← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 208

Sashe 14

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafin labarai ya kai ma masu kallo ko masu saurare. Kuma abuin da mutane wasu ba su sani ba, labaran da ake karanta su a gidan talabijin live ne, ko da an mai maitashi to sake karan tashi aka yi ba recording ba ne. Sannan broadcaster zai iya zama reporter, amma ba kowani reporter ke iya zama Broadcaster ba, kamar yadda Salim Bunza ya kasance a gidan talabijin na karamchi Reporter ne, sannan kuma shi in Broadcaster ne. Mimi ce ka ai ce ta kasance Broadcaster ka ai kuma a tsarin gidan talabijin in su biyu ne Broadcaster Kowani na karanta oabarai sau hakwai a sati tunda kwanaki bakwai sai tsarin ya kasance kowa ya na yin adadin rabin kwanakin da zai kasance a sati. Tun da safe da yammah ne, su ma suna shan wahala kwarai tunda suna da tsare tsare kafin ma a fara aukan labaran live a haska ma mai kallo. A kwai bukatar camera man tare da masu makeup tunda abu ne da duniya zata ri a kallo a matsayin majigin gani da ido akwai bukatar gyara ga mai karanta labaran. A can baya kafin Mimi ta fara aiki da su wata Cindera ce ta yi aiki da su yar Lagos ce, komawa ta yi garin su ya sa ta saki aiki da Karamchi a tsarin su, suke ba da kayan sawa in da zaka karanta labarai amma zuwan Mimi ta ruguza wannan tsarin ta ce ita da kayanta zata rika amfani tunda kuma yar ma su da shi ne daga ganinta kasan ba tsiya a jikinta kuma ta na da kyau ga iya aukan wakan da kwalliya sai suka amince da tsarinta. Abu aya ake yi mata kafin a fara aukan live shine makeup man ya gyara mata fuskarta ya an kara mata hoda shikenan. Duk da ba ta da e da fara aiki da su ba ta zama tauraruwa a gidan talabijin Karamchi saboda fuskar Mimi, ta kasance mace mai fara'a da farinjini manyan mutane sun sha kawo ziyara suna mai ya ba mata. Sannan ga za in murya ga turanci da ya zauna a bakinta, wanda in ta juya harshe sai ka rantse bata ta a jin yaren hausa ba. Daga office in editor ta fito zuwa mazauninta in da aramin oaptop in ta ya ke da sauran tarkacenta ta ja Kujera ta zauna ita ka ai ce a bangaren sai daga nesa kuma sauran reporters insu ne ke nuna ma an inten wasu abubuwan. Salim Bunza sai dare ya ke da karanta labarai bai riga ya shigo ba tukunnah. Sanye ta ke da doguwar rigar atamfa mai adon zanen golding a jikinta ta sanya mayafinta mai raga raga a saman wuyanta da ya ji sarka mai kyau da yarari, hannunta sanye da zabbunanta na zinare guda biyu kafarta sanye cikin wani bakin Booth in takalmi kalan na mata. Saukakkiyar kwaliya ce a saman fuskarta amma kallo aaya zaka yi mata kasan ko ba ta yi kwalliya ba ita in mai kyau ce. Ta zauna kenan wata matashiya daga cikin an inten ta zo kusa da ita cikin girmamawa lokaci aya tana fa "Barka da aiki Anty Mimi." Ta juyo Cikin fara'a kafin ta ce"Yauwa Safina kina bukatar wani abu ne? Safina ta karisa kusa da ita tana nuna mata takardan hannunta lokaci aya tana fad n"kan wannan ne, ina bukatar karin bayani." Cikin kwarwaarta kan abin da ta karanta ta fara mata bayani har sai da ta gamsu. Cikin jin da i ta ce"Na gode Sosai Anty Mimi" Gya mata kai ta yi cikin irin mirmishinta kafin ta ce"Kar dki damu aikina ne." Cikin jin da Safina ta wuce wajen an'uwanta kamar daman ita su ke jira sai aka zagayeta ta fara kora musu bayanin da Mmi ta kora mata yanzu. Ta na kallonsu a cikin ranta tana jin wani iri, dama ita ce dama dama ace zata iya maida hannun agogo baya. Su in ta san ba su da wata matsala a rayuwarsu ba kamar ita da ciwon dake ckin zuciyata yake taso mata ookaci bayan lokaci ya hanata sukuni ba. Ajiyar zuciya ta sauke lokaci tana bu e jakarta da ke kan desk in dake gabanta, ta dauko wayarta ta na latsa hasken wayar sai ta ga Missed call har guda uku da sauri ta ja ta duba, sai ta ga Mommy ce ta kirata bata gani ba. Da sauri ta yi kokarin nemanta sai ga kiran Mommy ya shigo kamar yadda ta yi mata saving acikin wayar. Da Sauri ta aga kiran cikin fara'a kafin ta ce" Barrister Murjanatu Soron inki" Mommy daga can bangaren Ta ce. "Na'am, Fatima kabir Dabo." Sai Mimi ta saki dariya kafin ta ce"Mommy mun ta shi lafiya? ya Abi ya tashi? Annuri na bayyana a saman fuskarta Ita fa Mommy yar ba ruwanta ne.Sunan kowa da sunan uban shi take yi masa saving a wayarta har Korafi ta ta a yi mata ita kuma ta ce sunan su ne cikakke ko suna kyamatar sunan ne? Mimi tace a'a Mommy ta ce to ba za ta sauya ma kowa ba, to ba ma su ka ai ba kowa haka ta ke yi masa saving acikin wayarta. "Lafiya kalau muka ta shi, Habibi ne ma tun jiya ya(e ta kiran sunan ki shi ne nace bari na kira ki na fa a miki.." Mimi na dariya ta ce"Allah Sarki Abi Mommy ba shi wayar mu gaisa" Mommy ta mika ma Abi wayar dake kwance a kan gado sai dai ta saka masa filo ta kara masa daga bayansa kansa ya an ta sa sama. Cikin yanayin Muryan sa da ta sha jinya ya ce"Mimin Abi." Da sauri Mimi ta ce"Na'am Abin Mimi ya jikin ka? Abi ya amsa mata da cewa yaji Sauki ya karishe da fa in "Honey tana kula dani sosai na gode mata Allah ya yi mata albarka." Mimi ta amsa da Amin Amin. Sun gaisa cikin fara'a da tambayan aiki ta ce gata ma a wajen aiki. Cikin yanayin muryansa ya ce"Mimi ki yi hakuri da rayuwar nan kin ji ko? Mimi ta amsa da cewa" In sha Allahu Abi Allah ya baka Lafiya." Abi ya amsa mata da Amin kafin ya ce" yaushe za ki zo? Da sauri ta ce"Abi kana son ganina ne? Abi ya gya a mata kai kafin ya ce"Eh ina son ganin ki, ki zo in kin samu dama." Mimi ta amsamai da fa in" In sha Allahu Abi Allah ya kara maka lafiya da tsawon kwana." Ya amsa mata dai dai ookacin da Mommy ta shigo bedroom auke da Mug a hannunta damn tana bashi wayar ta fita zuwa Kitchen. Tana zuwa kusa da shi ta sauke mug in hannunta saman Side drower in gadon dai dai ya na miko mata wayar ta amsa ta na karawa a kunne ookaci aya tana fa " later lokacin karya wan Habibi ne." Mimi ta ce"Mommy sai an juma." Daga haka suka yanke kiran a lokaci Mimi ta bi wayarta da kallo tana an Mirmishi, Abi da Mommy kenan sai ta tuna shekaru a can baya in ran Abi ya aci Murjanatu ya ke kiranta kai tsaye Honey sai lokaci bayan lokaci. Amman yanzu komai ya sauya tsarin rayuwar da komai shi ya sa rayuwar nan duk babu tabbas a cikinta. Yau fari ne gobe kuma baki, in yau ka ji da i gobe kuma akasin sa zaka shiga. Tunani ta shiga yi, tunanin wani irin nema Abi yake yi mata, ko da yaushe tsakaninsu ban hakuri, ita kuma har acikin ranta ba ta ta a rike Abi acikin ranta ba komai ya yi mata shi uba ne kuma duk abinnda ya yi domin ya inganta rayuwarta ne, ba ta a fushi da shi Saboda abijbda ya faru a baya ba, Tana kaunar Abi domin mahaifinta ya wuce sauran mahaifa ya kuma yi mata gatan duniya nan, abin da ya faru wani kaddaren al'amari ne daga Ubangiji da bawa bai isa ya kauce ma faruwarsa ba. Hankalinta ya yi nisa ba ta san Rukky ta shigo ba, sai kawai ji ta yi ta saita dai dai kunnenta ta wala mata kira. "Mimii..!." Firgigit ta yi gabanta na fa uwa domin ta ji tsoro sai ta ci karo Rukky da ta na mata dariya cikin jin haushi Mimi ta ce"Rukky Why? Kin bani tsoro ba ki ji yadda kirjina ke fa uwa ba" Rukky na dariya ta zauna saman desk tana kallon Mimi kafin tace"Tunanin wa kike yi ne da ba ki san shigowa ta ba? Mimi ta lumshe ido kafin ta bu e tana fa in" Me ya faru? Domin daga ganin bakin ki akwai mgana." Rukky ta ce"Maganar dai da muka fara ta waya, ki zo mu tattauna yadda zamu shirya bikin Bibi." Mimi ta kalleta a karkace kafin ta ce"Saboda ita Bibi ba ta da awaye? mu fa yayye ne Baby ina ruwan mu da tsara biki wannan ai sai awayenta." Rukky ta ce" Bibi ta ce mu tsara komai kinsan fa ba ta da wasu kawaye, sai wasu yan makarantar su kuma kinsan yadda zamu tsara al'amarin ba kamar su ba." Mimi ta yi shuru kafin ta kara mgana Rukky ta shagwabe fuska ta na fa in" Haba mana Hajiya Mimi ta." Mirmishi ta yi kafin tace"Yaudara! Zan shigo gidan sai mu yi mgana." Rukky tace" Yauwa ko ke fa? yaushe to za ki shigo ? Ko yau kawai ki jirani na tashi sai mu tafi tare." Mimi ta ta e baki kafin tace"Yau daga nan ina komawa gida zan dauki Hajiya mu je gidan Daddy kinsan Mama ta kwanta asibiti jiya aka sallamo ta sau aya naje na duba ta shi ne yau zan kai Hajiya mu kara dubata." Rukky ta jinjina kai kafin tace"Shike nan Allah ya ba ta lafiya." Nan suka cigaba da hiran su Rukky na fa a mata yadda za su tsara Bikin ya yi kyau sosai. Mimi na dariya tac e"Kina ta tsare tsare Baby, shin angon nan zai fitar da kuda e ne masu yawa ya baki? Rukky tace"Ba ma dolen shi ba, ai na yi mgana da shi yace ba matsala akwai abokansa da suke tunanin aukan nauyin yin dinner, mu dai nan kamu ka ai Ummi
Chapter 14 · 0% Book details