Sashe 56
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jikokinta gaba za su shiga gida da sauri Bintu ta ce"Inna bari kawai mu wuce yamma ta yi" Sai da dariya ta kusa kama walida wato ta san abin a zai biyo baya dole ta gudu in gari banza ne Bintu sai Inna ta yi mata jan ido take tafiya. Ita kanta Inna Merin a sanyaye ta shiga gidan suna shiga da Magajiya suka fara cin karo, Mariya ba ta nan ta na gidan Zuwaira, Inna na yi mata sannu da gida dakyar ta amsa Ita walida ma wucewarta ta yi, ita kanta Innar yau ba tsaya bin Magajiyar kamar uwarta ba ta biyo bayan Walida. Suna shiga akin Walida ta juyo tana fa in"Inna yau mun shige su mun yi ma Baban ki laifi" Inna Meri na rataye hijabinta saman Kofa ta ce"An yi masa laifin sai ya zo ya dake ni." Innar ta fa a a kufule sai Walida ta ja bakinta ta yi shuru ta yi ciki ita kuma Inna sai ta fara zuba ruwa a buta ta shiga ta kama ruwa daman Hajiya ta yi ta yi su tsaya su yi sallar la'asar Inna Meri ta ce sun sai sun isa gida. Ta fito kenan ta fara alwala sai gashi ya shigo da gif gif da in tafiyarsa kafin ma ta ago kanta ta ji maganarsa a masifan ce a saman kanta. "Inna fisabillahi me kuka je yi gidan nan? Tana shafan kai ta ce"Gaisuwar mutuwa." Ta fa a itama kai tsaye, wani abu ne ya ji ya taso mai cikin kokarin danne abun ya ce"Inna har za ki iya zuwa gaisuwar wannan mutumin? Inna ta ce"Eh mana ai musulmi ne an uwana ko? Ta katse shi cikin gajiya da maganarsa zai kara mgana ta aga masa hannu cikin kosawa kafin ta ce"Ka ga na je gaisuwa gidan ma iyanka sai ka dakeni Mansoor haba don Allah, kai kenan shigen bakar zuciya ko a baya da ka ga na daina hul a da Hajiya wlh ba saboda abin da ya faru ba ne, saboda kai ne ba na so in dawo maka da abin da ya wuce ne amman ba domin tsoron fininarka ba." Ta fa a kai tsaye kafin ta juya ta cigaba da wanke kafarta, shi kuma takaici ya hana shi mgana. Kirjinsa ke wani suya yana jin hucinsa na fita ta bakin hancinsa. Sai kawai ya juya yana fa in"Shike nan Inna ai shike nan kawai." Gif Gif kamar wani damisa haka ya juya ya fice Inna ta rakasa da harara Ina dalili da sanyin la'asar zai zo ya tada mata da hankali. Ta kuma san tunda ya fusata ya fita an yi yaji sai ranar da kuma aka huce. Tsab ta idar da alolanta ta shiga aki tana kiran sunan Walida wacce ta leko tana fa in "Ya ta fi ne Inna? aramin tsaki ta ja kafin ta ce" Lokacin sallah ya kure Walida ki fita zuwa alola." Daga haka ta shimfi a sallaya nan tsakar falon ta tada sallah. *Janafty* *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA* Ina iyayem yara kuke kuzo MAIDALILI LACE AND THRIFT takawomuku ingantattun overralls bodysuit da longsleeves domin inganfa lapia dakuma kawara suturun yaranku.kamar yanda kuka sani damuna saida overall kisaqa bebynki ki sinkumeshi bakinki alaikum baruwansa da kamuwa da sanyi.akwai na yammadatan yara kamar yan 3yrs dabasan lulluba da sanyinnan kiyuta rufe yaro yana budewa tokizo kisaya musu overrall kawai dare nayi kizura yaro ciki kisamasa sock da saf wannan shi ake kira blanket huta kiyi kokari ki killace yaranki awannan damunar dan gujewa kamuwarsu da damshi.inanan kano unguwar sharada ina tyra kayana ko ina a nigeria.08033627255 *Page 18* Huci kawai ya ke saki shi ka ai ransa in ya kai dubu ya aci Inna ba ta kyauta masa ba, ba domin Baba anjuma ya ga fitowarsa ba, da anguwan zai bari dole ya yi alwala suka tafi masallaci tare ana idarwa saboda kada ma su Baba Sani su tare shi ya yi saurin tashi yana kara waya a kunne kamar yana waya Baba anjuma yana can yana musabaha da mutane Baba Sani da Baba anlami kuma ganinsa ya sa suke Allah Allah su fito domin su ha u amman ko da suka fito ya bar haraban masallacin ma gaba aya. Baba Sani ya jinjina kai kafin Ya ce anlami wai ka lura yaro nan yana gudun mu ne yanzu? Baba Danlami ya yi kayfci kafin ya ce"Wlh nima na lura, ka bar mutum kawai saboda ku in da yake ba mu ne duk wata sai an taimako in ya taso, ba dole ya ganmu ya yi wucewarsa ba tunda ga yan maula." Baba sani ya yi shuru kafin ya ce"Laifin duk na Yaya anjuma ne, in da amana muma fa muna da hakki akan dukiyar yaron nan tunda ai gidan uban mu aka ri e shi, amma ya tattare komai ko nuna masa matsayin mu ba ya yi yadda ake ba ni labarin ku in yan wallon kafa wlh zai iya kai mu saudiya ma sannan ya siya mana manyan gidaje a garin Abuja da motoci." Baba anlami sai da ya yi wata yar dariya kafin ya ce"Haba! to ai naga shi ma Yaya anjuma bai kai shi Saudiyan ba ma sannan bao sai siya masa mota ba, ya dai gyara gidan ya siya masa mashin itama tunda aka sace ai bai kara siya masa ba, kai ko uwarsa Meri ai ba kai saudiya ba mu kuma a suwa? Karan ka a miya." Baba Sani zai yi mgana kenan sai ga Baba anjuma ya zo wajen sai ya yi shuru hannu ya ba suka yi yi musabaha daman tunda ya gan su yasan da wata mgana. Baba anlami ne ya fara fa "Yaya Danjuma gaskiya ka yi ma yaron nan Mansoor mgana, kamar mu zai gani ya rika wulakantawa? Baba anjuma ya yi saurin cewa"Anya? Ko dai bai gan ku ba ne? Baba Sani ya ce" Zencen kake so, ya fa ganmu amma sai ya auke kai ya yi wucewarsa in ma saboda an abin da yake ba mu ne ya ke ganin kamar ya na yi mana alfarma gwara ka gaya masa gaskiya muma muna da hakki a kansa tunda ya tashi a arkashin mu, duk tsiya dai a gidan Wanzamai ya tashi kuma da gidan zai yi tutiya yau ko saudiya ya kaimu bai biyamu rikon da mu ka yi masa ba ahto." Baba anlami ya arishe da fa in"Ka ji zencen gaskiya." Baba anjuma bai yi mamaki ba sanin halin an uwan nashi kamar wa anda suka ta a tsinana ma Mansoor in wani abu suna ta kumfar baki, baya son nana ta mgana aya ya sa ya ba su hakuri yace zai yi masa mgana. Ashe korafin na su ba aya ba ne nan take Baba anlami ya kalli Yayan na shi yana fa in" Shi kuma Mu'azzamu dai ya manta damu? Ko wancan zuwa ma bai bari mun ha u ba, ina ga ko ya yi sa o iya kai da Meri sa on ke zuwa gare ku, domin ba na jin ko Magajiya tana samun wani abu aciki." Sai alokacin ya bu e musu ido cikin garga i ya ce"Ko ni da na haifesu ban kwanta a gida na dogara da su ba, suma ai suna da na su uzurin rayuwar duk abin da kuka ga ba'a baku ba ba'a kawo ba ne, wani abun ma ba na sanin da shi ake auka a baku ba yaran nan duka biyu daga Mu'azzamu har Mansoor in ba sa yi min abu ba su yi muku ba ko da inki ne na kaya domin aya suke aukan mu, kune da shigen zarge zarge da tsegumin ku da ya sa kuka kasa fahimtar komai ballantana ku godema Allah Bisa ni'imar da ubangiji ya yi muku." Yana gama fa in haka ya yi wucewarsa ya bar su su na raka shi da harara Baba Sani har ya na kwaikwayon maganar Yayan na shi Baba anlami ya ce"Dankari! Mgana fa ya fa a mana wato ba ma gode ma Allah kuma sannan mu zuciyarmu ta mutu sannan har da gorim mu anmu su yi mana in " Baba Sani ya yi tsaki kafin ya ce. "Kyaleshi akwai ranar maida martani." Suna tafe suna ta fa in mganganu.Suna zagin an uwansu uwa aya uba aya da suke tunanin ya samu duniya zai wulakantasu Ahalin duk tarin alherin da sanadin su Mu'azzam suke samu har gobe ba su gani ba an na su kowa na fama da rayuwa wasu ma ga iyalai ba aikin yi, shi fa babban yaron Baba Sani Direba ne yau ya na da mota gobe bai da shi, bai da ma takamammen mai gidan da zai ba shi mota saboda tsabar rigime rigimensa, sauran mazan na shi kuma duk ba wani mai wakwaran Sana'a sai Hayatu ka ai da ya ke sana'ar fenti amman kuma shi kanshi ya sani da iyalansa ko ka an ba shi da zuciyan taimakon iyayayensa da ga shi sai matar shi sai ansa dangin matarsa kawai da ita suke shanawarsu. Sauran matan kuma suna gidajen mazajensu suna ji da kansu, wasu ma suna nema ne, shi ko Baba anlami duk wannan Kumfar bakin da ya ke yi ya na da ya'yan amman ba su iya taimakonsa da komai, tunda Abdurrahim insa ya na sana'ar sai da kayan wuta, sannan arsa Bara'atu tana auran mai ku i sai dai irin makokan nan ne, ita kanta ba ta ci ba ballatana ta kawo gida. Amman ba'a ta a jin suna mgana kan ansu ko samu suka yi ba su ta a nunawa a gani bar su dai ko da yaushe idanuwansu na kan Mu'azzam da Mansoor gani su ke yi kamar suna kawo ma Baba anjuma wani duniyar ne su ba ya ba su, ko kuma suna ware su ba sa ba su ku i tunda su gani suke yi wani duniya Mansoor da Mu'azzam suka tara. ******* Da bacin rai ya isa gidansa, daman kuma a mashin in haya ya zo, motarsa ya kunna ta sai ta fara wani hayaki sai kawai ya barta sai ya kira bakanike mashin in sa kuma ta yi kura sai ya kai wanki kuma yana jin