Sashe 25
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tunda zai kai ta gareji a yi juyen ba in mai ya jima bai kaita an duba ta ba. Shifa ba domin Mu'azzam ya matsa masa ba bashi da ra'ayin siyan mota mashin insa ta ishe sa, farko mashi in da ya siya Baba Danjuma ya ba ma wa, ko wata ba ta yi ba aka tare shi aka karbe mashin in Allah ya sa ba su yi masa rauni ba sun dai dake sa, sai yanzu ya ke tunanin zai ba shi wannan mashin din sai ya siya babba mai kama da mota. Daga anguwarsa ta Tunfere gareji ya je da yake kanukawan sun waye shi yana zuwa suka fara kiran sunansa "Aji Aji.! Shi kuma yana ba su hannu suna gaisawa anan ya ata lokaci har wajen biyar na yamma Nasir ya kara kiransa ya ki auka sai ga Ahmad ya kirasa shi kam daman sun jima ma ba su yi mgana ba. Shi ya sa ya auka sun fara gaisawa kenan Nasir ya kar e wayar yana fa in "Aji ni kake yi ma wulakanci ko? Duk abin ka dai yau a katifarka zan kwana." Bai gama sauraransa ba ya katse wayarsa Nasir dai ba zai taba sauya hali ba. Sai da aka gama duba motar ya ba su ku insu sannan ya baro garejin zuwa gida, ya je ya iske Inna Meri ita ka ai a bangarenta Walida ba ta nan ta tafi islamiya. Ya zauna suna gaisawa ta ce masa yanzu su Mu'azzam suka fita suna ta jiransa. Shuru ya yi bai yi mgana ba, Inna Meri ta je ta kawo masa ruwa da abinci kamar ta san ya na jin yunwa. Shinkafa da wake ne da manja ya na son dahuwar Inna wake ya dame da shinkafa. Yadda ta ga yama cin abincin ne ya sa ta san ya da e bai ci abinci ba. Cikin Tausayin shi ta ce" Baban Inna ka rika cin abinci don Allah, zama da yunwa babu amfani ka tattala lafiyarka tun kafin ta kubce maka." Kai ya gya a mata kafin ya ce'" To inna." Daga haka ya cigaba da cin abincin sa, tana lura da shi ana ta kiran wayarsa yana kashewa. Kuma tana jin Nasir kafin su fita dazu yana in baya aga kiransa, sannan Mu'azzam ya ce"Don Allah Inna ki roki Baban Inna kar ya ce zai ja baya a sha'anin nan na Makama kin san halinsa." Shiyasa yana gama cin abinci ya sha ruwa ta kalle sa kafin ta ce"Su Nasiru sun fita suna ta neman ka, ka kira su kaji in da suke Baban Inna." Ba musu ya ce To Inna ya auko wayarsa ya Kira Mu'azzam sai yace suna kofar gidan su Ahmad. Sai ya ce yana gida su kariso, Bayan sun gama wayar Inna Meri ta kalle shi tana fadin" ka saki jikin ka bikin abokin ka ake yi ba na wani ba, Don Allah ka zama aboki nagari ban san kana zille zille nan." Sai da kalaman Inna su ka bashi dariya sai ya girgiza kai kafin ya ce"Mu'azzam ne ya kawo miki ara ta ko Inna? Inna ta ce" ba ruwa an Inna ni na haife ka ai na san halin ka." Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba Inna Meri ta zauna ta na ta masa nasihanta na kullum ya yi hakuri ya manta baya ya dawo da rayuwarsa kamar ta baya. Jin ta kawai ya ke yi, shi fa bai ga wani Sauyawar da ya yi ba, ya na dai guje ma wasu abubuwan ne saboda gudun tuno da abjn da ya wuce a baya. Kiran wayar Mu'azzam ya wace sa ya mike ya ce bari yaje waje suna jiransa. Yana fita ya gansu gaba aya Makama ne kawai babu Ango kenan, yana fitowa Nasir ya auki dutse ya jefe dashi ya ca e dutsen Ahmad na dariya ya ce"Ka ga Ajin wallon kafa akwai iya kama saiti." Mu'azzam na jikin Motar Mansoor in shi da Ahmad suna dariya. Nasir fa i ya ke yi" yau fa sai mun raba hali ni da kai Aji." Aji ya kallesa kafin ya ce"Nasir ka yi aure ba ka girma ba? Sai yaushe? Ahmad yace" Sai matarsa ta haihu, daman tsohon ciki gareta." Mansoor ya yi mirmishin saman fatar baki bai yi mgana ba, ya isa wajen Ahmad ya bashi hannu suka yi musababa Ahmad ya jinjina hannunsa yana fa Aji an da e ba'a ha u an gaisa ba." Aji ya ce"Wallahi ya rayuwa.? Ya amsa ma sa da Alhamdulillah. Mu'azzam ya mika masa hannu suka gaisa ya tambaye shi ya hanya? Ina su Junior ya ce duk suna gaishe su. Nasir ne ya warce hulan kan Mansoor ya ora bisa kansa Mansoor ya bisa da kallo kafin ya bata rai lokaci aya yana fa in. "Nasir ka rika yin abu cikin Aji don Allah mana." Gaba ayansu suka fashe da dariya, Ahmad da Nasir suka ha a baki wajen fa iin " Da girman Kujeran Aji Allah ya kara lafiya." Mu'azzam nata dariya, shima Ajin sai da ya Murmusa kafin ya mika hannu ya warce hulansa daga kan Nasir yana fa in"Kai yaro ne har yanzu Nasir na kara samun tabbacin tsawon kafan ka ne, ya ru eka ka yi saurin aure." Nan ma suka kara kecewa da dariya Mu'azzan na ta mirmishin jin da ganin an uwansa na hira har da mirmishi. Makama ya tambaya Mu'azzam ya ce ya karbi motarsa ya je ya dawo, suna fa a masa wai akwai kamu a gidan su Amarya kuma ana bukatar ganin Ango da abokansa. Aji ya kallesu a kaikace kafin ya ce"kamar wasu mata sai ku je kuma? Ahmad ya ce"Ni kaina na ce ba za mu je ba." Aji ya ce"Kana da girman ka Ahmad gwara ka kama kanka da harkan yara." Ya fa aa ya na nuna Nasir, Nasir kuma ya ce shi in ba za su je ba zai raka makama, Mu'azzam ma ya ce shi yanzu Tudun wada zai je ya kai wani sako saboda jibi ya ke so ya koma saboda aikinsa. Nasir kuma ya kira Makama ya ce ya shirya zai raka shi su tafi kamun tare da sauran abokan shi. Nan ya barsu ya wuce gida su kuma suna nan kofar gidan suna ta hira har aka kira mangariba. Abun mamaki Mansoor ya saki jiki suna ta hira da Ahmad. Duk dai yawancin hiran ta wallo ce daga nan suka aika cikin gida aka ba su butoci suka yi alwala suka wuce masallaci. Daga nan Mansoor ya uke su a mota zuwa Tudun wada gidan su Hibba ya kai mata sakon da ta ba da, daga nan dakyar ya roki Mansoor ya biya da su Bolari can gidan su mahaifiyar Mu'azzam kakarsa Innayi ta na nan da ranta da ta ga Mansoor sai da ta ce shiyasa ta ga an sha iskar rahama ashe shi ne zai zo. Tunda ya da e rabon shi da zuwa a baya dai duk zuwa shi da kansa zai raka Mu'azzam gidan ya gaida kakaninsa. A gidan suka an jima shi ya sa ba su baro anguwan ba sai da suka yi sallar Isha'i. Daga nan suka koma anguwan Arawa Ahmad ya ce zai auki sako a gida suma sai suka shiga gida suka gaida Baba Danjuma. Magajiya ba ta nan ta je kauyen su wani kawunta ya rasu. Tare da Mariya ta tafi duk yadda Baba Danjuman ya so ta kyaleta tunda akwai makaranta ta ce da ita za ta tafi. Mariyan ma ba ta so hakanan ta shirya suka tafi. Suna akin Inna Meri tare da Baba Danjuma da Innar suna ta hira Walida ta zuba musu tuwon da Inna ta yi da yamman nan suka ci a kwano aya tare da Baban su. Ba su bar gidan ba sai goma lokacin da Ahmad ya kira su ya ce yana jiran su a waje, su daga nan suma wuce gidan Mansoor, a nan ne ma Mansoor ya ga kayan da Mu'azzam ya siya musu Shadda mai ruwan kasa su hu Ahmad ya dinka musu daman shi ya tura ma ku in ya siya musu shaddar. Daman shi ba'a iya masa sai da ya kalli Mu'azzam kafin ya ce" Sai kace wasu yara mu saka anko? Tunaninka ya koma na yara ne Mu'azzam". Shi dai dariya kawai ya yi Ahmad ke fa in. "Haba a baya ai muna inka kaya iri aya Aji ka manta ne" Kai tsaye ya ce"Yanzu mun girma mun zama magidanta kai da matarka da yarka, Mu'azzam da matarsa da ansa Nasir ma haka ga shi Makama zai yi aure ace duk ba ku fita sahun yara kun fara halin manya ba? Ahmad na yar dariya ya ce"Kuma fa hakane to daga wannan shike nan da bikin ka kowa kalan na shi zai saka." Banza ya yi masa kamar bai ji ba suka ha a ido da Mu'azzam suna dariya. Su Nasir ne ba su dawo gidan da wuri ba megidan ya ri a masifa yana fa in"Ku kira su Nasir ku dawo kar na rufe gidana ya zageni, yana magidanci yana yawon dare" Ahmad ya ce"Ba sun je kamun Amarya ba." Aji ya yi aramin tsaki kafin ya ce" kamun amarya ko kamun shirme." Mu'azzam ya kira Nasir a waya ya ce ga su nan a hanya. Sai wajen sha biyu saura suka dawo Mansoor ya yi ta masifa yana cewa da sun kara mintina zai rufe gidansa ne. Nasir na rungume da katuwar jakar kayansa ya shigo yana fadin"Mun ji to megida mun ji to." Ya fa a yana ture Mansoor ya shige falon. Makama tare da wasu maza su uku biyun bai san su ba amman yasan ayan abokin makama ne Nura suna ga gida ga gida ne. Hannu suka bashi dukkansu suka yi masabaha, daman da motar Mu'azzam suka dawo sai da ya fita ya rufe get sannan ya dawo. Allah ya taimaka nepa suka kawo wuta sai fanka ta fara ka aawa. Makama da abokinsa Nura da sauran anwansa suka kwana a falo. Nasir da Ahmad da Mu'azzam da mai gidan suka kwana a akin Mansoor. Dolensa ya bar katifa nan ya kwana a asa saboda yana kwanciya Nasir yazo ya shige tsakiyar su