Sashe 29
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hanyar anguwan Tunfere su Mimi kuma su dauki hanyar da za ta sada su da GRA. Lokacin suka isa har Hajiya ta jima da yin barci Baaba Uwani ta ji bugun kofar falo ta zo ta bu e musu daman Hajiyan ta ce kada ta yi saurin barci Binta ba ta ce za ta kwana acan ba. Sai ko ga su sun dawo, Rukky ta ga abun mamaki Mimi da wannan rigar kamkame ajikinta ta kwaana. Kamar ta rike Mutum haka ta rika ji sai kuma mirmishi ta ke yi kuma ta yi tambayan duniyan nan waye Aji Mimi ba ta ba ta amsa ba. Sai da safe da Hajiya ta shigo akin Mimi ta mike da gudu ta isa gareta tana rike da rigar ta Rumgume Hajiya lokaci daya t na fadin"Hajiya albishirin ki" Hajiya na mirmishi ta ce"Gori fari tas Binta." Mimi na Dariya ta ce"Hajiya jiya na ga mansoor wlh na ganshi, kalli wannan rigar ma ta shi ce fa. Hajiya ta yi shuru cikin mamaki tace"Mansoor dai da na sani na wajen Meri.? Mansoor na Binta" Mimi ta gya a kai farinciki ya cika zciyarta Hajiya ta ce"Ikon Allah ya na nan daman? Ubangiji mai yarda ya so. Masha Allah." Hajiya ta na fa a lokaci aaya ta na zama gefen gadon Mimi sai a lokacin suka samu gaisawa da Rukkaya. Rukky tace"Hajiya wai waye wannan Mansoor da tun jiya da Mimi ta ganshi ta ke farinciki duk da wulakancin da ya yi mata? Hajiya ta yi tsai kafin ta ce"Wulakanci ya yi mata kuma mai sunan yangayu? Nan Rukky ta zauna ta kwashe komai da ya faru jiya ta gaya ma Hajiya ta karishe da fadl in"Masifaffe ne Hajiya wlh bashi mutumci waye shi har da zai saka Mimi kuka? Hajiya ta yi dariyasu na manya kafin ta ce" Ina wanda Yaddiko ta ta yi ma Binta zencensa lokacin da kika rakata wajenta?. Da sauri Rukkaya ta gya kanta ta kosa taji kan zencen. Hajiya ta gyara zama kafin ta ve" Shi ne kike mganar shi yanzu. Saurayin Binta ne tun tana da kuruciya shima ai yaro ne lokacin shi ne kuma har gobe ta kasa mantawa da shi acikin tunaninta kuma ina da tabbacin saboda shi ta kasa aminta da kowani namiji har yau." Mimi ta yi saurin cewa"Ba saboda shi ba ne Hajiya." Hajiya ta katse da cewa",Saboda shi ne mana Binta, kinsan na san ki sarai ko mahaifiyar ki murja ba zata gayamin wacece ke ba." Sai Mimi ta yi shuru sai ta dukar da kanta tana wasa da Botirin dake jikin rigar Aji da ke hannunta. Rukkaya ta gyara zama tana fa in"Hajiya me ya faru ne? Ina so naji labarin wannan Soyayyar? Hajiya ta gyara zama tana fa in "Yau zan faxamiki komai mai sunan yan gayu" Daga nan Hajiya ta fara bata labarin yaddaa Alaqan ta fara ta dalilin Inna Meri da yadda ha uwar Mansoor ta kasance da Mimi, da duk soyayyarsu da yadda abubuwa suka faru da kuma yadda alaaqan ta lalace daga karshe. Hajiya ta karishe da fa in"Tun daga wannan abun da ya faru iyayensa suka yanke alaaqa damu, tun daga lokacin Meri bata kara zuwa wajena ba nima kunya da nauyi sun hanani na taka shima yaron ban kara jin labarinsa ba, Binta saboda haka ta ta fi can wani gari karatu ko an yi hitu ba ta cika zuwa Gombe ba , itama tun da Mahaifinta ya ce ko bayan ransa bai yarda ta auri wannan yaron ba ta nuna dakiya duk iya tsawon wa anan shekarun tana nuna bata damu ba ne amman ni nasan ta damu kuma ya na cikin ranta ba ta manta da shi ba, kamar yadda shima bai manta da ita ba, saboda ya aunaci Binta kuma duk da soyayyar dukkansu suna da yarinta ne alokacin sun dauketa da zafi, saboda shi Binta ta zauna a wajena har ta gama babbar Sakandiri, mahaifinta bai so ba, saboda ni na matsa ya sa ya barta Saboda mahaifiyarsa ko da yaushe yana gidanan sun shaku da juna sosai har ta kai su ga aminta da auran juna ni kuma ban hana ba saboda yaron ya fito da gidan mutumci mahaifiyarsa ta zauna da ni har muka rabu ina kewar kyakyawan hallayan ta har gobe in na tuna abinda Kabiru ya yi ma iyayen yaron nan da shi kanshi sai naji ciwo a raina Rukkaya ba ni da yadda zan yi ne kawai.". Hajiya ta arishe kamar za ta yi kuka Rukky ta cire tagumin da ta yi ta na kallon Mimi da ke kuka hawaye wasu na koran wasu Ajiyar rai ta sauke kafin ta ce"Ikon Allah, Hajiya ai ba laifin Mimi ba ne bai kamata ya yi mata abin da ya yi mata ba jiya." Hajiya tace" Zai iya yi mata ma wanda ya fi shi, tun a lokacin mahaifiyarsa na kuka da shi wajen bakar zuciya da riko, ai daman tun a wajen ya furta ko ita ka ai ta rage a duniya sai dai ta mutu ya mutu amman ba zai ta a auranta ba, kila ya kasa manta abin da ya faru ne shi ya sa ya nuna mata haka kuma Kabiru daman ya yi masa tsakani da Binta haka suka yi yarjejeniya da iyayensa." Rukkaya ta ji hawaye sun cika mata ido cikin tusayin kawarta ta ce"Hajiya Mimi na son wannan mutumin har gobe kuma nima ma yadda saboda shi ta hana kowa wata damar, me zai hana shi Abi a rokesa ya janye kalamansa saboda farincikin Mimi? Hajiya ta yi shuru kafin ta ce" Duk da Kabiru ya yi sanyi saboda rayuwa ta sauya masa amman dai bai taba furta haka ba sai dai ya nuna kar a takura mata, Ai an gama lalata alaqar tunda farko yanzu da wuya kalaman baki su iya gyara ta." Rukkaya ta ce"Da kuma haka Hajiya, ai shima na ji abokansa na fa in yanzu ya samu duniya wallo yake yi fa yana babban kungiya a nan garin Gombe ne." Hajiya tace"Ba shakka ai yana da zuciya ni dai a sanina burinsa ya zama sojane to ina ga bayan faruwan lamarin komai ya sauya." Hajiya ta kalli Mimi dake kuka kafin ta dafa kafa aanta tana fa in" ki kwantar da hankalin ki Binta na sha kuka a gaban Allah ina rokon ya kawo miki abokin rayuwa nagari tunda kika ha u da Mansoor yau ina ji a jikina kaddaran ku ba ta kare ba, ki yi addu'a sai ki ga komai ya tafi da sauki." Sai kawai Mimi ta saki kukanta ta kwantar da kanta saman Cinyar Hajiya tana fadin"Hajiya ta nan anan nake jin wani irin zafi acikin irjina, Ina son Mansoor soyayyarsa ita ce ta cigaba da rike rayuwata Hajiya. Tun da Abi ya raba ni da shi farinciki na ya zama rabi da rabi, ganinsa kuma da na yi yau ya fama min wannan cutar dake cikin zuciyata Hajiya Mansoor na sona har yanzu sai dai ya kasa mantawa da abinda ya faru ne, har yanzu ya na ganin bai cike wannan bambamcin da Abi ya nuna akwai a tsakanina da shi ba shiyasa ya nuna ya manta da ni, in har baya sona me ya sa ya damu saboda rigata ta yage? Hajiya shi ya sakamin wannan da kanshi a jikina." Take fa a ta na gunjin kuka Hajiya na ta faman lallashinta a oye sai da Rukky ta share kwalla. Daman akwai irin wannan soyayyar ta a mutu har yanzu?. arshenta dai tafiya ta yi gida saboda Mimi ta yi kuka har ta gaji kanta ya fara ciwo Hajiya ta saka Baaba Uwani ta hada mata Tea ta sha sai ta sha magani ta kwanta. Tana kwanciya sai barci ta fara barcin kenan Mommy ta kira wayar Mimi sai Hajiya ta kira Baaba Uwani ta aukar mata wayar suka yi mgana Hajiya ba ta oye mavta komai ba na game da Ha uwar Mimi da Mansoor ba, da kuma halin da take ciki Hajiya ta ce"Murja ku yi mgana da Kabiru ya janye kudurinsa a kan Binta da yaron nan matukar yana son cigaba da ganin farincikin arsa, in kuma ya na son ba incikin da ta danne acikin zuciyarta ya yi sanadiyar mutuwarta ai shike nan, amman ki fa a masa ya sani ya tursasa ma Binta ta yi masa biyayya akan tafarkin sunnar ma'aiki ai aure ta ce za ta yi ba karuwanci ba, sannan da talaka da mai ku i duk na Ubangiji ne, yanzu yaron da ya ce ba shi da makoma mai kyau Allah ya aukakasa an ce wallon kafa yake bugawa sannan shi dai wanda ya wulakantan shi ar sa ke so har kwanan gobe, ki sanar dashi ni ma uwace a gare shi kuma ya yi ta sa a umarnina tun a baya kuma na yafe mishi to shima ya yi hakuri ya duba Isharan da Allah ya nuna masa tun a duniya ya Janye kalamansa a kan Binta ya saka baki a nemo wannan yaron da ahalinsa ya ro esa su gafara ya kuma amince Binta ta aure shi shine kawai masalahan da zamu samu sannan shine farincikin Binta a yanzu." Duka mangaganun Hajiya a kunnen Abi tunda a speaker Mommy ta saka wayar ya na kwance ne amman kuka yake yi, ita ma Mommy sai sharan hawaye take yi tana kauda kai ba ta so ya gani. Ita ya kallo ya na tuna a zamanin baya bai ta a ba ta damar magana ba, duk abin da ya yanke ko ta na so ko ba ta so haka za ta bi, kuma gaskiya Hajiya ta fa a shi ya san ya rika take maganar Hajiya a matsayinta na uwa ba ta isa ta ce ya bar abu ya bari ba ya na ganin ya na da kaki sannan ga yadda ya gina rayuwarsa ba wanda ya isa ya rushesa masa. Ya da e da yin nadaman abin da ya aikata ma wannan yaron sai dai kunya da tunanin inda ma zai fara ya kasa mgana. Ya sha kiran Mimi sai ta zo ya kasa magana sai dai ya yi ta lallashinta yana bata Hakuri, ya na so ya samu damar neman gafaran kowa