← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 208

Sashe 139

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

amman ko da ita ba ta yarda ta furta mata wata mgana ba. Ita yanzu wa za ta zauna ta fa a ma tun auran su ko hannunta sai bisa kuskure Aji ya ta a kamawa? Sai maganar ta kara girma sai daga baya ma ta fahinci kamar ba ya sha'awarta ne tunda ba ya sonta amman ko ita ta san tana da sura mai jan hankali maza. Wata zuciyar ta ce" Ba yana kishin ki ba? Sai kuma a zuciyarta ta ce kishin banza da wofi ba shi da amfani a wajenta yanzu. Jin da in ma tana Annual Leave ne, shi ya sa ba ta aikin komai a gida sai kwanciya da tunanin. Tuni ta da e da blooking in duka lambobin yan gidansu Mansoor domin ba ta so ma ta auka a roketa abin da ba za ta iya ba, Ko Rukky ba su yi waya ba ballantana tasan abinda ke faruwa ra bon ta da mgana da ita tun ta na Abuja, kila za ta yi tunanin ba ta dawo ba ne. ita kuma ba ta so ma ta sani saboda surutun Rukky ne ba ta so, daman itama tana daga cikin an adawa da auran. ****** Bangaren Mu'azzam kuma tun da ya sauka garin yake lallashin Inna da ban baki da ro on ta domin Allah ta shirya ta je gidan Hajiya ta ba ma Mimi hakuri ta dawo, haka duka yaran suka ha e mata kai, ita kuma ta yi rantsuwan cewa ba in da za ta je suma kuma duk wanda ya je ba ta aike shi ba. Abin a ya fi bata musu rai ma shi ne a ranar asabar da safe aka fara kwaso kayan Maeesha zuwa akin Mimi ba sanarwa ba komai maza na giftawa, bayan Inna Meri da kanta ta zo ta share akin ta goge. Sannan ta fito da kayan abincin da aka bari a akin ta watsar nan kofar akin Inna Meri sai da Hibba da Walida suka kwashe suka shigo da su akin Innar. Ganin Inna ta cije, domin ita acin ranta aya, yadda shi uban gayyar bai ma san ana yi ba tunda washegarin ranar da ya yi tsiyar bai ara dawowa ba to sai ta ga ko an shiga mganar ba amfani zai iya maimaita abin da ya aikata tunda bai san darajan matar ba, Sannan ita da kanta ta kira Alhaji Kabiru babansa na Bauchi tana gayamasa abin da ke faruwa a tunaninta zai zo garin ya same shi ya yi mishi fa a tunda ita dai daman ya renata ba ya jin mganarta. Amman kawai sai ta ji ya ce"Haka aka yi kenan? Daman ai Gwaggon sa Yalwa ta fa amin baya son yarinyar, kawai ya saketa sai ya zo gidana ya duba mata na aura masa ." Haushi ya kama Inna to ko iyar Babansa ya aura zai iya yi mata abin da ya fika haka in dai wanna mai bakar zuciyar ne. Daga nan ba ta kara neman su ba, Domin ta na da tabbacin suma ya fi arfin su. Mu'azzam tare da su Yaya Amina suka yi shawara, shi yanzu su Nasir yake jira Ahmad ne yace a jira shi zai shigo garin tunda dukkansu sun ji labari, kuma cikinsu duk wamda ya kira Aji baya aukan wayansa su sun ce za su yi masa ne bisa zaman tare da abokantaka bisa Amana, za su je su yi gamgami su samu Mimi su ba ta hakuri, Sai Mu'azzam yace kafin su je, su matan su shirya su je su gani. Ba tare da Inna ta sani ba suka ha u a gidan Bintu domin Hibba cewa ta yi Walida za ta rakata gida ta auko wasu kayan. Inna bqta sani ba suka ha u gaba ayansu Har da Yaya Halima sai gidan Hajiya amman abin da ya ara ba su tsoro Hajiya da kanta ta ce musu Mimi ta kwanta kanta na ciwo kuma ba zai yuyu a tashe ta ba. Zaman kusan awa hu u suka yi tun la'asar anan ma suka yi sallar mangariba amman Mimi ba ta bari sun ganta ba. daga baya dai suka fahimci cewa Ita ce ba ta son su ha Yaya Amina ce ta yi ma Hajiya mganar a yi hakuri abun bai kai haka ba don Allah Mimi ta dawo akinta su suna sonta, Inna ma kunya ce da nauyi suka hana ta zuwa. Amman sai Hajiya ta yi dariya kafin ta ce" Ayya ni kaina zan so hakan, amman kuma mganar ba ta hannuna tana wajen Binta da Babanta ne, abin da duk suka yanke shike nan." Fahimtar da suka yi lamarin ya wuce tunaninsu haka suka dawo gidan Inna jiki ba da i suka iske wani arin abun haushi an'uwan Maeesha sun dawo da ita sun yi kaca kaca da shashen suna ta shewar su, Inna dai ba ta gaya musu ba ne amman Ko darajan gaisuwa ba ta samu ba. Sai da suka dawo ne suka fa a mata abin da ya faru da in da su ka je, Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce"Sun yi min dai dai, ku kuma Allah ya ara sai da na ce kar ku je, wanda ya ata bai san hanyar gyara ba sai ku? Mu'azzam da ya zo ya ji labarin abin da ya faru sai jikinsa ya yi sanyi, yanzu haka Aji ya bar masa gida shi a Camp yake kwana in kuma ya je da niyyar su yi mgana sai ya ce suna da traning haka dai duk ya shanshantar da maganar Mimi, shi kuma Mansoor tunaninsa ya bi Mimi gidansu ya ba ta hakuri kamar ya sauko ne ya yi Arha, a tunaninsa auranta na hannunsa to zai tsaya ya ga iya gudun ruwanta shi bai ce ta tafi ba, ita ce ta za i tafiya shi kuma ya goya ma za inta baya, kuma ba ya son kowa ya shiga maganar kotun da ta ce za ta kaisa ya ke jira, ayan tunaninsa nasa kuma na gayamasa Mimi na son shi ba za ta iya rayuwa ba shi ba, tabbas duk in da ta je ma za ta dawo ko labarin an kwashe kaya bai samu ba balle ya dawo cikin hayyacinsa ya fahimci shirmen da ya tafka yana nan yana shirme da tunanin banza.. Ahamad ya shigo garin. A kuma daran suka ka ha u su hu u zuwa gidan su Mimi, suma in dai Hajiyar kawai suka samu gani, a cewarta Mimi ba ta jin da i ta kwanta alhalin tana nan tunda Hajiya ta ce mata abokan Mansoor ne da aninsa ta ro i Hajiya da ta ce ba ta garin ta tafi Abuja ita kuma Hajiyan ta ce ba za ta yi arya ba. Sai da Mimin ta marairace tana fa in" Don Allah Hajiya ki taimaka min, ko na je mun ga juna ba zan yi musu abin da suke so ba." Dole Hajiya ta fito ta sake aryan Mimi ba ta jin da i ta kwanta, Suma sun ta rokon Hajiya suma kuma ta ce magana na hannun Mimi da babanta. Jin haka ya sa suka ce bari su karisa gidan tsohon Sanatan su gan shi, daga gidan Hajiya can suka nufa sun kuma ci sa'an yana na gidan nan da nan aka yi musu iso zuwa falon da yake ganawa da ba in sa. Shima dai bayan sun gama gaisawa, Nasir ne ke rattaba hawabin ban hakuri Alhaji Hamza ya gama karantarsu duka da jinsu sannan ya gyara zama yana fa in" To duk na ji bayanan ku, abin da nake son sani shi Mansoor in ne ya aiko ku, ko kuma kune ku ka aiko kan ku? Daga yanayin yadda suke magana ya sa ya fahimci ba shi ya turo su ba. Sai kawai ya yi wata yar dariya kafin ya ce"Me ya hana shi zuwa da kansa ya yi bikon matarsa? mu'azzam ke fa in saboda baya gari sun tafi buga wasa. Sai kawai Daddy ya ce"Shike nan kun gama naku bangaren a matsayin ku na abokan sa na amana kuma an gode muku, abin da nake so daku shi ne ku cire bakin ku a wannan maganar shi dai shi ne mijin Mimi in har kuma yana sonta zai zo ya zauna a gabana kamar yadda kuma kuka zo kuka zauna a gaba na.". Sun san gaskiya Daddy ya fa a shi ya sa su ka kasa masa musu hakanan jiki ba wari su lka yi masa sallama su ka fito daga gidan a hanya Nasir nata fa a yana fa in" Wallahi ni na cire hannuna kuma abin da Baban Mimi ya fa a mana gaskiya ne, akwai bangaren da mu ba mu isa mu gyara masa ba sai in har ya gyara da kansa." Ahmad ya ce" Wannan gaskiya ne, shima zuwa yanzu yakamata Aji ya san ya girma ya daina wannan taurin kai." Makama kuma ya kar e da fa in" To wai ba ya son ta ne? In bai son ta ya sake ta kawai kowa ya huta tun da shi girman kansa da jin kansa ya sa har yau bai gane annabi ya fa u ba." Suna tafe ne a motar Mu'azzam, suna wannan mganar shi dai Mu'azzam ya ma kasa mgana Ahmad ya ba da shawaran duk in da Aji ya k a neme shi cikin dare su gayamasa halin da ake ciki. Mu'azzam ya ce yana Camp in su nan da nan suka juya mota zuwa cikin gari. Aji na cikin akinsa aka sanar da shi yana da ba i ya auka Mu'azzam ne sai da ya fito kawai ya ga su Nasir bai yi mamakin ganinsu ba, Sanin halin da ake ciki. Waje ya samar musu suka zauna saman wasu fararen kujeru Da Ahmad ka ai suka gaisa Nasir ya fara masa masifan ashe bai ji shawarwarin da ya basa ba. Kai tsaye Aji ya ce"Naji mana, amman sai zuwa gaba zan yi amfani da su" Cikin mamaki ya ce"Saboda mene ba yanzu ba? Aji kuma ba tare da tunanin komai ba ya ce" To ba ka ga Mimin ba ta nan ba ne? Ka bari sai ta gaji da yajin da ta yi ta dawo tukunna."
Chapter 139 · 0% Book details