Sashe 11
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a Lokaci aya tana mikewa Hajiya ta ka da baki ta ce"Gaskiya kwanciya da zama waje aya ba da i. Kabiru Allah yasa kaffara ne amma ana ta Ibada Allah ya bamu sa'a kawai." aka amsa mata da Amin Shi kuma Abi sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Honey kyaleni kawai nafi jin da in kwanciya in na zauna sai kuguna ya rika min zafi zafi wani lokacin.' Sulaiman ya kariso yana fa in "Abi to ai saboda kana jimawa a kwance ne, yawan zaman zai rage lan washewar da jikin ka ya yi a waje aya" Kwallah suka cika kwarmin Idanuwan Abi ya yi saurin shanyewa yana fa in"Ku kyaleni kawai, na fi jin da in kwanciyar fiye da zama." Yadda ya yi mganar ne ya sa sai jikin Kowa ya yi sanyi, Hajiya ta yi tagumi kafin kuma ta fara sharan wallah tana fa in "Lafiya lau kabiru ya bar wajena ina saka masa albarka, sai ganin Hamza nayi yazo cikin imuwa ya na fa a min Kabiru sun samu hatsari a hanyarsu ta komawa Habuja, Allah ya ji an Mallan Sale ina ganin fuskarsa a cikin Idanuwana har yau wlh." Sai akin ya dauki shuru aka koma Jimami, Abi kuma hawaye suke ziraro mai ta gefen kunnuwansa duka biyu Mommy ke saka tissue tana share masa, Mimi ta sauke wayar hannunta ta na sauke numfashi hankalinta duk ya tashi, in ta kalli Abi sai ta ji ta kara tsoron rayuwa gaba aya ba Abin da ta sani a baya ba ne jajirtacce namiji wannan Abin a kwance yake yana kokuwa da kaddaran Ubangijinsa. Sai da Hajiya ta dai na kukan sannan Abi shima ya dai na. Shigowar Sisto Khadi ya sa sai a ka shiga wata hirar na dabam, Jawahir kuma taja ayant azuwa Kitchen suna kukan yunwa suke ji, ita kuma Mimi sai ta koma kan wayarta tana karanta sakon Baby Rukayya. "Don Allah ko sunan shi ki fa a min Mimi ta" Charting suke yi tana ta mata magiyan sai ta fa a mata sunan wanda ta ji yaddiko da Hajiya na mgana ita kuma ta ce mata wannan wani abu ne da ya shu e bukatar taso da mganar da ba ta da amfani. A wajen aiki ma haka Rukky ta rika yi mata magiyan wai sai ta ba ta labarin shi ko wannan mutumin waye shi da Mimi ta kasa mantawa da shi. Ita kuma Mimi ta ce ta bar damunta da wannan mganar, abu ya riga ya wuce ba amfanin ta da maganar yanzu. "Sunan shi Hayatu.." Sai ta fara yar dariya saboda yadda Rukky ta turo mata emojin kuka da damuwa, saboda Hayatu sunan saurayin Rukayya ne da suka rabu shi ya sa ta mata shakiyanci. Tana cikin Mirmishi taji Hajiya na fa in"Hamza fa ya matsa kan mganar Jaheed da Binta, yaddiko ma ta yi min orafin tunda shi Jaheed in na sonta mai zai hana ayi yar gida? Mimi ta tsaya cak da abin da take yi tana kallon Hajiya cikin mamaki. Har sau nawa za ta fa a mata bata son Jaheed amma Hajiya ba za ta fahimci yaren ba kenan "Mimin ta amimce da shi ne yanzu Hajiya? Mommy ta katse Hajiya da wannan tambayar Sulaiman ma ya ce"Matsalan har shi Jaheed din ba ka gane in da ya dosa ne." Mommy ta ce"To nima shi na gani mai so ai shi ya ke nema ko Hajiya? Khadija da ta fi kama da Mommy ta gyara zama tana fa in "Mommy ni ko sai na ga Jaheed ba laifi, Mimi ce matsalan kusan halinta kowa sai ta ce ba ta so kuma in aka biye mata sai dai kila ta mutu ba ta yi aure ba a take taken ta wlh." Khadija ta fa aa lokaci aya ta juya tana mai kallon Mimi ta ke ta hararanta. Sulaiman ya kalleta ya na yar dariya kafin ya ce"Sisto taho nan naji me ya sa baki son Jaheed din? Mimi ta tura baki kafin ta mike sanye ta ke da doguwar riga mai santsi ta na da bu ewa ta kasanta sannan ba ta kama Jiki sosai ba. Har gabansa ta zo ta tsaya ya kama hannunta yana fa in"Me ya sa ba ki ba ma Jaheed dama ba Mimi? Mimi ta yi shuru ba ta yi mgana ba kuka ke son taso mata sai dai ta danne amma taki mgana. Khadija ta ce"Ba ta da wani dalili fa, Saboda tasan ba shi da makusa, haka abokin Dee ya ce yana sonta nan ta wulakantashi ni nasan abin da take yi ma ulafuci wannan yaro shi ke cikin ranta har yau ta kasa cire shi." An so so mata in da ke mata ayi kawai sai ta fashe da kuka har da jiniya, Abi na kwance fa i yake yi" Dr. Kyaleta ku kyaleta Mimin Abi taho nan taho nan wajena." Sa gudu ta haura gadon ta fa a gefensa ta na kuka shi kuma ya saka hannunsa guda aya yana shafa kanta cikin lallashi yake fadin"Ki daina kuka, ki kwantar da hankalinki tunda baki son shi ba wanda zai ce dole sai kin aure shi Ok? Sai ta gya a kai kafin cikin kuka ta ce" Abi ba na son shi, ni wlh ba na son Jaheed" Ta karishe fa aa ta na gunjin kuka kamar wacce aka daketa. Mommy da Hajiya suka kalli juna ba su yi magana ba. Abi ya ago idanuwansa ya na kallonsu kafin ya ce"Kar a ara takura ma Mimi da mganar kowa tunda ta ce ba ta so a kyaleta, shima Hamzan zan kira shi a bar wannan mganar tunda Mimi ba ta so period." Khadija ta bu e baki ta ce" Amma Abi..'" "Na ce tunda Mimi bata so a bar mganar nan, abin da Mimi take so ko bayan raina shi za ku yi mata wanda kuma ta ce ba ta so kar ku ce za ku matsa mata don Allah.." Abi ya katse Khadija, ya na mgana kamar zai saka kuka da sauri Sulaiman ya ce"Abi ba wanda zai takura mata kan abin da ba ta so tunda tace ba ta ra'ayi nima ina goyon bayan a bar mganar." Hajiya ta ce" Ni kaina ba zan ce a yi ma Binta fole ba Kabiru, Yaddiko ce da Hamzan suka matsa da zamanta haka ba aure shekaru talatin ai ba kwana talatin ba ne." Mommy ta yi shuru ba ta yi mgana ba wani abu da ya faru a shekarun baya suna dawo mata, duk abin da ke faruwa da rayuwar Mimi ba kowa ya ata komai ba sai shi. Ba'a maida hannun agogo baya tasan da ana maidawa da tuni Major Kabir ya maida lokacin ya gyara kuskuren da ya tafka a zamanin baya da ya ke ji da duniyar a saman kansa. Mimi jin a bar mganar Jaheed sai ta daina kuka ta tashi ta fice daga ' akin ta koma Bedroom inta na gidan kwanciyarta ta yi ta na sharan kwallah, Jaheed in fa da gaske ba shi da makusambSai dai ita kawai ba ta son shi ne, sannan shagwa e ne ko ita mace albarka ta zauna tana wannan shagwa an Mama boy ne. Jaheed babban yaron Daddy Hamza ne yana Lagoa can ya ke aiki a wani babban kamfanin sarrafa Karafuna. Sannan kuma a America ya yi karatunsa na Engeniaring har na tswon shekara biyar, yana da wayewa har ta yi masa yawa kuma ita a tunaninta ba sonta yake yi ba kawai yana sonta ne saboda tana aikin gidan Tv asan fuskarta a duniya sannan tana da kyau domin ya sha fa a mata shi bazai iya auran macen da bata da kyau ba, shi komai nashi ya na son harka da abu mai kyau Yaddiko ta matsu ta yi aure kamar a saman kanta take zaune shi kuma Daddy saboda Jaheed ne shi ya ke matsa masa tunda ta ki ba shi dama kuma yasan har yanzu bai samu kar uwa. Ba ko da yaushe take aukan wayansa ba sai ta ga dama, a chart kuma sai ya yi mgana da wajen sati sannan ta ke dubawa. Ita fa Namiji kwara aya ta ta a so kuma har abada shi ka ai take so. Tunda Abi ya ce a bar mganar tasan mganar ta mutu. Saboda a baya ne Abi ke girmama ra'ayinsa saman na kowa, amma yanzu zai iya girmama nata ra'ayin sama da na kowa ba na shi ba ma. Saboda yana tuhumar kanshi da komai ya faru da rayuwar Mami shi ne silar hakan. Tana jin shigowar Khadija aakin sai ta yi kamar ta yi barci tana jinta ta kira Anty Madiha a waya tana fa a mata duk abin da ya faru da yadda Abi yace a bar mganar. Abu aya ya fi bata haushi irin in da Khadijan ta ce"Ni fa nasan me ya sa Mimi ta kin sauraran kowa, wannan yaron ta kwallafara rai akansa wanda ba ta san isalinsa ba, tuni ya yi auransa ma ya manta da ita, itama ai ya kamata ta manta da abin da ya faru a baya ta gina wata sabuwar rayuwar." Tana da tabbacin khadija ba ta san menene SO..! Da ace ta ta ana shi ta ji ya ya ra insa yake da ba ta yi wannan mganar ba. Da ace tasan ya ya zafin dafin so ya ke da ta yi mata uzuri, ammh itama ta yi ma lta uzuri saboda wanda take so ba ta sha wahala a kansa ba ta same shi. Shi ya sa ba za ta san zafin dafin ka rasa wanda zuciyarka ta aminta da shi ba, ba ta san ya ya zafi da ra in raba ka da wanda kake so ba. Duk ba ta san wannan zafin da ra in ba so khadija tana bukatar a yi mata uziri ko da uzurin ya kai kimanin sau saba'in ne. Saboda wannan dalilin ya sa har suka koma Gombe ita da Hajiya ba ta kara walwala a gidan ba. Haushi Khadija take ji, itama Khadijan haushinta ta ke ji Sulaiman kuma ranar oahadi suka bi jirgi zuwa Kano shi da matarsa da ayansa. Mimi kuma sai washegarin litini suka bi jirgi ita