← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 208

Sashe 26

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi da Mu'azzam yana fa "Ni fa na saba da katifan matata ba zan iya kwanan asa ba." Mansoor ya yi ta tsaki ya na fa in" Nasir sam ba ka da Aji." Ya na dariya ya ce"Na ji Aji mai Aji ba." Karshe kasa ya kwana shi da Ahmad da Asuba shi ya ta da su suka yi alwala zuwa masallaci daurin auren na safe ne misalin sha aya ne. Shi duk haushin su yake ji wannan abun fa sai ya yi kamceceniya da abin da mata suke yi. Ko a baya da yake cikin su ba haka halinshi yake ba yana komai da class ne shi ya sa ma a nan ya fara samun ssalin sunansa na *AJI* ****** *SATURDAY, 28 APRIL 2022* 8:50PM. A cikin anguwan Dubai Quaters Usman makama ya kama gidansa mai kyau anan aka saka Amarya. Tun 7:30pm na yamma aka kawo Amarya gidanta saboda yanayin tsaro, daga nan Amarya da gayyarta za su wuce wajen dinner da abokan Ango suka ha a. Acikin motocin da suka kwaso Amarya da tawagarta har da motar Aji amman ba shi ya ja motar ba Ahmad ne domin shi ya ce ba zai je ba, Nasir ya ce ya ara masa ya ce bazai ba shi ba sai da ya ba ma Ahmad aro. Nasir in yana da mota saida ita ya yi daga baya, ana aura aure Aji ya zille musu ko hotunan da aka je gidan Amarya aka yi bai je ba gida ya koma ya kwanta ya juta abun sa. Sun je dai Reception suka ci abinci daga nan ya hau mashin ya koma gida tunda daman key in motarsa na wajen Ahmad. Dinner dai sun ce ko ya so ko bai so ba sai ya je, ga shi ya yi musu tsiya bai sanya kalan kayansu ba wani farin yadi ya saka mai shara shara. Wai shi ba yaro ba ne ko mace da zai saka anko. Hakanan suka kyale shi, ya saka nashi dabam a wajen aurin auran ma dakyar ya bari suka yi hoto cewa ya yi wai hoto na yara ne, komai sai ya ce ba aji aikin yara ne. Sun je gidan su Amarya sun sha hotuna, Mu'azzam ya so ya ga yayar Amaryan da Nasir ya ba su labarin ta kankame komai a sha'anin bikin, sai Makama ya ce Bibi ta ce Anty Baby ta je kar inki ita da kawarta Anty Mimi. Kuma har suka gama hotuna su ka tafi ba su dawo ba, suna tafiya sai ga su sun dawo tella ne ya yi musu tsiya. Mimi sai masifa ta ke yi tana cewa "Rukky ke kika ja mana da kin bari na kai ma tela na da tuni ya in ka mana." Rukky ta ce"Ina na san haka Habu zai yi mana ,ai ya ci taliyan karshe." Ko makeup ba su samu yi ba mazan ma'aikansu daga karamchi Talabijin da suka zo musu aurin aure ma ba su ha u ba sai dai suka yi ma Rukky fatan alheri ta waya. Matan ne ka ai suka samu tunda su sun jira su, saboda bakin ne yasa ba su samu zuwa kwalliya ba Rukky ta ce su bari anjuma su yi na dinner. Tun Safe Mimi ta baro gida sai da za'a kai Amarya ta auki Rukky a motar ta suka koma gida ta auki jaka da takalmin da za ta yi amfani dashi tare da an kunne da sarka suka tafi wajen kwalliya daga can za su wuce dinner. Hajiya ta ga yadda Mimi ta yi kyau cikin Atamfar yinin biki saboda ajikin Atamfar akwai ja, a cikin ranta addu'a take yi mata Allah ya ha ata da wanda zai sauya mata rayuwa a daren nan. Baaba Uwani kuwa har hqraban gidan ta raka su tana fa in" Binta Allah ya tsare ya sa a dawo lafiya, Rukkaya Allah yasa a watse taro lafiya." Suka amsa mata da Amin, sun je shagon kwalliyan daman sun yi booking, Rukky aka fa ra yi mawa.Wacce za ta yi ma Amarya gida suka tura ta. Sai kira Bibi take yi ta na fa in an gama mata kwalliya ta shirya suna jiran angwaye ne yanzu za su tafi can in da za'ayi Dinner Da za su jira sune, Mimi ta ga yanzu ma aka fara mata nata kwalliyar sai ta ce kawai su tafi in sun gama sai su zo daga baya. Haka aka yi Amarya Bibi da tawagan awayenta da an'uwa suka yi gaba su Nasir suka zo da motoci suka kwashe su. Sai wani Hall ha e mai kyau wanda, ya ke tashe a garin Gombe wajen yin bukukuwa. Ko da suka je an gama tsara komai daman kuma sai da Ango ya jira zuwan Amarya sannan tare da awaye da abokan ango suka shiga wajen. Wajejen goma na dare aka fara gudanar da Dinner in Amarya ta yi shigan Blue ne shima Angon kalar shaddar jikinsa kenan. awaye kuma Less in su mai ruwan ash ne da zanen pick, sun yi inkin fitted gown gabadaya sai suka yi amfani da head pick. Makama ya tambayi Bibi da cewa shi fa yau kwata kwata bai ga Anty Rukky ba Bibi na danna wayarta ta ce"Suna wajen kwalliya ita da Anty Mimi su nake kira ma yanzu." Makama ya ya fito Ahamd da hannu yana fa in " Nima wani abokin mu muke jira, bai zo har yanzu." Bibi ta kalle shi kafin ta ce" Wai wannan wallon da kake ba ni labarinsa,? Sai ya gya a mata kai dai dai karisowan Ahmad yana fa in" Ango ya aka yi ne? Makama ya duba agogon fatan hannun shi yana fadin" Aji ba zai zo ba ko? Ahmad ya ce" Mu'azzam ya je ya auko sa, na kirasa ya ce suna hanya." Makama ya sauke Nunfashi kafin ya ce" Allah ya orani akan sa kenan ya ga dama zai zo." Ahmad na dariya ya ce"Gaskiya ka ci babbar sa'a." Ita Bibi rabin hankalinta na kan wayanta sai ji suka yi tana fa in"Anty Mimi ku yi sauri an fara fa tun azu" Sai da ta gama wayar ne angonta ya ga duk ta bata rai sai ya ramkwafa ya na lallashinta. Aji da Mu'azzam sun shigo hall in Sha aya dai dai na dare. Aji na sanye da wata anyan shadda mai Ruwan asa shi ya na son abu mai ruwan asa da bakin abu da kuma fari. Hulan kansa dara ce baka, gefe da gefe gashinsa kansa da ya tara ya samu wajen zama a gefe da gefen hulan kansa, kafarsa kuma ba in takalmi mai rufi na gata mai kyau agogon hannunsa ma ba i ne na fata. Suna shigowa Nasir ya je ya yi ma Mc ra a sai hall ya kaure da muryan Mc da ya ratsa ya shiga kunnuwan mutane da fa "Kai jama'a ashe dai yau kila sai na tafi gida da kujeran hajji, bikin na masu asa ne yanzu na ke samun ,labarin Aji jiharmu Captain in kwallon kafa na kungiyar Gombe United matashi nan mai tashe MANSOOR AJI aminin Ango ne kuma ya shigo wannan Katafaren akin taro domin taya wannan Ango mai kunya da Amaryarsa mai kyau murnan zamowa ma'aurata kai jama'a don Allah a yi tafi masu garin ne suka shigo." Sai tafi taf raf! Sannan kallo tuni ya koma wajen Aji da Mu'azzaam shi yasan suna shirya wani abu tunda suka matsa masa sai ya zo, Mu'azzam ya rakasa har wajen zaman su shi da Ahmad da Nasir dai dai Mc na kara fa in" kai jama'a yau dai gani ga Aji matashin da kaf garin gombe ba wanda ya kaisa iya taka leda ni a nuna min Aji in kai gaisuwa nima ina cikin masoyansa" Nasir ya nuna Aji Mc ya zo ya duka ya kwashi gaisuwa yana fa in " Gari naku asa ma naku sannu da zuwa aiwa kuma wallah ya ci sunan shi akwai Aji ga shi nan ya bayyana kansa." Hall ya auki Ihu, yan mata sai waige suke suna kallon shi ,Aji ya yi tsam ko dariya bai yi ba ya na kallon Nasir ga shi duk kallo ya koma kanshi. Bibi na hightable ita da Angonta ta kalle shi tana fa in" Wanne ne abokin naka an kwallon? Sai ya gya a mata kai lokaci aya yana Fa in"Mansoor Aji ba." Sai ta jinjina kai kafin tace"Ya ci sunan shi Aji domin tunda ya shigo wajen bai yi dariya ba." Dariya ya yi mata kafin ya ce"Haka yake shi" Mc dai ya nace sai zuba kirari yake yi karshe dai mu'azzam aka bari da yi ma Mc likin yan dubi i yake yi" Allahu Akbar an ce anin Aji ne da wannan ban girman, ni fa yau na zo bikin masu jihar da kansu." Aji duk ya ji ya takura saboda aran Speeker sun kusa kashe masa dodon kunne, sai kawai ya kar in key motar Mu'azzam lokacin ana kokarin fara ciye ciye, ya mike yana fa in "Zan je gida, hayaniya ya yi yawa a nan." Kafin ma su samu zarafin mgana ya kama hanyar fita daga hall Daidai Rukky sun sawo kai ciki ita ce a gaba ta sha kwalliya ta juya baya ta na yi ma Mimi mgana ba ta ga Aji ba. Shi kuma daman yana da tafiya Sassarfa da gaf gaf sai ya yi okarin kauce mata bai san da wata a bayanta ba yana kauce mata sai ya saka kanshi da niyar fita daga wajen sa ji ya yi wani abu kamar mai nauyi ya daki Kirjinsa. amshin turarenta mai sanyaya zuciya ya fara yi ma hancinsa maraba Tsayawa ya yi cak ya na tunanin abin da Ya tokare shi haka, ita ma Rukky sai ta juyo jin shuru sai ta hangi bayan wani dogon mutum ba i da sauri ta dawo daga baya ta na fa in"Mimi are u ok? Ta fa a ta na kallon Mimi dake faman sosa goshinta. Ashe kanta ne ya bugi kirjinsa, tana faman gyara hannun doguwar rigarta tunda mai wani zalo zalon igiya ya yi musu ayan kuma jakarta ne da wayarta. ago ta na kallon Rukky kafin ta ce"Am fine Rukky Allah yasa ban fa i
Chapter 26 · 0% Book details