← Book details Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 208

Sashe 82

Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wutar nepa sai Rukky ta fito da da Kittle ta saka mata ruwan zafi bayan ta juye mata na wanka ta ara sakawa yana fafasa ta Juye acikin babban fulas in da su ka fito mata da shi, bayan ta shiga wankan ne suka zauna suna fa in irin kirkin Inna Meri a cewar su Mimi za ta ji da in zama da ita, tunda an yi komai cikin girma da arzi i Hatta da Magajiya Inna Meri ta saka an kirata duk da kafin ta zo sai ta ata ma mutane lokaci har ita ta samu turmin zani na uwa, Baba anjuma ya samu shadda gangariya Inna Meri ma ta samu turmin zani super mai kyau sannan duka annin Mansoor da Yayyensa sun samu Kololi masu kyau na tuwo da miya da kofuna sai farantai masu kyau, hadda Hibba matar Mu'azzam hatta ko da su Jummai da Zuwaira har kuma da an su Gaje domin kaf yan gidan Mama tace a lissafasu Hatta da walida sun samu kofina da farantai su Gaje kuma tun iyaye ne sun samu su ma kololi da farantai, Sai suka ba da turarukan jiki da na aki sai sabulan wanka da omo da na wanki suka bai wa Inna Meri da ta ce kayan sun yi yawa, Mama ta ce duka Hajiya ta ce su kawo kayan abinci kuma garan da ke akinta sai su ka raba biyu, rabi na su Inna Meri rabi kumana Mimi ne, sai manyan botikan karfe masu yau na zamani har guda Goma cike da Kayan fulawa sai suka aukar ma Mimi guda uku ita da mijinta sauran kuma suka ce ga shi nan na su ne gaba aya. An yi harkan girma kuma arzi i ya nuna kansa matuka. Duk da suna da tarin arzi in da za su yi abunda ya fi haka amman abunda suka yi in ya yi dai dai da na masu arzi in da suka san Mutumci, bayan fitar su akin Inna Meri ya ru e da hayaniya su Jummai suna ta ranga a gu a, Harira ta rike kayan da aka bata tana fa in" Kai Baban inna dai ya auko auro gidan masu arzi i." Bintu na gefe ta ce" warai kuwa, shima ai da ya ke mai arzi in ne sai ya auko dai dai da shi." Ana ta faman tattaunawa ana bu e botikan da su ka kawo su cincin ne, da donut sai dublan sai alka i sai nakiya, har da su samosa da cake sai waje ya ara kaurewa da gu a, Magajiya fita ta yi ta koma akinta ta rasa gane yanayin ta amman a asan ranta ta na jin ba in ciki bai kamata komai mai yau ya ri a fitowa ta bangaren Meri ba kamata ya yi a fara ganin shi ta bangarenta, ta tuna auran Auwalu gara ma iyayen yarinyar nan ba su kawo mata ba, ya yi hidima biki ba shi da ku i haka ya zo mata abunda an'uwanta suka tara mata ta kwashe ta bashi ya siya abinci ko fallen zani ba su ba ta ba, ballantana a kai ga su yi harkan arzi i irin wannan, sai ta ji a ranta ai ga auran Saddi u ya zama dole ta gaya mishi matar da zai aura ya dace su fitar da ita kunyar mutane abunda ya fi ba anta mata rai sai ganin yadda Harira da Gaje su ka samu waje su ka yi kane kane a wannan sha'anin sai lamarin su ya yi matu ar ba ta mamaki. Mimi ta yi wanka Khadi ta shirya ta cikin wani uban su leshi cikin wanda Daddy ya in ka mata ne mai kalan ja a jikinsa sai ta yi amfani da mayafi ja, da takalmi ja a kafarta, nan da nan su ka rufu kanta suka yi ma ta ruwan turare, daman sun zo ma ta da ruwan turarenka amman gilashin sai daga baya mai ha awa zai zo ya ha a su in suka ce za su zo da shi za su iya fasa shi a bisa hanya, a karo na biyu su ka ara kai Mimi gaban Inna Meri su ka ara damka amanarta da cewa zuwa gobe an'uwa duk za su koma gidajensu tunda an gama biki, Inna Meri nan in ma hakane gobe su yalwa duk za su koma sauran yaran nata ma suna zuwa goben kowacce zata yi shirin komawa gidanta. Nan su ka bar Mimi a akin Inna Meri su kuma suka yi haraman tafiya sai ga Mimi ta ri e Khadi da Rukky tana hawaye ta cikin mayafinta sai Inna Meri da kanta ta taso ta ri e ta lokaci aya tana fa in" Bar su tafi kin ji ko Binta? Na yi miki al warin ba za ki nemi komai ki rasa ba acikin gidan nan, ga ni sannan ga annen ki ina da tabbacin ba za su barki cikin ka aici ba." Sai ta zauna gefen Kujeran da Mimi take zaune ta auki kanta ta ora saman kafa anta ta na lallashinta su Bintu suka saki ihu tare da shewa su kansu su Inna Zainaba sun ji da i a ka rabu cikin godiya suna godiya su yalwa na godiya suma, suna komawa gidan Hajiya tace tawagan Ango ba su da e da fita ba. Da sauri Khadi tace"Har da Angon? Hajiya ta ce" A'a abokan sa ne da aninsa shi sun ce suna da baki ya je sallaman su." Jawahir ta na gida daman ba ta je ba, ta tashi cikinta na ta ciwo, ashe abun ya yi tsanani Ulcer ce sai da mijinta ya je ya siyo magunguma da drif ya saka mata arin ruwa sun dawo sun iske ta kwance domin an ce yini ta yi amai duk ta zabge ta rame. Mommy da Hajiya suna ta tambayan yadda su ka baro Mimi Mama ta ce"Lafiya lau ta na can akin Suru arta mu ka baro ta tare da yan'uwan mijinta, Alhamdulillah ba su da matsala a yadda na lura ina fatan za ta ji da in zama da su musamman mahaifiyar ta sa." Hajiya na mirmishi ta ce"Haba ai Meri uwa ce ga Binta in sha Allahu ba wata matsala." Sai a ka zauna maida mgana Inna Zainaba ke tambayan wai nan ne gidan Mahafin sa? Hajiya ta gyara zama ta na warware mata komai. Sai ta jinjina kai kafin ta ce"Au! Amman dai suna ji da shi daga gani gaskiya." Hajiya tace"To shine Babba, sauran matan biyu suna akunan su, Mijin Meri ya kama shi ya ri e shi kamar a shi yasa ba shi da bambamci da abunda ya haifa." Inna zainaba tace" Ba shakka, shiyasa a ka bashi wannan an akur akin ashe ba shi da gado a gidan ne." Mganarta sai da ya saka su dariya gaba aya har Mommy da ke zaune a gefe sai da ta murmusa. ****** Su Mu'azzam kuwa daga gidan su Mimi anguwar da gidan Mansoor yake suka nufa amman ba su shiga gidan ba sai da suka tsaya a masallacin anguwan suka yi sallar Isha'i bayan sun fito ne suna Hanyar gidan daman dalilin su zuwan za su mayar mishi da motarsa ne, sannan Nasir ya ce sai ya yi mishi tsiya iri iri ya saka su yau sun je gaban surukansa sun yi arya. Tun da da Mu'azzam ya kira shi a waya ya ce Inna ta kira shi ta ce su shirya su je can gidan su Mimi su gaishe su, sai cewa ya yi shi ba zai je ba yanzu haka ma yana Camp in su suna sallaman ba i, da Mu'azzam yace ko su jira shi ne? Kai tsaye yace"Ku jira ni? Ai ni ban ce muku zan je wannan gidan ba, amman in za ku je Bismillah.' Daga haka ya katse wayarsa sai Mu'azzam ya yaleshi ko Inna Meri ba ta san ba da shi aka je ba ya samu ya lallashi Nasir da ya ri a masifar shima ba zai je ba, hakanan suka shirya su ka je gidan ana ta tambayan ina Angon Mimin? Sai ya barsu da aryan suna can suna sallaman akin su da suka buga musu wasa jiya. San da suka iso gidan Mu'azzam na da key in gidan a hannun shi, shima saboda zirga zirgan wannan sha'anin ne Mansoor in ya ba shi key in tunda watarana kada ya zo shi kuma baya gidan motar Aji ka ai suka shiga da ita haraban gidan ta Nasir da ya aro tana waje sai ta Mu'azzam ba su shiga da su ciki ba. Ba su auka ma maigidan na gidan ba sai da su ka ganshi tsaye a kofar shiga falonsa ya le o daga shi sai ba in dogon wando ba riga a jikinsa hannayensa na har e a saman kirjinsa cikin mamaki ya ce" Haka ake yi ehe? Sai kawai ku kama shigo min gida ba tare da kun fa a min ba?" Nasir ya yi aramin tsaki kafin ya ce"Sai ka ce gidan da ka gina shi da Gold" Ban gaje sa ya yi ya shige galon gidan Aji ya bi shi da kallon mamaki Ahmad ne da Makama suka ba shi suka yi musabaha shi kuma Mu'azzam ne aka bari da fa in" Motar ka muka zo ijiyewa, kasan nima gobe zan koma saboda aiki." Ko mgana bai yi ba ya juya ya koma cikin falon anguwan ba su wuta duhu sai fitulin wayoyin su su ka kunma Nasir ya ji ya fara gumi yana zama a kasan Cafet lokaci aya ya na fa in" Gaskiya Aji ka rage son ku i, ka na da dukiyar da za ka iya saka ma anguwan gaba aya Solar ba ma gidan ka ba." Kai tsaye Aji ya ce"Eh ina da shi ban yi ra'ayin sakawan ba ne ko za ka sakamin ne? Nasir ya girgiza kai kafin ya ce" Ni? ia ni ina ara ma mai arfi arfi? Ai wannan albuzurranci ne, kai ai ba mabu aci ba ne Aji ka sani." Yana jinsa bai ce komai ba ya nufi aramin fridge in sa ya auko musu ruwa guda hu u duka ya ijiye ma kowa a gaban shi Nasir ya saki jiki shima ya ga
Chapter 82 · 0% Book details