Sashe 40
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta a makaranta da yaransa ke zuwa kuma Mimi da kanta ta yi ma Hajiya maganar tana so a saka ta a islamiya ita kuma Hajiya ta yi ma Inna Meri mgana, Daga karshe dai Mansoor ya kaita makarantarsu islamiyasu ta mallam ahiru aka jarabata aka ga tana da okari sai aka sanyata a ji hu u ya so a sakata Ajin su Bintu amman ba zai yuyu ba tunda ta girme ta kuma sannan ta fi ta gaba a karatun. Saboda ita Mansoor ya koma makaranta lokacin suna rubuta jarabawar fita daga makaranta Sakandiri ne shi da su Nasir. In bai je makarantar islamiya ba Mu'azzam za'a ja ma kunnen ya Kula da Mimi in aka tashi sai da ya tabbatar da ya rakata har gida. Tun suna Nasir ba su gane ba har suka fahimci wani abu saboda yadda Aji ke kafa kafa da yarinyar masu ku in nan suka fahimci yana sonta Nasir ne ya fara magana, ganin abun na Aji na yin yawa kishin yarinyar yake yi ko miye abun kallo a jikinta Oho. Yana tafe tare tare da ita baya so ta yi ma kowa mgana sai shi in ko ta na yi musu mgana yanzu zai ata rai amman in ita da shi ne sai ka ga yana wani annurin farinciki. Kuma in aka ce wacece ita? Iyaka yace jikar Hajiyar e da Inna ke zuwa mata aiki ce. Amman Sai ayyukansa suka tona shi ita kanta Mimin ba ta iya oye kaunar da take yi masa ko a gaban waye sai ta kira shi" Aji Nah." Kuma in yamman ta yi gidan su Mansoor ke wucewa da ita sai an gama sallar mangariba zai rakata gida suna tafe suna hira. Hajiya kuma hankalinta kwance yadda ta aminta da Meri haka ta aminta da anta Wata rana ma Mimi har kwana ta ke yi a wajen Inna Meri Hajiya ta ce in duhu ya shiga a daina wahalar da su Mu'azzam ta rika kwanciyar ta nan, ita kanta ta fi son haka acikin gida Magajiya ta rika habaicin kwa ayi da wahala tunda suna gani kamar kwa ayi ne yasa Inna Merin da anta ke tafe tarairayan Mimin. Wata rana sun dawo daga islamiya Mimi na tare da su Binta daman Mansoor ya ba ma su Yaya Amina Amanarta da an tashi za su je su nemeta saboda su kamo hanya tare, ta na hango shi daga nesa tare da su Nasir ta walamasa kira sannan kuma ta nufosa yana ganin haka ya yi saurin barin su Nasir ya nufeta yana fa in"Ba na ce ki daina biyo ni cikin maza ba, ba ki ga ke mace ba ce? Sai ta tura baki kafin ta ce"To ni ai ba ina son ganinka ba ne" Sai ya arya wuya kafin ya ce" To tunda kin ganni koma wajen su Yaya Amin a kin ji ko?. Kafa kafa ya rakata har wajensu Amina suna gaba su kuma suna bin su a baya Nasir da Makama suna ta ha a ido suna gulma. Sai da suka zo layinsu, suna tafiya Mimi ta tsaya ta na waigen Mansoor Nasir kuma ya na tafiya bai ganta ba ya taka mata igiyan takalmi shike nan sai ta fa asa goshinta har ya kuje. Ranar Nasir ya ga masifa haka Aji ya dinga masa masifan yaa gani ya tureta ta fa ran Nasir ya aci cikin ufulwa ya ce"Eh ina gani, tunda da gangan ne zan tureta Aji." Mansoor ya ce"Wa ya sani ko da gangan in ne? Nasir ya ce"To wai kana ta wani jijiyan wuya Aji anya anya? Ko dai son yarinyar nan kake yi ne? arfi ya ce"Eh INA SONTA ko za ka hana ni ne? Sai Ahmad da su makama su ka kama baki Mu'azzam daman ya jima da ranfo yayan nasa. Haka dai aka rabu da fa a saboda haushi daga nan ya tasa Mimi zuwa anguwansu ko gidan ma bai bari ta shiga ba. Mu'azzam kuma ya je ya na gayama Inna Meri labarin abin da ya faru. Ta yi dariya kafin ta ce"Shirmen ne kawai irin na shi, ita da ba yar nan garin ba ko yau mahaifinta ya so zai auketa ta koma wajensa." Mu'azzam ya ce"Inna ba fa wasa ba ne Yaya Mansoor na son Anty Mami." Inna Meri baa ta auki abun da wani gaske ba tace"To kawai." Da irin haka da suke auka ne lamarin ya yi nisa ba su sani ba. Saboda Mansoor na gida tunda suka gama sakandiri bai cigaba da makaranta shi a dole sai ya samu makarantar Sojoji, kuma a lokacin makarantar na wahalan samu shi kuma ya dage in ba nan ba bazai yi wata makaranta ba. A zuwa lokacin komai da ya danganci Mimi Aji ke fara sanin kafin kowa har Jinin al'ada da ta fara shi ta samu tana kuka ta gayamasa yana kunshe dariya ya ce ta je ta samu Hajiya ta sanar da iya, sai da ta je ta gayama Hajiya ta zaunar da ita ta yi mata bayani sai ta dawo tana jin kunya. Lokacin da ta gayama Hajiya Aji ta fara gayamawa. Hajiya ta ran washeta akai lokaci aya tana fa in"Me ya sa kika fa a masa? Ni kika tsallake ni Binta?. Ta na tura baki ta ce "Hajiya shi fa zan aura kuma ni to." Sai ta kasa arisawa sai ta bar Hajiya da rike baki daga nan Hajiya tasan Binta da gaske ta ke yi ta na son yaron nan tunda har ta iya furtawa. Kuma har zuwan da Mommy ta yi ganinta sai da Mimi ta ba ta labarin Aji. Mommy ta gaji da jin Labarin Aji ta samu Hajiya tana fa in "Hajiya wai waye wani Aji ne? Tunda na zo Mimi ke yi min hiran sa,? Hajiya ta ce"Mijin da za ta aura ne.," Mommy ta zaro ido ta na kallon Hajiya Mimi kuma sai ta rufe fuska ta tashi ta bar wajen tana dariya. Nan Hajiya ta zaunar da Mommy ta ba ta labarin tun daga farko sannan ta arishe da fa in"To kin ji ba sai ki shirya Binta ta samu miji a gombe." Mommy ba ta wani auka da gaske ba ne har da Inna Meri ta zo gaisheta ta ce a ce ma Mansoor ya zo ya gaishe da surukarsa. Ta fa a cikin Raha saboda ta na kaunar arta kuma abin da yarta take so shi take so. Mansoor ya zo ya gaida Mommy tare su ka zo da Mu'azzam da Nasir makama shi ya fara zuwa jami'a ba ya samun zama sosai. Ahmad kuma babanshi ya kai shi shagon inki. Mommy sai ta ga shi kanshi Mansoor in ai yaro ne sai a ranta ta ce yarinta ne kawai irin na Binta da kuma jaa uwar Jini. Shi kuma Aji in su Nasir suka ce auran Mimi zai yi? Sai yace eh Nasir ya sha fa a masa wata mgana bai ta a tsayawa ya duba mganar ya ga ko za ta yi masa amfani tun a wancan lokacin ba, sai daga baya yake ganin gaskiyan Nasir a wancan Lokaci. Nasir kan cewa Mansoor" Aji gaskiya ka saka kanka a wahala, Yarinyar nan ta fi arfin ka, ba auranta iyayenta za su baka ba, ba ma haka ba kai a yanzu kamata ya yi ka zauna ka yi tunanin makomar rayuwarka ba ka saka kanka a maganar aure da ananun shekarunka ba, kai baka tara ba. ba kuma ka ba wani ajiya ba.". A lokacin da ya fa i haka sai da Mu'azzam ya shiga tsakaninsu shi Aji ya na ganin Nasir ya raina shi ina ruwansa da rayuwarsa. Shi kuma Nasir yana ganin Aji ya shiga inda aren sa bai kai ba ma'ana ya janyo abin da yafi arfinsa. Saboda Aji ya sa Mimi ba ta son zuwa Abuja in su ka samu hutu sai Abi ya kira waya ya ce Daddy ya sakata a jirgi zuwa Abuja haka zata je ta yi hutuntaduk ba da i Mommy dai ke shan labaran Aji har ta gaji, ta ta a ce mata" Mommy Aji ma fa Soja ya ke son zama ki yi ma Abi mgana ya yi masa hanya, so yake yi in aka yi auran mu sai ya tafi ya barni wajen Inna Meri." Daga nan mommy ta fahimci yaron ke kara saka ma Mimi wani tunanin, sai dai alokacin ta yi karaf ta ce mata'" kul na kara jin mgamar auran nan a bakin ki Mimi ga sauran an'uwan ki nan karatu suke yi, ba wacce take mganar aure sai ke in kika bari Abin ku ya ji maganar nan sai ya harbe ki." Mimi na tsoron bindiga sai ta fara rawan jiki tana cewa" Mommy shi fa yake cewa zai aureni nima ai ina son shi." Mommy ta tsawar ta mata da cewa" To ba na son jin haka, in ya ce miki zai aure ki, ki gayamasa ke ba yanzu za ki yi aure ba sai kin girma kin gama karatu." Abin da Mommy ba ta sani ba dukkan abin da ta fa a Mimi na dawowa Gombe ta kwashe komai ta fa a ma Hajiya. Har ta na mata kuka da cewa"Ni hajiya Aji zan aura kuma ya ce in muka yi aure zan yi karatuna." Jikin Hajiya sai ya yi sanyi wato kenan yan zantukan da suke gudana a tsakaninsu kenan? Lalle yara nan da gaske su ke yi. Dakyar ta lallashi Mimi ta yi shuru amman Aji na zuwa ta kwashe komai ta sanar masa. Shi kuma sai ya kalleta yana fa in"Ki gayama Mommy ba zan hana ki karatun ki ba sannan ni nafi son na aure ki kafin ki kara girma, in kika kara girma zaki iya fin arfina" Kuma sannan ya fahimci Mimi ba ta son ya ce zai zama soja. Da ya fara magana sai ta ata rai, ranar dai ya tsareta sai da ta gayamasa dalilinta. Abun ya bashi tsoro tana hawaye ta ce" Abi sai ya yi ta ma mommy tsawa wata rana ma har ya na saka ta kuka, ni ba na son ina ganin bindiga irin ta Abi in muka yi laifi sai ya ce zai harbi kan mutum." Daga nan