biyu a tsakiyar gadon ma'ana ya raba tsakanin su, ba ta ce komai ba ta bu e Bangaren kayan ta ta auki na barci riga da Wlwando ta shiga tiolet ta shirya kanta daman ta rufe kofar waje itama shirin kwanciyar kawai ta yi, ba ta ji motsin Aji ba tana tunanin ya yi barci. Haka in ne domin duk yadda ya so kar barci ya kwashe shi sai dai ba shi da mafita sai da ya samu kansa da fa awa cikin nannauyan Barci. Ba ta cire abin da ya saka domin raba tsakanin su ba, itama sai ta kwanta a gefe ta rufe kafafunta da blanket in da ta ciro sabo tun da Aji ya kwanta da ayan a daran kwanan farinciki Mimi ta yi domin wani shuda en mafarki ne na ganinta kwance a gado aya da Aji abin da bata ta a tunanin faruwar shi ba. Dukkansu sakin jiki suka yi suka samu barci cikin kyakyawan salama sai asuba suka farka Kuma dai an ci sa'a dukkansu ba su da mugun barci ba wanda ya haura Bangaren an'uwansa. Safiyar Litini tana da zuwa aiki shi ya sa da wuri ta tashi ta ha a abun kari. Shi daman ya yi barci mai yawa jiya bayan ya dawo sallar asuba ka an ya yi barci sannan ya tashi ya yi wanka ya ce ma Mimi zai tafi, ita kuma ta ce su fita tare mana tunda itama za ta je wajen aiki ne. Galala ya kalleta kafin ya ce" Wai rage min hanya kike so ki ce za ki yi? Tasan halin shi ya sa ta ce" To sai ka tukamu." Kai tsaye ya ce" No.! Ki je kawai ba hanyar mu aya ba, zan hau mashin kawai.". Sai ta shagwa e tana cewa" Ko dai ba ka so naje na ga gidana ne? Abunda ta fa a yasa sai da ya an murmusa. Tare dolenshi suka fita domin Mimi ta nace sai sun fita tare, da zai hau motar sai da ya ce" Ni dai ba alfarma kika yi min ba, ke kika matsamin shi ya sa na shiga." Kai tsaye ta ce" Wace ni da yi ma Aji alfarma? Ai sai dai shi ya yi min alfarma." Wani auke kai ya yi ya na cin mgani shi a Dole kada ta raina shi ya hau motar ta. Shi ya ri a nuna mata hanyar sai gasu a Kofar gidan Aji na anguwan Tunfere. Mimi ta sha mamakin ganin makeken gidan da Aji ya gina ya i aminta ya sakata aciki saboda shigen tsauri irin na shi. Ganin ta fito ne daga Motar ya sa ya ce" Ki wuce wajen aikinki Nana Hajiya Fatima." Kawai sai ta fara yi masa dariya ya Juya ya ga akwai mutanen da ke wucewa sai ya yi saurin cewa" Ba fa za ki shigar min gida ba Malama." Mimi na kusa da motarta ta aga kai sama ta ce" Ni daman ba shiga zan yi ba, na dai ga shigar ka ciki." Bai san wayau ta yi masa ya Juya ya ciro key in gidan ya bu e gidan Mimi ta danno da gudu ta ture shi ta shige gidan ta barshi tsaye sake da baki, har key in gidan wanda ke tare da na motarsa da na mashin na fa i kasa, shi megidan ai sai dai ya biyo ta daga baya. Bai ce mata komai ba tana masa dariya ya ce" Kin raina ni Mimi Allah." Ranar Mimi shiriricewa ta yi a gidan Aji aki aki sai da ta shiga tana dubawa. Har akin Kayan motsa jikinsa Mimi ta ri e baki kafin tac e" To nima dai zan ri a zuwa motsa jiki" Kallon da ya yi mata ne yasa ta ce" To zan rika haya nawa ne? Kai kawai ya kauda yana danne dariyansa, Gajiya ya yi da ita a gidan ya rike a hannunta ya kai ta waje ya ce" Ki tafi wajen aikinki ki bar ni zan huta ne." Sai ta aga masa hannu tana fa in" Bye Bye." Bai iya komawa ciki ba sai da ta shiga motar ta bar wajen, shi kuma ya koma ciki ya motsa jikinsa ya yi wanka ya kwanta daman ya arya a can gidan. Bayan ta tafi wajen aikin ma ba ta barshi ya yi hutun da yake so ba ta rika kiran shi a waya har sai da ya gaji ya ce" Mimi ki yi wa girman Allah ki barni na yi barci." Kai tsaye tac e" Sai ka yi al awarin yi min duk abin da nake so." Ba tare da tunanin komai ba ya ce ya yi al wari Saboda dai ta yale shi ya huta. Ai ko dai ya yi ma kansa al warin da cikawarsa mai wahala ne. Domin Mimi na tashi aiki ta kira shi ta marairace ta ce Motar ta ta i ta shi ya taimaka ya zo ya auke ta. Ya ce shi yana barci ne ta kira bakanike mana sai ta ce sai dai to ta hau adai daita, kuma ai shi ya yi al wari ai wannan dai al wari ta bakin Aji ya ce ya zame masa bala'i, wasa wsa sai Mimi take son maida shi direban ta, ta addabi rayuwarsa yanzu dolensa a gidan yake kwana kuma a kan gado aya sai dai suna saka filo su raba tsakaninsu abincin Mimi yake ci, in ma bai ci ba ta ce duk in da ya ke sai ta biyo shi da shi. Haka kurum motar ta lafiyan ta kalau amman sai ta ce wai ta lalace shi zai kaita wajen aiki in ta tashi ya je ya auke ta, Daga baya ya gane lafiyan motar ta kalau domin daya gaji ya ce"Ke ki chanza mota mana, ni fa ba ki da ku auka ta direban ki." Ta na danne dariyan ta ce" Bani da ku in ne shi ya sa." Hararanta ya yi kafin ya ce"Zan rankwashe ki anan wajen , ni kike fa ama ba ki da ku i? Ina ku in gadon da Babanki ya mutu ya bar muku? jin ya ambaci babanta sai ta yi masa shuru shi kuma ai daman ya gano lagon ta. Kawai yana camp wani lokaci za ta kira shi ta ce ya zo ya auketa, motar tafi wata a wajen gyara ta i zuwa ta auko. Ranar da ya gaji key in
Chapter 118 · 0% Book details