Sashe 182
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta kawo ma Rukky ba ta sha ba zaune kawai ta yi , kamar mara lafiya, Mimi ta kariso ta zauna kusa da Rukky lokaci aya tana dafa Kafa anta cikin wani yanayi ta ce"Me ke damun ki ne Rukayya? Na damu da ganin ki cikin wannan halin don Allah ki gaya min abin da ke damun ki.? Rukky ta furzan da numfashi kawai sai ta sakar ma Mimi kuka kamar wata aramar yarinya. Ta ora kanta a saman kafa an Mimi tana shesshekan kuka daga gani kukan na fitowa daga asan ranta ne wanda ya da e yana cin ta a cikin zuciya ta kasa furtama kowa. Mimi ta ri a lallashinta ta hanyar an bubhuga bayanta da sigar lallashi. Har sai da Rukky ta daina kuka sannan Mimi ta ago kanta ta saka hannu tana share mata hawaye lokaci aya tana fa in" Ki daina kuka ki natsu ki gaya min abin da ke faruwa." Rukky ta ja numnfashi kafin ta ce"Nasir ne." Mimi daman ta tsammaci haka amman kuma sai da ta nuna mamakinta kafin ta ce"Me ya faru da Nasir in? Ko kun yi fa a ne? Rukky ta girgiza kanta kafin ta ce" Ba fa a muka yi ba matsala ce daga wajen mahaifiyarsa ta ce ba ta amince Nasir ya aureni ba." Cike da wani karin mamaki Mimi ta ce"To Saboda mene kuma? Ba an gama mganar cewa tura magabatansa kawai zai yi gidan ku ba.? Rukky na sharan wallah ta ce" Eh mana, mun gama mgana da shi kawai daga baya yake gaya min maman shi ba ta amince ba." "To saboda mene? Mimi ta je fa mata tambaya, Rukky ta gyara zama lokaci aya ta na fa in" Saboda hujjarta na fi karfin Nasir idanuwana sun bu e na yi karatu mai zurfi sannan ina aiki zan zo na fi karfin shi, zan raina shi zan kuma raina yan'uwansa da matansa Shi ya sa ta ce ya bar mganata ba ta amince ba." Sai kawai Rukky ta kara fashewa da kuka ta na cigaba da fq in" Ina son Nasir Mimi shi ya sa na shiga tashin hankali, yana ta ce min zai samu mafita amman har yanzu ba mafita ko mgana ta waya ma mun rage baya zuwa wajena saboda maman shi ta hana shi, ya a ke so na yi? wlh ina son shi ina jin wani zafi a cikin zuciyata Mimi" Haka ta ke fa a tana kuka kamar wata aramar yarinya, Mimi ma ta shiga tashin hankali cikin damuwa ta ce"Subhanallah to shi daman ya san ba ta amince ba ya tusa kansa? wallahi ban sani ba kuma ina jin ko Aji bai san abin da ke faruwa ba." "Ba wanda ya sani, ba na tunanin ya fa a ma wani" Sai Mimi ta ka a kai kafin ta ce"Abin bai yi da i ba, ki yi hakuri ki daina kuka bari na kira Aji na gaya masa kila akwai abin da zai iya yi a kai." Da haka Mimi ta auki waya ta kira shi, amman bai auka ba daman sun fi mgana da daddare ko da asuba sai Mimi ta cigaba da lallashin Rukkaya da kalaman kwantar da hankali.Har ta samu ta daina kuka ita dai Mimi ta ce ta yi ta addu'a abin da ya ke alheri ne Allah ya za a mata amman kuka da damuwa ba nata ba ne, Rukky na gidan har mangariba tare suka yi girki da Mimi ta na shirin tafiya sai ga wayar Aji nan fa Mimi ke gaya masa abin da ke faruwa kai tsaye ya ce"Topha, Shi kuma Nasir ya zai yi haka? Ya san ba amincewar iyayensa kuma ya zo ya bata ma ar mutane lokaci? Mimi ta ce"Ka ji fa, ita ta damu ne na ce ko za ka shiga mganar ne? Da sauri Aji ya ce"A'a ni bai gaya min ba kin ga kenan bai so na sani ba. Kawai ta koma gida ta cigaba da addu'a, mgana in ta ha a da iyaye tana da karfi in mijinte ne kaddara za ta sake ha a su." Tunda Mimi ta ji haka ta san cewa Aji ba zai yi wani abu ba Sai ta fara wani tunani acikin zuciyarta. Rukayya awarta ce da kowa ya santa tare da ita abokiyar kuka abokiyar dariya ba za ta iya barinta cikin damuwa ba. Har ta Rukky ta tafi tana tunanin yuyuwar abin da take tunani. Ta so ta yi mgana da Aji ta neme shawaransa sai kuma ta fasa a tunaninta sai ya dawo sai ta nemi shawaransa. Ba tare da wani tunani ba ta kira Jaheed a waya shima dai ya yi mamakin kiran nata tunda ba kiran shi take yi ba. Sai dai maganar da ta zo masa da shi ne ya ba shi mamaki, kai tsaye ta tambaye shi" Jaheed ka na da wata dudurwan da kake nema ne yanzu? Cikin mamaki ya ce"Eh a'a kinsan dai bazan rasa masu sona ba amman ni ba kowa a raina." Da sauri ta ce" In ka yarda da ni zan ha aka da awata Rukayya na san ka santa kuma ina mai baka tabbacin za ka so ta." Sai ta shiga ba shi labarin soyayyarta da Nasir da halin da a ke ciki. Amman ba ta gaya masa abokin mijinta ba ne ta roki Jaheed domin Allah ya fara mgana da Rukkaya domin ya yi mata gwaji ya tabbata dai, ba za ta kawo masa wani abu mara kyau ba. Bai yi mata gaddama ya ce"Ki turomin da lambata da ni da ita za mu iya daidaita wa tunda duka zukatanmu suna fama da ciwo iri aya." Ko Rukkyn ba ta gayamawa ba ta turama Jaheed lambar Rukayya a daran, amman ta turama Rukkyn sakon cewa Jaheed zai kirata sauran mgana sai sun ha Sai washegari suka ha u a wajen aiki Rukky ta tsareta da tambayan ba ta gane manufar ba ma Jaheed lambarta, Mimi kuma ta warware mata niyyarta na alheri Rukky ta ce"Ina son Nasir fa kin sani Mimi." Mimi ta ce"Ki cire sa a ranki domin mganarsa sai dai in kaddara ki bu e zuciyarki ku fahimci juna da ke da Jaheed kin san dai ba shi da wata matsala" Ita dai Rukky kamar ba ta yarda ba amman ta kasa yi ma Mimin gardama bi sa ga abin alherin da ta yi masa. Cikin ikon Allah kuma sai ga shi da Jaheed in ya kirata ta saurare shi har ta ke jin za ta iya manejj da shi a yanzu ko hakan zai rage mata damuwa a kan Nasir da har yanzu ba wata mgana mai da i daga bangarensa. Kwanansu Aji takwas suka dawo Mimi ta shirya masa tarba amman kuma sai ya Dawo a fusace kamar ya na jiranta.Fa a kan fa a ya na cewa shi ba zai iya ba ana kallonsa da mutumcinsa amman daga gefe ana masa kallon sakarai. Abun ya aurea Mimi kai ta ga dai ko da safen nan suna hanya sun yi mgana lafiya lau amman ya dawo kamar ya na jiranta ko an gaya masa wani abu ne a kanta mara da i ko an ce masa ta yin wanin abin ne? Cikin mamaki Mimi ta ce" Me kuma na yi? Ko wani abu ne ya faru? Kai tsaye ya ce"Komai ma ai ya faru, aikin nan na ki Allah za mu samu matsala da ke in har haka za'a cigaba da yin sa" Kenan mganar aikinta ne sai ta kasa mgana amman tana mamakin abin kuma ya faru. Wayarsa ya danna ya nuna mata Sreenshoot in da ya yi. Ashe wai shirin labaran da sukan ora a shafin su ta facebook wani ya yi comment da cewa" Na ga Hajiya Mimi na ta kumatu ne ko dai an samu aruwa ne? Aji to ya shiga kuma ya ga wannan Comment in a hanyarsa ta dawowa shi ne fa ya dawo a fusace. "Ba ta yuyuwa kina matata amman daga gefe kina burge wasu banzayen ba,ki ji fa wannan wula anci? Ina ruwan sa in kin yi kumatun? In ma kina da cikin ina ruwan sa? Matarsa ce? Ko anwarsa ne ya dace ya Fa i haka? Mimi ta kasa mgana kanta na kasa ta ce"Ka yi hakuri zan musu magana su rufe comments section Tashi ya yi a fusace ya shige ciki ya bar Mimi da dafe kai, gaba aya tarban da ta shirya masa duk ya rushe saboda kishi baya ya juya mata duk son harka irin ta Aji bai lalu eta ba, ga shi ta sha kayan gyara daga Kwararriyar mai gyaran amare da uwargidaye daga Surayya Dee Bojuwa da kanta. Kayan gyaranta suna da kyau da inganci tun da Mimi fa fahimci nagartansu shikenan ta ri e su, kema in kina son zama tauraruwar mata a wajen mijinta irin Mimin Aji nemi Surayya dee Bojuwa domin ki zama kasaittaciyar mace a gidan auranki.+234 803 277 3332. Tuni yanzu Mimi ke da lambarta suna waya duk abin da take so, in ta siya za'a saka a mota a kawo mata har gida, wani lokacin daga gidan yadikko ta kan saka makocinsu in nan ya kar o mata a tasha ya kawo mata har gida. Sai da mganar nan ta fi sati sanman Aji ya bar ta ta wuce, shima bayan Mimi ta yi ma Manaja mganar a rufe comments section mutane ba sa sanin abin da suke fa a. Kada mutane su kashe mata aure saboda mijinta na da kishi, maganganun na su ya na harzu a shi, kowa ya aminta da ita sai kawai a ka rufe comments section in gaba aya.. Aji kuma ko yana zaune ne in ya tuna da abin sai ya yi ta tsaki shi ka ai har ce ma Mimi Ya yi" Malama wai ba za ki iya komawa wani shashen da ba mai ganin fuskar ki ba ne? Kawarki ai tare kuke aiki amman ai ba'a ganinta ko? Mimi shuru ta yi ba ta ce komai ba, saboda lamarin Aji ya daina bata mamaki neman fin karfinta ma yake yi. Kishin sa a kanta mai yawa ne, ba aramin hakuri yake yi da aikin nan nata ba amman in abun ya