← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 208

Sashe 60

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kowa tsit sai jefa jefa mutane na wucewa, ta kasa fitowa daga cikin motar ta sama da minti sha biyar sai da ta duba agogon fatan dake hannunta ta ga har shidda saura duhu zai fara shiga sai ta yi gundunbala bu e murfin motarta ta fito daman tana sanye da doguwar rigan wani material mai kalan ratsin pick sai ta yi amfani da pick in mayafi mai roba ta yi Rolling da shi fuskarta sanye da wani siririn gilashi na ado kafarta sanye da bakin takalmi mai tudu ka an wanda ya yi maching da bakar karamar jakar dake hannunta. rufe motar ta yi sannan ta riko key in motar a hannunta tare da wayarta hannunta na hagu kuma ta rike jakarta sai ta an ha a da rike gefen rigarta daga kasa tunda ta na an sharan kasa, rasa kofar da zata nufa ta yi yasa ta yi kumdubalan fa awa na gabanta lokaci aya da sallama a bakinta. Gaje ke cikin madafi ta na ka a miya Harira kuma ta na tsakar gida ta na wanki suna Hira ita da Gaje su ka tsinkayi sallama cikin wata murya kamar ta yan gayu. Gaba ayansu suka ago suna kallon Mimi da ta kariso tsakiyar tsakar gidan na su da Mansoor ya simince shi ya yi kyau sai dai ba gyara daga gani yau ma gidan bai ga shara ba. Mamaki ganin ta suke yi shi ya sa har Gaje sai da ta fito daga cikin madafi tana kallon Mimi cikin mamaki. Itama kallon mamaki ta ke yi musu saboda sai taga kamar ta gane su amman ta manta sunayensu. Rankwafawa ta yi cikin ladabi bayan sun amsa mata sallamar ta, ta gaishe su a tare su ka amsa har suna ha a baki. Cikin yanayin maganarta ta ce"Ina neman Inna Meri ne, don Allah ina ne akinta? Saboda ta ga gidan kamar ya sauya mata, Harira ta kalli Gaje itama ta kalleta suma su na mata kallon sani amman sun rasa in da suka santa. Harira ce ta ce"Ai ba nan ne bangaren su Merin ba hala kin jima ba ki zo gidan ba ne ? Ai an fi shekara da raba mana kofa." Mimi ta kalleta sai ta yi mirmishi kafin ta ce"Allah Sarki! Gaskiya na an jima ban zo ba shi yavsa yanayin gidan ya ace min." Gaje ta ce" ofar su tana gaban namu da kin fita za ki ganta tana kallon garun nan, in kika shiga sai ki yi tambaya a nuna miki bangaren Merin." Mimi ta yi musu godiya har ta Juya sai Gaje ta ce"Baiwar Allah.! Sai ta juyo ta na kallonta kai tsaye ta ce"Kamar na sanki wlh, ko ke awar Walida ko Bintu ce? Mimi ta yi mirmishi ba ta yi mamaki ba saboda mutane na yawan ganinta su ce kamar sun santa fuskarta ba oyayiya ba ce ba lalle su iya ganeta a baya ba amman ta na da tabbacin fuskar Mimin karamci suka sani. Ba ta samu zarafin mgana ba sai ga Mariya ta shigo shanya sai ta ga su Gaje cirko cirko ga kuma wata yar gayu a tsaye daman ta ga mota a kofar gida tana ta mamakin motar waye tunda ba ta Yaya Mansoor ba ce. Kafin ma ta yi mgana Harira ta ce"To ai ga ma Mariya nan, ke mariya raka ta wannan bakuwar Inna Meri ce kai ta bangarenta." Mariya ta kura ma Mimi ido kamar za ta yi magana sai ta fasa sai tace toh ta ijiye botikin shanyar ta wuce gaba Mimi ta bi bayanta bayan ta yi ma su Gaje godiya suna fita Harira ta kalli Gaje kafin ta ce"Ni fa ina ji a jikina kamar na san yarinyar nan" Gaje ta yi shuru tana tunani kafin ta ce"Nima wlh kuma ba an'uwan Meri na can garin su ba ne, da kin ji hausan su, amman tabbas na san fuskarta sai dai na rasa a inda na santa." Sai su ka shiga tunanin in da su ka ta a ganin Mimi sun manta da a kwatin talabijin akin Gaje su ke ganinta tunda tana da wani tsohon tibi da iyarta ta sauya nata ta kawo mata tunda a gidan nan ba wanda bai san mai aikin gidan tibin nan ita ce wacce Mansoor ya so a baya babanta Soja ya sa a ka yi ta dukansa ya kusa mutuwa ba. Ita kuma Mimi suna fita kofar gida Mariya na gaba tana binta a baya sai dai tana ta juyowa ta na kallonta Mimi kuma sai ma ta mirmishi ta ke yi ta na mamakin girman Mariya ai ta santa mana ko da ya ke ga Walida ma ta zama yan mata. Sun zo kofar shiga gidan Mariya ta juyo da sauri tana nuna Mimi da yatsa kafin ta ce"Laa ina ganinki a talabijin in Magajiya ke ce ko? Mimi ko? Mimi ta yi mata mirmishi hakoranta farare har su ka bayyana a waje kafin ta ce" Mariya a she za ki gane ni? Mariya ta ji muryan Mimi ta fi ma za sarari sai kawai ta daka tsalle ta shige cikin gida ta bar Mimi na bin bayanta da dariya, ita Mariya da i ta ke ji ta kama sunanta kuma sannan ta ganta a fili ba'a talabijin ba wanda sau tari ma Magajiya na ganin ana nuno ta za ta fara maasifa sai an sauya mata tasha tunda gidan tibin na su babba ne ya na kan babban recodan da ake kama sauran manyan manyan tasoshi. Magajiya na bakin kofar akinta tana tuka tuwo Mariya ta shigo ta na tsalle tana shirin mata mgana ta ga ta wuceta zuwa bangaren Meri ba ta samu sauke numfashi ba ta ji Mimi na gaisheta ta amsa kai tsaye tana kallonta, ita ma sai ta kalleta ta gane ta Magajiya kai lalle rayuwa gidan duk ya sauya mata ganin Mariya ta yi gaba ya sa itama ta bi bayanta cikin irin yanayin takunta. Magajiya ta bi ta da kallon mamaki tana tunanin itama a inda ta san fuskar, Sai abun ya kasa barin ta, ta yi sukuni a gurguje ta gama kwashe tuwo sai ta hau walama Mariya kira sai da ta fito tana zuwa ta kalleta kafin ta ce"Wannan wace ce na ga kun shigo tare? Kusa da ita ta matsa kafin ta ce"Laa ba ki gane ta ba? Ina wannan da ake nunota a talabijin wanda har Walida ta ta a fa amin wai budurwan Yaya Mansoor ce to ita ce fa Magajiya leka waje ki ga wata hada iyar motar da ta zo da ita" "Ke Dilla rufemin baki sakara kawai, ina botiki na.? Mariya na tura baki an katseta ta ce"Ban shanya ba fa" Kamar za ta mareta haka ta kai mata hannu kafin ta ce"Wuce ki je ki shanya ki aukomin botikina." Ba yadda ta iya haka ta wuceta fita amman sai da ta gama tsayawa wajen Motar Mimi da ta koma su gaje su ka turketa da tambayan ko ta san wace ce? Kamar yadda ta gaya ma Magajiya haka ta gaya musu sai Gaje da Harira su ka ha a baki wajen fa in "Haba shiyasa mu ka ga kamar mun santa, ikon Allah to me ta zo yi? Mariya tace ita dai ba ta sani ba sai kawai ta fara Shanyarta ta bar su da rike baki suna faman tunanin me ke shirin faruwa kenan? Bayan fitan Mariya har leke su ka yi waje domin ganin Motar da Mariya ta zuzu ta su ma kan su sun shaida kyanta Har Harira na fadin"To me ya kawo ta? daman suna hulda da su ne har yanzu? Gaje ta ce"Ni dai Mallam ya fa a min ba wannan alaqar daman Merin ce kuma tuni ta daina aiki a gidan shi kan shi Mansoor in ya kama kan shi ke ko karo da Soja wasa ne, sai dai fa kinsan ni dake muka ga sanarwan rasuwan uban nata ko kila shi ne ya ba su lasisin sake dawowa har kuma ta ke zuwa wajen Meri? Harira ta ce"To wa ya sani? Gaba aya sai su ka rasa sukuni kamar yadda Itama Magajiya a na ta bangaren ta saka sukuni ba tunanin da ba ta yi ba. Yau sai ga shi da kanta ta tura Mariya akin Inna Meri saboda ta na so ta san abunda ya ke faruwa a cikin gidan. Ita kanta ta kasa shiga aki sai faman zagaye take yi ta na kasa kunni sai dai ko Minti ashirin Mimi ba ta yi da shiga bangaren Meri ba, sai ga shi ta fito Inna Meri iya kofar akinta ta rakata tana ba ta sakon ta gaida Hajiya Mariya da Walida ne su ka rakota har waje, Walida sai wani ji da Mimi take yi mariya kuma sai faman washe baki take yi. Ta bu e motarta ta shiga sannan ta bu e dirowan motar ta auko ku i ta mika ma walida ta ce su raba Walida ta ce ba za ta amsa ba. Sai ta harare ta kafin ta ce"In Mu'azzam ko Mansoor suka baki kyauta kina maida musu ne?.. Sai ta ji kunya ta kasa magana sai Mimi ta ce to kamar hakane in dai za su baku abu ku kar a ku yi godiya nima wajibi ne ku kar a. Dole Walida ta kar a Ita da Mariya suna ta kwarara mata godiya. Suna wajen har ta tada motar ta yi ribas ta bar anguwan sannan su ka koma cikin gida. Abib da ba su sani ba Aji na daga nesa ya na kallon su a saman mashin in sa daga gidan su Musa Zinder suke yaron dake cikin United in su jiya wajen evening traning ya samu rauni sai aka maida shi gida to da yamman nan ne ya fita ya je ya auki Coach daga gidansa suka je su ka duba shi daganan ya mai da Coach gida shi kuma sai ya gangaro ta anguwar tunda yau wajen kwana uku bai leko ba sun yi kuma waya da Inna akan za ta je biki can bauchi tana son ganinsa. Mamaki da wani irin takaici ya sandaran da shi a inda yake, me wannan yarinyar ta zo yi musu kuma a
Chapter 60 · 0% Book details