← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 208

Sashe 137

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba shi Mimi kamar sadaka. Ita ta kira Jaheed taa gaya masa abin da ke faruwa ya yi mamaki kwarai.Har Maman na zolayanshi da cewa ila in da rabo Mimi rabon shi ce nan da nan farinciki ya cika zuciyarsa. Kuma Daddy ya ba da umarnin a nemo mota a je a kwaso duka kayan Mimi a kai mata gidan Hajiya, amman ko shi a cikin ranshi ba shi da niyar kashe ma Mimi aure ita kanta a mganganunta fushi ne kawai amman tana son mijinta kuma shima yana sonta amman girman kai ne ya hana shi zama ya fahimci yadda zai iya nuna ma mimin so. Shi ya sa ya za i ya yi amfani da karatun siyasar sa ya gyara auran Mimi sannan ya cire wannan jin kan da fushi daga zuciyar Mansoor ba tare da ya bari ko Mimin ta san ga manufarsa ba. *Janafty* *INZB3003* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke bu ata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Daddy na yi ma Mama maganan kwaso kaya ta kira anwarta Hajiya Turai suka yi maganar ta nema musu mota, Har tana yasa mata abin da ya far u Hajiya Turai ta ce"Haba ni fa daman na sani duk burgan banza ne, yarinyar nan ba za ta iya zama a wannan gidan ba." Mama na ar dariya ta ce"Uhm to ai komai ya are" ita kamar har wani jin da i take yi ita da suka yi mgana da Daddy sai ga shi har Antyn yara sai da ta sanar mata da ga abin da ke faruwa kowa ya ji sai ya ce gaskiya daman wannan auran na Mimi sai a hankali. Jaheed ya fi kowa murna da faruwar haka, Tun bayan auran Mimi yake cikin garari, sai dai kule kulen anmatan zamanin nan da ba ka raba Mazan zamani da shi, bai san Yaddiko ba ta sani ba sai da ya kirata ya gaisheta kawai ya fa a mata saboda ya san tana goyon bayansa ko a baya aiko nan da nan ta ce ba ta sani ba amman anjuma za ta leka gidan Hajiyan ta ga abin da ke faruwa, Lamarin ya daure mata kai, ita fa ba ta son ta ga mace da uruciyarta tana bin akuna in ya zama jiki bshike nan duk in da ta yi aure ba za ta zauna ba. Da daddare ta saka aron makotan su ya kawo ta gidan Hajiya, Ta kuma gasgata abin da Jaheed in ya fa a mata tunda ta ga Mimi a gida sannan da ta yi mganar ba'asi Domin sai ta nuna Kamar ba ta san abin da ke faruwa ba. Nan Hajiya ta yi mata bayani da zuwan Daddy jiya da maganar da ya yanke a kan Mimi in, Yaddiko ta gyara zama lokaci aya ta na fa in" Haba Hajiya me ya sa za ku biye mata? Tun farko sai dai a ka nuna mata ga an'uwanta ta dage sai abin da take so an kuma yi auran nan amman kawai sai ta kamo kafa ta dawo ta ce ta hakura da zaman aure? Haba dai Hajiya ai ya kamata ku ma ku zauna ku yi tunani kar ta maida mi kananun mutane mana" Hajiya ta kalleta kafin ta ce" To yanzu tunda mu ba mu iya ba, ya kike son ayi? Kai tsaye Ta ce" A kira shi mijin nata Yaya ya zauna da shi sai a ji shima ta bakinsa." Hajiya ta gya a kai kafin ta ce"To kuma har yanzu bai zo kuma bai kira waya ba, shi kuma Hamza ya ce ba wanda zai neme shi." Sai Yaddiko ta yi shuru ta kasa mgana Hajiya ta cigaba da fa in" Ba na nufin Auran Binta ya are har ga Allah Yaddiko. Amman mu ba su lokaci mu gani ina ji a jikina ko ba yanzu ba nan gaba ka an za su daidaita in sha Allahu." Yaddiko dai ba ta kara mgana ba saboda ta ga Kamar wannan karon ma Hajiya tan goyon bayan Bintar ne. Kuma ba ta hakura ba da za ta tafi, sai da ta le a har akin Hajiya ta na ce ma Mimi" Binta rayuwar nan ta aure duka fa hakuri a ke yi, ke shaida ce irin hakurin da Murja ta yi da Yaya Allah ya jikansa da ba ta yi ha uri ba,da ba ku ta shi kun ga iyayen ku waje aya ba, kowa ki ka gani a gidan auran shi ya na zaune to karki so ki ji irin ha urin da yake yi a zamantakewarsa, in ka ji na wani sai ka ce naka nafila ne, auran dai kika na ce kina so kuma a ka bi abin da kike so a ka baki shi sai kawai aure ko shekara bai yi ba sai ki dawo gida ki ce ba za ki koma ba? Kar fa saboda kin ga ana bin abin a kike so ki ri a zuwa mana da renin hankali aure ibada ne ba wajen wasa ba." Har Yaddiko ta gama maganarta Kan Mimi na asa ta kasa mgana sai dai Idanuwanta sun tara walla ai ba ta da wani ikon kare kanta yanzu shiyasa ta yi shuru. Yaddiko na fita ta koma ta kwanta tana kuka, Mommy ma da safe ta kira ta tana yi mata fa a akan wannan abin da ta yi har ta na cewa ta shirya ta koma gidan Mijinta, ita kuma ta saka mata kuka cewa ba za ta koma ba ta yi ma Daddy magana kuma shi yace ta zauna. Da Mommyn ta kira Daddy bai saurare ta ba ya ce in ta samu lokaci ta shigo Gombe su tattauna da haka suka rabu da juna, Mommy da kanta ta sanar ma Khadi, ita kuma khadi ta sanar ma da Dr . Sulaiman da Madiha a bakinta suka ji L labarin abin da ya faru tun daga lokacin suke rige rigen kiran wayarta amman ba ta auka ba, Madiha ma ba ta kira ba cewa ta yi daman ta fa a ma Mimin ba abun kunya ba ne in ta dawo gida ta nemi Saki, ita kuma Khadi kanun zencen ta ke so ji. Dr. sulaiman ka ai ta daga kiransa suka yi magana shima dai bakinsu aya da Mommy in ma wani abu take so ta yi mgana a yi mata amman ta bar mganar kashe auranta gwara ta koma zai fi mata alheri. Shima kuka ta saka masa tana fa in ita ba za ta koma ba. Saboda ai shi Ajin ya san tafiyarta kuma da kanshi ya ce ta tafin, kuma har yanzu bai zo kuma bai kirata ba kenan shima ya gaji da auran nata. Jin haka yasa bakin Dr ya mutu amman shima ya ce a cikin ranakun weekend in ya samu lokaci zai zo Gomben. Shima ya kira Daddy sun yi mgana ya an dai yi masa bayanin Mimi za ta koma matu ar Mijinta ya zo biko a ka zauna a ka ji inda suke da araka a yi gyara amman matukar bai tako ba shi ba zai maida masa Mimi ba tunda ba ar sadaka ba ce. Ta nan kuma Dr ya ga gaskiyan Daddy ko ya ya ne a nuna masa Mimin tana da daraja, amman matarka ta biyo dare ta dawo gida amman baka kira ba, sannan ba ka zo ba, sannan ba ma tunanin ko wani abu ya faru da ita bayan fitar ta ba, shima ta wannan bangaren ya ga wawancin mijin na Mimi a haka kuma a fuska kamar mai hankali da Tunani. Ita Hajiya sai fakewa take yi da annensa suna kiran ta wayarta ba ta auka Daddy ya ce annensa dabam shi dabam, ba annensa ke auranta ba shi ya ke auranta kenen bai ma san darajanta ba kenan. Kan kuma maganar kwaso kaya ne domin Maman ta zo a daran ta ce gobe da safe za su je tare da Turai su kwaso kata kayanta da umarnin babanta. Hajiya ba haka ta so ba, ta so a dakata ba ta san vaggawa amman Daddy ya ce sai an kwaso saboda shi ka ai ya bar ma kansa Sanin dalilin shi na cewa a kwaso kayan da gaggawa. Washegari misalin arfe 10:20am na safiya ranar jumma'a Mama ta isa gidan Wanzamai, ita ta fara yo gaba Hajiya Turai za ta zo da mai motan aukan kaya, Inna Meri na ayyukanta a tsakar gida Mama ta shigo ta gane ta sai ta kar e ta hannu bibbiyu ta shigarta da ita har cikin akinta ta saka Walida ta kawo mata ruwa, Inna Meri kunya duk ya kamata a tunanin ta ko Maman ba ta san Mimi ta koma gida ba ne, Tana shirin ce mata ai Bintar na gidan Hajiya sai kawai ta ji Mama tana fa in" Key akin Mimi nake so don Allah." Sai Inna Meri ta kasa magana saboda jikinta ya yi sanyi amman sai ta yi ya e kawai ta tashi sda kanta ta shiga ciki ta auko daman ita da kanta ta rufe akin ta ri e key in a hannunta. saboda jatsari ne barin akin a bu e tunda akwai kayan kudi a ciki. Ba tare da ta tambayi ba'asin abin da Mama za ta yi a akin ba ta damka mata makullayen akunan, Ita kuma har ta amsa ta fita daga akin ba ta ara cewa komai ba, Ta bu e dakin ta shiga ciki Inna Meri ba ta taba tunanin za'a kwashe kayan Binta ba ne duk daman ko yau sai da Magajiya ta zo Kofar akin ta ta tsaya ta na fa in suna bukatar
Chapter 137 · 0% Book details