Sashe 111
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mimi ta ce" Ki yi sauri ki sanar dani matakan da zan bi, nima ina so na ga Aji ya manta komai mun gina rayuwar auran mu kamar na sauran ma'aurata masu son junan su. Wallahi Hibba ina son Aji a tsawon shekarun da suka wuce ban ta kallon wani namiji da sunan so ba, shi na fara so kuma shi nake so har arshen rayuwata." Ta arishe fa a tana ri e hannuwan Hibba lokaci aya ta na cigaba da fa in" Na yi miki alkwarin zan yi duk abunda kika fa amin in sha Allahu." Hibba ta yi mirmishi itama ta ara damke hannun Mimi lokaci tanaa fa in" Ki fara kokarin matse wanman nesan da ya gina a tsakanin ku" Mimi ta zaro ido kafin ta ce" Eh! Kinsan a falo ya ke kwana bai ta a taka kafarsa cikin aki na ba, bai ta a ko ta a hannuna da gangan ba, bai ta a sakin jiki ya kalleni domin ya ya amin ba sai dai in a sace bai ta a ganin na yi kwalliya ya ce na yi kyau ba bai ta a cin abincin da na girka ya ce ya yi da i ba, ta wata hanya zan iya ha e wannan tazaran da ya riga ya gina a tsakanin mu? Da Sauri Hibba ta katse ta da ga in" Kar ki damu da wannan, daman tun farko laifin ki ne, ke kuma kika ja lamarin ya yi tsawo kar ki ara barin ku ara kwana a mabambamta waje, ke macece ki yi amfani da isarmu na mata namijin da ke sonka duk abin da ka gayyace sa zai amsa ko ya doje ki nace masa za ki ga ya kasa yi miki gardama ba, sannan ki koya masa in kin yi kwalliya ki ce sai ya yaba, sannan ki koya masa duk abin da kika ka dafa yaci ya yi santi, ki koya masa ya ji sha'awarki duk da nasan yana ji baya nunawa ne, amman ina so ki koya masa bayyana sha'awarsa a kan ki, sannan ki koya masa ya nuna miki so a gaban kowa da kowa, ki nuna masa cewa ke matarsa ce halas in sa kina da Ikon sanin komai a kanshi, ki li e masa kada ki bari ya yi wani tunani da sukuni sai na ki, sannan ki ha a da addu'a zaman lafiya. Ki ri a yawaita fa in ya Allah ga bawan ka nan Allah ka rage masa zafin zuciya ka saka masa salama da farinciki a cikin zuciyarsa kina yi kina ha awa da matakan mu ina baki da tabbacin in sha Allahu cikin wattanni biyu zai sauya wata ila ba sai ma kin kirani kin bani labari ba, ila ni zan zo na ganin ma idona in sha Allahu." Mimi sai kawai ta fashe da dariya lokaci aya da kuka, kafin ta rumgume Hibba tana fa in" Thank you so much Hibba. Allah ya saka miki da Alheri na gode warai." Hibba na Mirmishi ta ce" Bakomai kar ki damu, ni kamar a'uwata na auke ki." Mimi ta ce itama haka bayan ta ago fuskarta ta share hawayenta Ita kuma Hibba ta ce'" Tun a daran yau zai san Takun ya sauya maza ki auki waya ki kwala masa kira." Mimi na mirmishi ta ce" Ko? Hibba ta ce" warai da gaske." Sai Mimi ta jawo wayarta tana fa in bari na kira shi, Hibba na jin haka ta ce" Bari na je na yo ma Inna sallama kafin nan ma Masoyan sun gaisa da Juna.". Ta fice ta bar Mimi zaune tana faman mirmishi. Kiran har ya katse bai aga ba ta na shirin ara kiran sai ga shi kiran sa ya shigo sai da ta an ja Aji sannan ta aga kiran. "Hello.." "Assalamu Alaikum" Shi kuma ya fa a daga can bangaren, Sai Mimi ta arya tattausan muryarta ta amsa masa sallamarsa kuma da gaske sai da ya ji muryanta ta dake shi. Shuru ya biyo baya shi bai yi magna ba, ita kuma ta na tsara abin da za ta ce. "Kina lafiya? Shi ya katse mata shurun na ta, jin abin da ya ce ne ya sa cikin yar muryan shagwa a ta ce" Ka damu da kasan yadda nake ne? ai baka ta a kirana ba tun da ka tafi ba sai ni yau da na kira ka." arishe fa a kamar mai kuka har tana jan majina. Daga can bangaren Aji ya yi tsam da rai kafin ya ce" To da ban kira ki ba me ya sa ke ba ki kirani kin ji ya nake ba? Da sauri tac e" Ba ga shi yanzu na kira ka ba." Shima kai tsayen ya ce" Ai ba yau na yi tafiyar ba! Ban kira ki ba, ke ma ba ki kirani ba shike nan." Sai kawai ta yi tsai da numfashin ta kafin ta ja numfashin ta saki a cikin kunnensa har baisan lokacin da ya ce" Lafiya? koo ba ki da lafiya ne?. Kai Tsaye ta ce" Eh mana. Ba ni da lafiya" Har ya tsorata da zauri ya mike daga kwancen da yake a akin hotel in da suka sauka tun zuwan su garin. Cikin wani yanayi ya ce" me ke damun ki? Inna ba ta fa amin ba ki da lafiya ba." Mimi ta ja hanci sannan ta ce"Ai rashin lafiyan tawa t ka ce, su suna ganina kamar mai lafiya ce." "Ni kuma?" "Eh, ciwon rashin ganinka ne." "Na kewar ka ne Ajin Mimi." A jere ta sakar masa mganganun da sai da ya jawo filon kusa da shi ya ri e a hannunsa cikin mamakin kalamanta, sai ya ji bakinsa ya yi nauyin da ya kasa mgana. "Yaushe mijina zai dawo, matar sa ta yi tsananin kewar sa." "Hmmmm..." Haka kawai ya ce domin ya rasa abun cewa, Mimin ce yau kuma ta ke jin shagwa a kenan. Baisan bakin sa ya furta" In na dawo gidan me zan miki? Ko kuma me ki ka tanadar min da kika matsu na dawo? Da sauri Mimi ta ce" Kai ko za ka yi min amfanin ko kallon ka in na yi ba sai naji da i ba!. Sannan na tanadar maka farinciki da annushuwa mai orewa in sha Allahu." Gaba aya muryanta ta sakar masa kasalan da yasa murya a sha e ya ce" ka ji ta kamar gaske" Da sauri ta na yar shagwa a ta ce" Wallahi da gaske nake yi, zan shirya maka kyakyawan tarba ranka ya da e na Mimi." Sai da ya yi mirmishi a hankali, wanda ba ya so ta ji sautin sa. Bai san ya furta" Shike nan ina jiran na ga wannan tarban, jibi za mu dawo in sha Allahu." Sai kuma ya koma ya na mamakin kansa, bai gama mamakin ba ya ji Mimi ta saka an Ihun murna kafin ta ce",Eyee na ji da i, Allah ya tsare min kai, Allah ya dawo min da mijina cikin oshin Lafiya." A saman le ensa ya amsa da Amin, "I love you.." Haka ya ji kamar ta fa a, sai ya ce" Ehen me kika ce? Domin sai ya ji kamar daga sama ya ji kalmar daga bakinta. "I love You Aji.." Lumshe ido kawai ya yi kafin ya ce" Sai da safe Mimi." Ba ta samun zarafin ara mgana ba , ta ji ya katse wayarsa kawai sai ta koma tana dariyan kanta. Sai da ta gama wayar da an mintina sannan Hibba ta dawo ganin ta zaune ya sa ta ce" Har an gama wayar masoyan ne? Sai Mimi ta yi mata dariya kawai nan suka zauna suna ara cigaba da hira, Hibba na kara koya mata wasu dubarin zaman aure sun kai har wajen sha biyun dare suna hira sannan su ka kwanta Mu'azzam daman a gidan yayansa yake kwana. Tun asuba suka tashi saboda masu tafiya Mimi ta ha a abun aryawa suka ci sannan su ka mi a hanya, sun rabu da Mimi akan za su ri a yin waya da Juna. Ranar Mimi sai da rana ta tafi wajen aiki amman kafin nan sai da ta ara biyawa gida ta ara duba Hajiyabda Safen ma ta kira Aji bai auka ba sai ta tura masa sa "Good Morning mijin Mimi." Har wajen arfe biyu na rana bai kira ta ba kuma ba amsar sa on ta sai kawai ta ara kiran shi har wajen sau uku bai auka ba.. Sai bayan ta ijiye wayar ta tafi Office in News Manaja ta dawo ta ga ya turo mata sa "Haba mana Mimi, muna meeting ne." Sai da ta yi mirmishi wato haba Mimi ta dame shi, yau ko wajen karanta labarai an shaida tana cikin farinciki. Bayan ta dawo gida ta yi wanka ta yi sallah taci abincin da Walida ta dafa ta ga har lokacin bai kira ta ba sai ta ara kiransa kira aya ya aga lokaci aya yana fa in" Mimi wani hali ki ka koya kuma yanzu? Cikin matse baki ta ce" To ni me na yi kuma? Ai sai ya kasa ce mata komai ita kuma har ara Ta aran murya take yi wajen fa in" Na ce me na yi kuma? "Ba ki yi komai ba, azu kin kirani muna wani taro ne, da wani abu ne? Sai ta rasa abun cewa sai kawai ta ce" Ka yi min tsaraba Ajin Mimi.? Cikin Mamaki ya ce" Me zan siyo miki? auka ki na da komai ba kya bukatar wani abu daga waje na." Da sauri ta ce" Laa ni na ce haka? ni dai ka siyo min tsaraba." "Me kike so? "Abu mai da i da mijina ke so.". Kai tsaye ya ce" To ni dai kinsan ban san abun da in da zai da ce da yar masu ku i kamar ki ba, na fi sanin na mu na an mallan Shehu." Mirmishi ta yi masa mai kayatarwa kafin ta ce" Irin shi nake so, goben za ku taso? "Eh da yamma sai mu iso gida jibi In sha Allahu." "Allah ya dawo min da mijina Lafiya. Sai ya amsa da Amin. Shuru na wani lokaci, shi kuma ba ya so ta