← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 208

Sashe 158

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rukky ta balla mata harara kafin ta juya ta na kallon Aji ya gama wayar yana tahowa wajensu da sauri ta matsa kusa da Mimi lokaci aya tana fa in" Dilla behave you self." Duk da bai ji abin da ta fa a ba amman ai ya ga bakinta na motsi, yana jin sau aya ya ta a ganin Rukky amman yana ganinta sai ya ganeta ita ce wannan kawar ta Mimi wacce ba ta masa ba munafuka ce, illau ga shi yau ya ga shaida sai wani kyfta ido ta ke yi alamun ba ta da gaskiya. Shi kuma cikin yanayin takunsa na masu karfi da Kuzari ya arisa gabansu duka hannayensa zube a cikin aljihun wandonsa. Sai da ya zo gaban Mimi Sannan ya tsaya ya kuma saka hannu ya an daga gularsa sama yana are mata kallo daga sama har asa ya juya yana kallon megadi na zaune a mazauninsa da radion sa ya na ji. Sannan ya juya ya na kallon Mimi Sai dai ba fara'a ko ka an a fuskarsa sannan Rukky dake wajen ko kallonta ma bai yi ba, sai ma ya yi kamar bai san da wanzuwar a wajen ba. "Haka kike fitowa waje ba hijabi ba mayafi Mimi.? Haka ya fara fa a lokaci aya yana ara da une fuskarsa kamar wanda aka fa a masa wani mummunan sa o, Mimi ta kalli Rukky itama ta kalleta a ranta dai sai da ta ce mai hali baya fasa halinsa amman a fili sai ta ha e rai itama ta juyar da fuska tana fa in" Wa ya gaya maka na dawo? sannan me yasa ka zo ba Sanarwa? Ta fa a tana wani masa jijjigan jiki lokaci aya tana ta o hannayen Rukky wacce ta dukar da kanta ta asa ta kasa agowa saboda Aji ya yi mata warjini ba ta auka za ta kasa ha a ido da Ajin in suka ha u gaba da gaba ba. "Alhaji ne ya gaya min kin dawo. Sannan domin zan zo wajen matata ai ba na bukatar an sa Haka ya ce mata yana kallonta cikin ara nazarinta da sauri ta kallesa kafin ta ce" Wani Alhajin? Kafin ya samu damar magana ta zaro ido tana fa in" Wai Daddy ne Alhaji? Ba za ka iya kiransa da sunan Daddy ba kenan? Ta fa a cikin masa wani kallon kasa asa, cikin mamakinta ya ce"Daddy kuma? To ai kinsan ni a gidan da aka haifeni da in da na taso, Inna da Baba muke cewa, in kin ji mun ce Alhaji alamamun girmamawa ne." Ita kanta ba ta san ta masa wannan kallon ba sai da ta ga ya yi mirmishi wanda tun zuwansa wajen bai yi ba sannan ya ce"To na bari, Daddy ba shike ban ba? Sai ta gya a masa kai, kawai sai ya gyara tsayuwa a ransa ya na fa in"Rigimammiya kawai." Rukky ce ta ga kamar Har Mimin ta manta da ita. Sai ta matsa gefe tana fa in" Mimi zan tafi, yamma ta yi" Ta gama fa a lokaci aya tana duba agogon fatan dake tsitsiyan hannunta na hagu sai a lokacin Mimi ta tuna da ita domin har ga Allah in tana gaban Aji mantawa take yi da kowa da komai ciki har da ita kanta ma. "Aji ga awata Rukkaya, Rukky ga Aji ku gaisa." Mimi ta fa a cikin Mirmishi tana kallon su duka, Aji ya yi shuru yi ya yi ma kamar bai ji ba sai can ya ce"OH na ganta." Daga haka ya juyar da kansa yana kallon wani arayin Rukky ta watsa ma Mimi wani kallo ita kuma tana faman ro onta da hannu a kan ta gaishe shi abin da ba su sani ba duk yana kallonsu ta gefen Ido, abin da ya bashi mamaki ita yanzu awar Fatima Jira take yi ya gaisheta? Amman yarinyar ba ta da hankali ya fara tunanin haka. "ina yini" Haka Rukky ta fa a Kamar ba ta so. To daman dole Mimi ta saka ta, sai da ya nisha u sannan ya juya yana kallonta lokaci aya yana fa in" Barka da amma" Sannan sai ya juya yana kallon Mimi kafin ya ce"Na auka tana jiran na gaisheta ne." Sai Rukky ta ji kunya ya kamata da sauri ta ce"A'a na bari ku gama gaisawa ne." "Gaisawa? da wa? Ba gaisuwa muke yi ba ko kin ji sanda ta gaishe ni? Sai Rukky ta kasa mgana shi kuma sai ya cigaba da fa in" Ko ita awar taki ba ta isa ta zauna in gaisheta ba, koda nake auranta ba ta isa ba." Daga Rukky har Mimi kai suka jinjina, kafin Rukky ta ce"Ta cancanci ka gaisheta mana, ka fa ba ma awata wahala." Ta fa a tana yar dariya mirmishin gefen baki ya yi kafin ya ce" Ita ka ba ta gaya miki nima ta ba ni wahala ba? Mun ba ma juna wahala shi ne gaskiyan magana." Ya fa a yana kallon Mimi ita kuma sai ta harareshi ta na tura masa baki har sai da ya yi yar dariya Rukky na tsaye tana kallon Ikon Allah a tunaninta Mimi ba za ta sakar masa fuska a zuwan farko amman kalli abin da take yi. Shi kuma agogon hannunsa ya duba kafin ya kalli Mimi ya na fa in" Kina da mintina goma,ki sallami ba uwar ki, ina son mgana dake." Yadda ya yi maganar cikin ba da umarni ya sa Mimi ba ta ga damar masa musu ba sai ta ce ya shiga falo ya jira ta bari ta taka ma Rukky kamar zai ce rakiyar ba ta isa haka nan ba sai ya fasa bai shiga cikin gidan ba ya tsaya nan yana jiranta daga in da yake suka matsa gaba ka an yana gani Rukky na ta magana Mimi na marairaicewa kamar hakuri take ba ta shi fa baya raba ayan biyu duk abin da Mimi ta aikata ba tunaninta ba ne tunanin wannan awar ta ta ce, kuma daman tana da fuska da yanayi na munafukai. Dole Mimi ta sallami Rukky ganin uban gayyar ya kasa ya tsare ta na fita daga get in Mimi ta dawo wajensa tana fa in" Ba ka ciki ba ? Kai tsaye ya ce"Ke nake jira, sannan kada ki ara fitowa a haka ba ki saka babban mayafi ko hijabi ba." Baki bu e ta ce" A cikin gidan? Kansa ya auke kafin ya ce"E na dai gaya miki." Yanayin yadda ya ha e rai ne ya sa dole ta yi shuru tana gaba yana Binta a baya har zuwa falon gidan Hajiya ta ce ya zauna sai ya samu kujera mai zaman mutum biyu ya zauna ita kuma ta ce tana zuwa. Sai ta juya tana tafiya ya bi ta da kallo yana ha iyan miyau har ta auke ma ganinsa Ajiyar zuciya ya sauke dole ma ya ijiye duk makaman ya in sa matarsa yake bukata cikin lokaci. akin Hajiya ta fara shiga ta isketa tare da Baaba Uwani suna mgana ta gaya mata zuwan Aji sai ta koma akinta domin ta gyara fuskarta, ita kuma Hajiya ta fito tare da Baaba Uwani ta gaishe shi ya amsa cikin yanayinsa sannan ta shiga kitchen ta kawo masa ruwa da lemu, Hajiya kuma har kasa ya sauka ya gaisheta ta na masa tsiyan ba ta ce in Binta ba ta son auran ita a zo a yi da ita ba kansa na asa ya ce shikeman in ta i komawa sai ya zo kawai su daidaita Hajiya na ta dariya bayan tambayan su Meri ya ce tana gaisheta kai tsaye Hajiya ta ce"Ai ka gaya mata na ce na yi fushi, tunda abun nan ya faru ban ganta ba sannan ba ta kirani ba." Mirmishi kawai ya yi ba tare da yayi wata magana ba, nan Hajiya ta bar shi ta shige ciki ta je ta na yi ma Binta tsiyar ta shanya shi, ita kuma har kaya ta sauya daga baya sai ta fasa domin zai auka ta hakura ne tunda har da kwalliya sai ta maida wanda ta cire har da saka uban hijabi sanda ta dawo falon yana zaune ya gama shan ruwa kenan kujeran dake kallonsa ta zauna shi kuma ya na kallonta daman tun shigowarta. Cikin mamaki ya ce"Wannan hijabin fa? fita za ki yi ne?. Kai tsaye ta ce"A'a ba kai ka ce na ri a saka hijabi ko a cikin gida ba ne? Dariya ta ba shi har sai da ya dara sannan ya ka a kai kafin ya ce"Kin yi nesa da ni, ta ya ya za ki iya jin abin da zan fa a? Ki matso nan domin ba zan aga murya ba." Ya fa a yana nuna mata kujeren dake gefensa mai zaman mutmn uku ba musu ta mi e ta koma nan ta zauna sai da suka auki wani lokaci kowa na sake sa e sannan Aji ya yun ura ka an yana fa in"Ina fatan hutun da kika yi ya ishe ki?. Kallon bangane ba ta yi masa sai ya cigaba da fa in" Na san ban kyauta ba. Mu manta abin da ya faru a baya Mimi ki dawo gare ni domin na nuna miki komai ya wuce." Kai tsaye ta kalle shi domin ta ga da gaske yake yi sai kawai ta kauda kai kafin ta ce"Ni fa na auka takardan saki na ka kawo min." "Subhanallah, ki daina wannan zencen ni ban aureki domin na sake ki ba" "To ana dole ne? tun da ka ce ba ka sona? Sannan ba za ka iya daraja iyayena ka manta abin da ya faru saboda ni ba, ni ma kuma ban ga laifina domin na ce ba zan cigaba da zama da kai ba." Yadda take mganar da alamun abin na taso mata ne domin kamar za ta yi kuka, huci ya fitar daga bakinsa kafin ya ce" acin rai ne ya sa duk na fa i wasu mganganun, ki yi hakuri." Mamakin yadda ya yi saurin laushi ta yi sai ta kalle shi shima ita yake kallon cikin irin kallon nan mai kassara oafiyan jikin a mace, ita ta yi saurin kauda kanta kafin ta ce" Wasu
Chapter 158 · 0% Book details