Sashe 92
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fuskarsa na shining in ba i Saboda rana sannan ga alamun zufa nan a saman goshin sa daga yanayin sa za ka san a tsume yake, kuma a kallo aya za ka san zai yi gadara da nuna isa, saboda ba shi da fara'a ko ka an a duka hotunan ba ta ga inda ya yi dariya ba, sai dai fuskar nan a kirne kadahan kadahan. Aisha Farida ta mi a ma Lauratu wayar itama ta kalle shi da kyau kafin ta ce" Uhm ganin sa ya fi jin sa." Aisha Farida ta ce" Daman kin san an ce baka en maza akwai fa in rai da nuna isa, daga kuma ganinsa mugun an yarfa mutane ne. Rukky ta kwashe da dariya kafin ta ce" Ina fatan watarana Allah ya ha aku, ai ya zarce tunanin ku wlh,." Aisha Farida ta ce" naga alama kam, to Allah ya ba su zaman lafiya amman za'a ga zama." Rukky na jin ta daganan ba ta kara mgana ba saboda ba ta so ta bu e musu L Labarin duka ne, kamar ta fallasa sirrin auran Mimi ne amman da sai ta fa a musu abunda ya faru a baya da yadda ma sanadin auran ya tabbata yanzu, har su ka sauketa bakin juction in layin su ta hau mashin Su Aisha Farida ba su daina mamakin lamarin ba.har kuma su ka isa ma'aikatan Labarin su ke tattaunawa da Lauratu, sannan suka koma da kayan arzi in da Mimi ta ba su, masu tambayan na su Aiaha tace yana hannun Rukky gobe za ta taho musu da shi, masu tambayar ranar da Mimi za ta dawo aiki Lauratu tace Ranar Monday ta ce za ta dawo in sha Allahu, sai su ka fara murna saboda Mimi, mace ce mai jama'a faram faram in ta ya siya mata soyayyar Mutane da dama a ma'aikatar su, sannan ga shi hannunta a sake ne in dai ta na da shi shikenan, in kuma ta yi albashi wlh kusan rabi a sadaka ya ke tafiya irin yadda take da tasiri a wannan ma'aikatan ya na ba ma kowa mamaki, sannan har ga masoya masu kallon su Mimi na da mutane warai da gaske ko yanzu da aka jima ba'a ganta ba orafi kawai ke zuwa musu na cewa ko dai Mimi ta daina aiki da gidan tibin karamchi ne? Gaskiya suna bukatar ta a dawo da ita wa anda su ka san ta yi aure ba kenan wasu kuma sai suke tunanin kila ta bar aikin gaba aya tunda shu ewar kwanaki sama da goma ba'a ganinta. ****** A cikin kwanaki bakwai in da tarewar Mimi, Mansoor zai zo duk dare ya kwana da safe ya yi tafiyar shi, shima kwanan saboda Kada Inna ta gane ba ya kwana a gidan ne, Sannan ya na cikin hutu shima tunda Couch ya ba shi hutun sati aya, sai dai ya yini a gida ya na hutawa, A satin kuma ya yo oder in injina motsa jiki daga China suka iso a cikin gidan sa ya ware aki guda a ka jera su a ciki, sai zaman gidan bai yi masa zafi ba in ya gaji da kwanciya sai ya tu e ya shiga ya motsa jikin sa domin a watan december mai zuwa suna da Wassani da yawa. Kuma har zuwa yau wata mgana ko kusanci mai tsawo bai ta a shiga tsakanin su ba, sai dai gaisuwa kawai ke shiga tsakanin su, ya kwana a falo ita kuma ta kwanta a bedroom in ta ba ta damu da shi ba, kamar yadda shima bai nuna ya damu da ita ba, ta dai samu sakewa a giden sosai saboda duk zuwan da zai yi sai dai ya ganta akin Inna suna hira sai ya shigo ne sai ta koma akin ta, itama an zo an ha a ma showglass in ta ta jera turarukan ta sannan an zo an ha a mata gas in ta an yi mata Refeling duk dai ba ta ta a girki ba Inna ke ba ta abinci safe da rana da yamma, hatta da gyaran akin ta Walida ko Mariya ke yi mata sai ta so ta ke yi ma wani aiki, ta na waya da iyayenta da sauran an'uwanta musamman Hajiya. Mommy kuma ta koma Abuja tun ranar da suka zo, sai dai su kan yi mgana ta waya da Mimi ita kwanciyar hankalinta yadda ta ga Mimi na cikin farinciki kuma duk sanda suka yi waya sai ta tambaye ta" Kuna nan lafiya dai ko? Ya wajen shi megidan naki? da surukar ki? Sai Mimi ta ce duka suna nan lafiya Mommy sai hankali Mommy ya kara kwanciya daman in su ka yi waya da Hajiya sai ta ce" ki kwantar da Hankalin ki Murja, In sha Allahu Binta na cikin alheri." Mimi ta fi yawan waya da Dr Sulaiman sai Khadi da kan kirata ta yi mata tsiyan ina ba in mijinta, Madiha kuma yar ba ruwanta ne wannan ta na da akida mai zafi, sai in ta kira ta su gaisa shima ba wani tsawaita hira ranar laahadi da ta kirata da daddare bayan sun gaisa ta tambayi yaranta abun da ta fara tambayan ta shi ne" Kin koma aikin ki kuwa? Ko kina zaune kin za i zaman aure? Kai tsaye Mimi ta ce" Sai gobe in sha Allahu, zan koma." Sai Madiha ta ce" Ya fi miki dai, domin kin san burin Abi kenan mu samu ilimin da za mu tsaya da kafafun mu, a take take wannan mijin na ki an renin wayau sai ya iya cewa ba za ki yi aiki ba, na kuma san halin ki wata sakara ce ke, sai ki amince ki zauna ya gur ata miki rayuwa a wannan gidan, ki tsaya ga kafafun ki ki nuna masa You are educated women, kuma da Komai na ki ya ganki kin gne ko? Sai Mimi ta yi mirmishi kawai kafin ta ce'" In sha Allahu." ba ta yi mamakin Madiha ba, sanin halinta yar boko ce ta arshe ita da Mijinta to har ta fi mijinta shegen akidan boko ma gidansu rayuwar turawa a ke gudanwar kowa da ra'ayinsa kuma su na girmama ra'ayin kansu da na ya'yan su. ,Sa anin khadi da ta ke da sau in kai ta sha cema Khadi ta bar wannan walahar koyarwan ta zo ta saka hannun Jari a kanfanin su ya fi mata wannan wahalan ita kuma Khadi sai ta ce koyarwa Hubby in ta ne, ba tana yi ne saboda ace ta na lecturing ba ne ta na yi ne saboda ta na sha'awar abun sa anin Dr Sulaimam da ya fita dabam acikin su, mara hayaniya shi kaf hallayansa na Mommy ne, shi da Mimi Khadi ce ta auko wasu hallayar Abi Madiha kuma photocopy in sa ce har ta fi shi ma tsauri ta wani bangaren. Tun a daran Mimi ta sanar da Inna Meri gobe Monday za ta koma wajen aikin ta , Inna Meri na ta saka albarka da fatan nasara, Bintu na gidan ranar saboda Inna Meri ta kira ta ita ta za ga ya da Mimi makotan su ta gaishe su daga Umarnin Inna sannan su ka ara shiga gidan su Gaje ta ara gaishe su, da ya ke ma suna shigowa in dai kuma su ka shigo gidan sai sun leka Bangaren Inna Meri sun gaisa, a daran ba a gidan Mansoor ya kwana ba Saboda washegari suna da morning training, Shi ya sa ya yi kwanciyar sa a gida Inna kuma Kanta ta ji ya na ciwo sai ta sha mgani ta kwanta da wuri ba ta masaniyar ya shigo gidan ko bai shigo ba, Baba anjuma kuma ya na cikin akin sa ba sani zai yi ba, Mimi dai duk safiyan duniya ta na zuwa ta gaishe su shi da Magajiya., inna Meri ta nuna mata ta ri a zuwa ta na gaishe su duk safiyan duniya. Ia kanta Mimin ba ta san ba'a gidan ya kwana ba sai da asuba da ta fito falo ta ga inda ya ke kwana wayam sannan ta san yau bai zo gidan ba, baki ta ta e kawai ranar ko barci ba ta koma ba sun yi waya da Manaja jiya yau za ta karanta labaran Safe ne, shiyasa ta yi duka shirinta tun da wuri, ita ta dafa ruwan zafi ta sha tea saboda ba za ta so takurama Walida da safiyar nan ba, ko kafin karfe shida rabi na safe ta yi shirin ta cikin Abaya mai ruwan maroon sai ta yi amfani da mayafi ba i mai roba ta yane kanta da shi ta saka takalminta mai tsini baki mai igiya sai jakarta ta zamani, ta yi kyau warai duk da ba ta yi kwalliya ba. Sai da ta gama duka shirinta sannan ta tuna da kiran Aji ta sanar da shi, wayarta ta auka ta kira shi, amman har ta katse bai auka ba wajen kira uku ta yi masa no answer, abun sai ya ata ma ta rai saboda ta na ta cin lokacinta ne, ita daman bai ta a kiran wayarta ba tun bayan auran su, sai dai suna waya da Mu'azzam domin har lambar matarsa ta kar a wajen Bintu ta kirata ta yi mata bangajiyan biki, sannan suna chart da Mu'azzam har su Nasir in sun saka status ta kan yi tagging ta yi mgana su yi ta tsokanar ta da amaryan Aji, har Nasir na zolayanta da cewa har yau ba ta kira su cin girkin Amarya ba shi gogan ne ba ma wanda yasan lokacin da ya ke hawa, Ita dai ta yi masa magana sama da wata hu u bai bu e sakon ta ba ga alamun ya yi ticking biyu nan wato ya shiga amman bai bu e sakon ta ba. Ta yi zaman sama da mintina goma. Bai kira ba ta duba agogon fatan da ke tsitsiyan hannunta na hagu, ta ga bakwai saura kwata da ka an, za ta makara saboda sai ta biya gida ta auki motar ta sai kawai ta auki waya ta kara kiran sa amman still bai auka ba. Kawai sai ta kira wayar Mu'azzam shi dai bugu uku ana