Sashe 193
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bai kawo masa Mimi ma ba haka ya kamata ta je ba. Amman ganin kayan da Inna ta nuna masa sai ya farga daga nan gidan Inna sallar isha'i ya tsaya ya yi a hanya sannan ya shiga gida ya iske gida sai ta shin kamshin turaren wuta, ga kamshin girki ga kanshin matar gidan da ta cha a ado ta ci kwalliya domin farincikin mijinta. Tarba ta yi masa kamar yadda ta saba, suka makale juna kamar wani zai raba su. Bayan ya yi wanka suka zauna saman dining suna cin abinci jefi jefi suna hira. "My Jan me za mu siya na sunan mai sunan Inna? Kamar daga sama ta ji tambayar na shi, lokacin ma nama ne a bakinta sai da ta hadiye ta sha ruwa sannan ta kallesa kafin ta ce"Kamar me kenan? Sai kawai ya ce"Kaya mana, ba na ga wai ana siyan atamfa ko kayan jarirai ba." Sai Mimi ta saka dariya kafin ta ce"Ashe ka sani, ko gaya maka a ka yi? Kai tsaye ya sanar da ita a gidan Inna ya gaani mirmishi ta yi masa kafin ta ce"Ni ai ban jira ka ba, mu gamaccin abinci mu shiga ciki ka gani." Sai da su ka gama cin abincin ta kwashe komai ta kai kitchen. Sannan ta gyara wurin ta rike masa hannu zuwa akinta a saman gado ya ga akwatinta arama. Gefen gado ta zaunar da shi sannan ta bu e wardrpe ta auko wata katuwar leda, ta sauke a gabanshi shi kuma dai dai lokacin ne ya kalli akwatin nata kafin ya ce"Wannan akwatin fa? Ko shima kayan sunan ne a ciki? Mimi na dariya ta ce" Kayan dai mai zuwa suna, kasan sati fa zan yi ina so ka bar ni zan je kofar soro na gaishe su sai kuma na le a gidan Dr." CBai samu ma bakin mgana ba, ya ga kawai ta zazzage ledan hannunta kaya sun fa o, Atamfa da less sai rigunan Jarirai masu kyau guda uku sai katon pampers guda aya sai wifer, sai wasu huluna na jarirai da safa a kalayensu masu kyau sai over roll shima na kwali masu kyau guda uku sai saitin man shafawan yara mai ha e da hoda da olive. Ta gama aga masa kayan ya gani sannan ta maida a leda lokaci aya tana fa in" Ni na gama mawa saura naka uban Maryama." Mirmishi ya yi kafin ya ce"Duk yaushe kika yi wannan siyayyar ban sani ba?. Gira ta aga masa kafin ta ce" Zauna nan, kasuwa na je ni da Rukkayya." "Da izinin waye kika je kasuwan? Haka ya fa a yana tsare ta da Idanuwansa sai kawai ta saka masa dariya kafin ta ce"Da izinin mijina mana, ka manta ranar na ce maka Rukky za ta rakani anguwa? Ka ce sai na dawo kada na yi dare? To ai kasuwan ne anguwan" Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Na ji kin yi naki, ni me ya kamata na yi? Sai da maida ledar in da ta auko sannan ta zauna gefensa kafin ta ce" To me ya kama ta ka yi? Tunda ni na siya wa anan kayan me zai hana kai sai ka ora mata da Ku Kai tsaye kuma ta cigaba da cewe" Ku in zai fi, tunda ka ga ni na siya kayan sai mu ora da ku in zai fi." Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Shike nan amman kamar nawa ki kke ganin zan ora na ku Kai tsaye ta ce" Duk abin da Allah ya hore maka Merapyaarr" Sai ya gya a kai kafin yace bari da safe in Allah ya kaimu. A daran bai mata mganar satin da ta ce za ta yi ba sai da safe tunda tun asuba ta tashi tana aiki. Daman tun a daran jiya ta yi masa miya saboda tasan shi ba ya son aiki. Sannan ta saka an yi masa snak cake da cincin da samosa ya ri a shan Tea da shi kafin ta dawo duk kuma ta kaisa kitchen ta nuna masa, har tana cewa ya ri a dafa farar shinkafa ko taliya ya na ci da miya. Kallonta ya yi a karkace kafin ya ce"Wai wata za ki yi ne a can? Mimi ba ta ba ma tambayansa muhimmanci ba ta ce"Ka manta, na ce maka zan yi sati aya." Bai ara mgana ba. Sai da suka karya har Mimi ta yi wanka tunda Bintu ta kira ta ce suna gidan Inna ita a ke jira mai motar ya ce karfe tara na safe za su tafi, Aji ya riga ya biya ku in motan na zuwa da na dawowa. Sai da suka zo sallama duk da shi zai kaita gidan Inna a motarsa, ya rumgumeta yana shafa cikinta da ya fara tasawa lokaci aya kafin ya ce"My jan.." "Uhm Merapayaar." "Bai kamata ki je ki yi sati ba. Saboda kina da juna biyu ni ya kamata na ri a kula da lafiyarki, don Allah ki yi kwana biyu ki biyo su Yaya Halima ku dawo" Da sigar lallashi ta fa a, da yasa ta yi shuru ta lafe a jikinsa. Ganin ta yi shuru yasa ya ara sausauta murya kafin ya ce" Na saba dake, ba zan ji da in zama ni ka ai ba, ba ki tausayina? Wa zai rika ba ni abinci yana min hira? Ki bari daga baya ko bayan kin haihu ne sai ki je ki gaishesu. Ni sai ma mu tafi tare na rakaki amman na roke i da Allaj ki dawo tare da su Yaya Halima.". Nan ma shuru ba amsa, Idanuwanta ya ciko da kwallah. Domin har ta fa a ma Mommy za ta je soron inki, sannan kuma yanzu sai ta ce ba za ta samu zuwa ba? Ganin yadda ta nuna ne ya sa sai ya raba ta da jikinsa lokaci aya yana fa in"Amman kin kin ga da takura ba zan hana ki ba, ki yi satin sai ki dawo daga baya." Sai kawai ya juya zai fita daga akin da sauri ta ri o hannunsa kafin ta rumgumeshi ta baya lokaci aya tana fa in" Umarni kawai za ka ba ni ba alfarmana za ka ro a ba, ai zaman ka nake yi, Kada ka damu zan dawo in sha Allahu tare da su." Kamar zai yi kuka ya juyo yana fa in "Kwana biyun za ki yi ko? Sai ta gya a masa kai, rungumeta ya yi cikin farinciki lokaci aya yana fa in" Allah ya miki albarka My Jan, na yi miki izinin ko Walida ko Bintu su raka ki ki je ki gaishe su kin ji ko? Sai ta gya a masa kai, Ita da kanta ta yi age ta sumbaci kumatunsa. Shi kuma ya yi saurin dam anta ya rankwafa yana sumbatar bakinsa, ita kuma sai ta zagaye hannayenta daga bayansa ta rumgumosa sun da e a haka kamar ka da su rabu gani ta yi zai ata mata kwalliyarta yasa ta wace jikinta lokaci aya tana fa in" Suna jira na fa." ara ri ota ya yi lokaci aya yana fa in"Minti biyar to." Dole ta kyaleshi ya rumgumeta kawai ya na shakan kamshinta. Sannan ya sake ta lokaci yana ri e mata hannu ayan hannun kuma ya rike akwatinta, sai ta kar a Lokaci aya tana cewa"Sai na sauya shiri." Shi taya ta ta rage wasu kayan, kayan sunan ma da za ta kai ma Hibba duk a ciki ta tusa kafin su fito har Yaya Amina sai da ta kira shima Kuma Mansoor Auwal na ta kiran shi Mu'azzan tun asuba ya kira baki ya i rufuwa yan'uwansa suna hanya. Shi ya rike mata akwatin har jakarta sannan ya saka mata mayafinta a saman kanta ya rike mata hannu ya kai ta har mota, sannan shima ya zagaya ya shiga a hanya suka tsaya ya cire ku i 50k yace ta ha a ta kai ma Hibba ta amsa lokaci aya tana fa in. "Mungode Baban Maryam Allah yasa ka ma nema albarka." Yana mirmishi ya ce"Amin Amin Ummu Maryam." Suka ha a ido suka yi ma juna mirmishi, ya rike mata hannu da hannunsa guda aya, ayan kuma ya na tuki dashi, kewarta yake yi tun kafin ta tafi, ganin yadda ya matse mata hannu yasa ta rike hannayensa da hannunta guda biyu ta jimke kafin ta kallesa cikin shagwa a Ta ce. "Ina sonka, ina matukar kaunar ka.." Wani kayattacen mirmishi ya saki kafin ya ce" Kin san dai na fi ki son ki ko? Ina sonki, ke ce komai nawa Fatima." Sai suka urama juna ido, ganin kamar hankalinsa na kanta yasa da sauri ta ce"Tuki kake yi, ka kula Merapayaar" Sai ya maida hankalinsa kan hanya Allah yasa ma titin ba motoci sosai. Suna tafe amman suna ame da hannuwan juna "Ki kula da kanki, kin auko magungunan ki? Sai ta gya a masa kai kafin ta yi mgana ya yi saurin cewa"Ka da ki ci wani abun da cikin ki ba ya so, ina son cikin nan Mimi nima na osa ki haifamin wata Maryama mirmishi ta yi masa kafin ta ce" In sha Allahu kada ka damu." Sai ya jinjina kansa, sun shigo anguwan Tunfere kenan ta ji yana fa in" Na ma gayama Mu'azzam ya kula da ke, kina da juna biyu." Mimi ta kalleshi cikin jin kunya ta ce"Kai, wai kai baka jin kunyar gayama mutane ina da juna biyu? Suna tsayawa ofar gidan Inna dai dai lokacin da ya kalleta yana fa in" To miye a ciki? Ai ba abun kunya ba ne na ga abin farinciki ne kowa kuma na son matarsa ta samu ciki." Mimi ta ce"Duk da haka dai ba a fa a sai dai a gan shi ya fito, haka fa da muka je gaida Daddy ka fa a masa wai ina da juna biyu." Dariya ya yi mai sauti kafin ya ce"Kin ji ki da wata mgana? Abun kunya ne? Na ga dai abun alhafari ne, kuma ke ba ki san masu shege ma suna nuna ma duniya ba? Ballantana ni da an sunna zan haifa" Dai dai yana bu e mota ya fito sannan ya zo ya bu e mata ya