← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 208

Sashe 46

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka cika aikinsu yana fizge fizge riko aya suka yi masa sai ga shi a hannunsu to in takamarsa zuciya ya zo gidanta. Mommy dake cikin aki tana jiyo duk abin da ke faruwa ita da Khadija..ta yi kuka har idanuwanta sun sauya oauni Me ya sa Major zai yi haka? Me ya sa zai saka a kira yaro nan saboda kawai yaci zarafin su?. Tun azu Hajiya da Mimi ke kira ta kasa aga wayarsu. Khadija ce ke leke ta kofa ta dawo da sauri tana fa in"Mommy Abi kada fa ya yi kisan kai ga shi can ya saka soldeirs sun ri e shi." Mommy na jin haka ta mike jikinta na rawa ta ce" Ba zan bari hakan ta faru ba Khadija yau sai na karya dokar Major." Khadija na riketa ta fizge ta fita saboda ji ta ke yi kamar abunda ya ke shirin aikatawa bai kyautu ba. Kuma daman ya ce kada ta sake ta fito in shi bai kirata ba. Tana fita dai dai lokacin da Major ya ba da umarnin su yi ta dukan Mansoor har sai ya gane kuran shi. Mu'azzam na kuka yana ro on shi ya daka masa tsawa da cewa ya rufe masa baki ko shi ya tashi kansa da bindiga. Mu'azzam ya koma gefe yana danne bakinsa, ji ya ke yi kamar ya saki fitsari saboda tsoro. Mommy da gudu ta arisa gaban Major ta duka tana fa in"Please Habiba ka ce su rabu da shi, na ji bai kyauta ba sai ka gaya masa ba yanzu zaka aurar da arka ba, shike nan ka bar su tafi." A fusace ya kalleta kafin ya ce"Wa ya baki izinin fitowa? .How dare are u Murja? Ya fa a cikin tsawa sai kawai ta fashe da kuka tana kallon yadda sojojinsa ke dukan bawan Allah da bai ji bai gani ba. Ta yi rokon duniyan nan ya kauda kai ya ce in har Mansoor ba zai ba da hakuri da bakin shi ba su yi ta dukan shi har gobe da safe. Mommy na kuka ta ce" To in suka kashe shi fa? Da arfi ya ce"In ya mutu banza ne ya mutu, rayuwarsa ba ta da wani amfani da ni zai yi wasa? Am i his mate? da Major zai yi gogayya yana an talakawa irinsa? Agola yaron mai aiki a arkaahin mahaifiyata , su dake shi in ya mutu zan saka su wurga shi daji namun daji su cinye banza a banza kuma babu abin da zai faru." Ya fa a ko a jikinsa sai ma hannayensa da ya goya a baya ya na jin da in a abunda su ke yi. Kukan Mu'azzam da na Mommy ya cika falon a gaban idanuwansu sojoji suka sumar da Mansoor gau saboda duka Sannan kuma anan take ya saka su suka dauke shi yace su je fa shi a cikin kurku zuwa safe. Sannan ya kalli Mu'azzam yanq fa in"Kai kuma zan baka wajen kwana, da safe ka san in da dare ya yi maka, yaron nan ba zai bar gidan nan ba sai ya gane ya ja da Major Kabir sulaiman Dabo sai na arar da rashin kunyarsa.,": Mu'azzam ya kwanta a gaban Major yana fadin"Don Allah Sir ka yi mana rai ka yafe masa." Mirmishi ya yi irin mirmishin basawa kafin ya ce"Sai na ga waye Boss tsakanin ni da shi."Daga haka a fusace ya bar falon ya taka zuwa akinsa bayan ya ba ma wani Soja umarnin a kai Mu'azzam aki ya kwana zuwa da safe. Sai bayan shigewarsa Khadija ta fito ita kanta sai da ta yi kukan tausayin Mansoor da Mu'azzam wanda shima aya daga cikin sojan ya zo ya ja shi sun bar falon Mommy haka ta ke kuka khadija na hawaye. Dakyar ta iya tashi ta shiga kitchen ta zuba abinci a faranti ta fita kofar falon da kanta ta yi ma shugaban sojojin tsaron gidan mgana ta mika masa abinci ta ce a kaiwa Mu'azzam wanda aka fitar da shi daga baya. Khadija kuma ta saci wayar Mommy ta kira Hajiya ta na hawaye ta labarta mata abin da ya faru Hankalin Hajiya ya tashi acikin daren ta Kira Alhaji Hamza tace gobe gobe ta ganta a Abuja, Mimi daman ta ji a jikinta tun kafin Hajiya ta sanar mata abunda ya faru ta ke kuka abun tausayi. Hajiya har kuka sai da ta yi na wannan cin zarafin da Kabiru ya aikata yanzu da wani ido za ta kalli Meri da Baba anjuma? ta yi nadama in da tasan haka zai faru da ba ta yarda ta tura su ba. Shima Mu'azzam lokacin da Mansoor ke shan duka wayarsa ta fa o daga cikin Aljihunsa sai ya yi sauri ya auketa, shima wani aki a ka saka shi amman ba'a kuntace ba ne kuma an kawo masa abinci amman tashin hankali ya sa ya manta da wata yunwa. Inna Meri ba ta da waya, Baba anjuma kuma ta shi ta lalace Nasir ya samu nasaran kira Mu'azzam na kuka ya na gaya masa halin da ake ciki da kuma rokonsa ya je ya gayama su Baba ga halin da Mansoor ke ciki yanzu haka bai san inda suka kai shi ba ko ya na da rai Allahu shi ya sani. Nasir ya shiga imuwa, a daran ya tafi gidan su Mansoor ya iske Inna Meri itama ta kasa barci saboda tunanin halin da ya'yanta ke ciki labarin da Nasir ya gaya mata ya sa ta fasa kuka har yan cikin gida su ka ji. Baba anjuma na akin Magajiya ya fito da gudu shi kanshi da ya ji abin da ke faruwa sai da cikinsa ya karta. Inna Meri na salati ta na kuka tana fa in"Shike nan abinda nake ta gudu ya faru." Su Baba anlami kuma suna ta fa a suna fa in yaro zai jawo musu fitinar da ya'yansu ma ba su jawo musu ba. Nasir shi ya kira Makama yana gaya masa halin da ake ciki su kansu sun shiga tashin hankali daman su san halin taurin kan Aji gashi nan ya kai kansa inda za'a kashe shi. Saboda dare ya yi ya sa a ka bar ma gobe har da safe sai da Mu'azzam ya sake kiran Nasir ya ce har yanzu bai ga Mansoor ba kuma shi ba zai tafi ya bar an uwansa a wannan bakin gidan ba. Nasir ya ce ina kada ya je ko'ina bari ya je can gidan ya gani, ai yana zuwa sai ya ji labarin tun safe Inna Meri da Baba anjuma suna gidan Hajiya shima sai ya Nufi acan, can in ma abun tausayi Mimi ta kwana kuka duk idanuwanta sun kumbura haka Hajiya ya iske Alhaji Hamza ya yi musu Bucking din jirgi zuwa Abuja har da Inna Meri da Baba anjuma za'a tafi, Inna Meri fa i take yi"Sai ni naje na duka na bashi hakuri zan ro e shi Allah ya sakar min ana ba su da kowa Allah ne gatan su." Yaddiko na gidan itama duk daga baya take jin labarin abubuwan da suka faru. Amman abunda Yaya Kabiru ya aikata ya yi son rai, ba kyau ka wulakanta mutum. A ranar suka bi jirgi zuwa Abuja daga filin jirgin suka hau taxi zuwa gidan su Mimi da ke Abuja Mommy ce kawai ta san da zuwan su domin itama ta ce ya kamata su zo gaba aya in ba haka Major zai kashe yaron mutane. Yana Office Alhaji Hamza ya kira shi ya ce ga su sun zo har da Hajiya ma.Shi ya yi tafiyar sa ma ya bar yaron mutane sojoji na yi masa azaba, Mu'azzam kuma ya i tafiya saboda tun jiya bai kara ganin inda a ka kai masa Dan'uwa ba, abinci ko ya kasa saka shi acikin cikinsa shima ya yi kuka ina zai nufa gida cike da sojoji shima yanzu su kamashi su yi ta ta duka Mommy ta aiko masa da abun kari ruwan zafi kawai ya iya sha yana jiran zuwan su Inna Meri tunda Nasir ya sanar da shi tare da su za'a taho. Mu'azzam na haraban gidan tsaye su Inna Meri suka iso, wajen su ya nufa yana kuka ya rumgume su. Mimi kuma tana kuka ta kwashi gudu zuwa cikin gida tana kiran sunan Mommy. Inna Meri sai tambaya take yi Ina Baban Inna? Mu'azzam na kuka yana fa in"Inna an kai shi wani aki, ban kara ganinsa ba a sume su ka fita da shi. Jini na zuba ajikinsa." Mu'azzam ya kara rushewa da kuka Inna Meri na salati da sallallami. *Janafty* *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA* Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi kamar haka. *Zumar Matsi Guarantee 3500* *Maganin sanyi komai nacinsa 4k* *Zumar kacha kacha 2500* *Zumar kiba 4k* *Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki* *Dahuwar kaza ta manyan mata 8k* Zaku sameta a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani arin jin da in ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0 *Page 15* Baba anjuma kuma sai maimaita fa in" Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un" kawai yake yi shi kan shi ba domin yana namiji ba tashin hankalin da suke ciki ba zai saka ya iya mallakan kansa ba. Ba shi ya haifi Mansoor ba amman da gaske yake yi ya kar o amanarsa kuma yana jin sa kamar Mu'azzam ne shi a wajensa. Tabbas Baban Inna ya janyo ma kansa fitinar da tafi karfinsa haka Inna Meri da Baba anjuma ke ta raya acikin ransu saboda ganin samudawan Sojojin dake tsaran gidan Major fuskarsu ba fara'a daga gani ba su san wani abu wai shi Imani ba sun fi gane yaren umarnin wanda ya ijiyesu. Su kansu kafin Sojan dake tsaren get ya amince su shiga sai da Alhaji Hamza ya kira Yayan na shi da kansa ya yi masa mgana sannan
Chapter 46 · 0% Book details