Sashe 129
Idan An Ciza Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
masa uzuri.." A fusace ya ce" Ban yi masa ba, ba kuma zan ta a yi masa ba na ce ba zan iya yafe masa ba." Ya fa a lokaci aya yana saka kafa ya daki jikin gadon akin da karfi ji kake Gam! Da sai da ya sa Inna Meri dake kofar akin ita da su Hibba suka fa o falon ba su sani ba. Daga falon Inna cikin tashin hankali take fa in"Baban Inna me ke faruwa ne? Binta kuna ji na? Amman ina ba su ji ba sa gani, Mimi kuma ta ago tana kallon shi ganin yana ta haarbin iska shi ka ai a cikin aki, tsoro ta ke ji kar ya dawo kanta ya yi wallo da ita. Amman ta daure ta kalle shi cikin muryanta da ta disashe saboda kuka ta ce" Me ya sa? In saboda ya hana ka aurena ga shi ka aureni daga baya, saboda na shafe maka abin da ya faru a baya ya sa na amince na aureka bayan duka sharud an da ka saka min, ka kawo ni gidan nan na zauna ban yi mgana ba ka sakamin duka dokokin ka na zauna ban yi ma magana ba, a tsarin kuntatar rayuwa ka kuntatamin duk saboda na goge laifin Abi a wajen ka ban ta a nuna orafi ba, tun da ka aure ni da gangan baka taba rikemin hannu ba duk da haka na hakura, ka kira sunan iyayena ka ci musu mutumci duk da haka ban ta aga ido ba ashe ko Saboda haka ba zai saka su samu yar daraja a zuciyarka ba? Ko saboda haka ba za ka iya yafe masa ba? Shi fa uba ne kuma in ya yi kuskure domin kare ni arsa sai ka tuna da kaima wata rana za ka iya zama uba ka iya aikata kila fiye da abin da Abi ya aikata wajen are ansa, Kuma sannan ka daina ganin laifin Abi a kan abin da ya faru da rayuwarka Kaddaran ubangiji ne, kuma yarda da Kaddara a matsayinka na musulmi warai wajibi nr. Cewar Allah ne ba za ka zama Soja ba, Kaddaran sa ne a lokacin baya ba za mu yi aure ba sai yanzu duk abin da ya faru daga wanchan lokacin har zuwa yau duka Kaddaran Ubangiji ne, in kana biye zuciyarka tana kitsa maka abu mara kyau to kamar dai dai yake da kana jayayya da addaran Ubangiji Mansoor." Ta dakata tana sauke numfashi tana kuma Jan majina saboda kuka. Inna Meri taji kafafunta sun fara rawa saboda tashin hankali. Hibba itama zuciyarta duk ba da i Walida har ta fara kuka. A cikin akin kuma Mimi ba ta ba ma Aji damar magana ba ta mi e tana fa Sai yanzu na fahimci wani abu, me ya sa ka aure ni? Domin ka aukin fansa abin da ya faru? tun da na gama gane cewa KA DAINA SONA, aukan fansa ya sa kake zaune da ni? Kasan ka daina sona me ya sa ka amince ka aureni? me ya sa ba ka barni na cigaba rayuwata bayan ba ka ba? Me ya sa na ce meya sa..? "Ta karishe fa a cikin tsawa mai tafe da gunjin kuka. Kamar zai ji tausayinta tasirin soyayyarta na taso masa, ammh kuma sai dai kash, abin da ya faru shekaru goma baya suka shiga dawomai daki daki yana jin amsar kuwan kalaman mahaifinta a kansa, nan take yaji ya kara harzu a cikin wata nurya mai ranazarwa ya ce"Eh ba na sonki, ba na sonki nace, na aure ki ne saboda ro on da kakarki da mahaifiyarki suka yi min a kanki, ammh ina matsiyaci kamata ya dace da ar masu ku ar major guda kamar ki? Kuma da kike mganar Kaddara arya ne, ba kaddara ba ce, wannan kaddaran da kike mgana babanki ne ya ireta da kansa. Shi ne sila kuma Sanadi saboda haka ba ki da bakin kare shi da sunan kaddara Fatima." Ya arishe fa a yana sakar mata jajayen idanuwansa, jijiyon kansa sun daga ra au, karfin hannayensa sun fara tasowa naman kirjinsa na sama da kasa kamar wani zakin da ya jima a dawa bai samu naman daji ba, haka suka tsaya gaba da gaba suna kallon juna, cikin zubar kwallah Mimi ta ce. "Nago de ma Allah da ka sanar da ni komai da bakin ka. Yau ba sai gobe ba zan bar maka gidanka, zan jira ka domin ka aikomin da takardan sakina." A fusace ya ce"In na i fa? Ta yi wani mirmishi kafin ta saka hannu ta share hawayenta lokaci aya tana fa in" ka jira sammaci." Daga haka ta juya ta nufi wardrope in ta ta bu e tana neman hijabin da za ta saka ta na kuma hana kanta kuka amman wasu hawayen suna ara fitowa. auka wasa ta ke yi ba tafiya za ta yi ba ,bai ta a tunanin soyayyar da Mimi take yi masa zai saka ta bar shi ba. Sai kawai ya juya yana fa in" Is better da ki tafin, sannan ina jiran sammaci iyar Soja sannan iyar lauyoyin duniya." Daga haka ya fice daga akin a fusace sai dai ya na fitowa falo sai da ya yi turus ganin su Inna tsaye sai ya ji kuma gushinsa na sauka. Amman ya kasa mgana. Sai kawai Inna ta kalleshi kallo ido da ido, kallon da ba ta ta a yi masa ba, sai kawai ta ka a kai ta Juya ta fice daga akin su Hibba suma jikinsu a sanyaye suka rufa mata baya. Sai ya tsaya tsam da ranshi wata zuciyar na fa a masa bai kyauta ba me ya sa ya yi haka? Me ya sa ya fa a ma ma wacce yake so cewa baya son ta? Me ya sa ya saka ta kuka? Kamar ya juya ya koma ya bata hakuri amman ba ar zuciyarsa na hana shi, yana jin sautin kukanta amman kuma Wannan girman kan nasa da ri o ya sa ya kasa iya bin shawaran zuciyarsa yana jin Ssutin kukanta ya taka ya fita ya bar gidan gaba aya motar shi ya shiga ya kunna ba hanyar gida ya nufa ba sai ya nufi hanyar zuwa camp in su yana jin wani irin zafi a kasan ranshi Bai ta a tunanin da gaske Mimi ta ke ba, bai ta a tunanin haka ba, da ya san za ta iya tafiya ta bar shi da bai aikata abin da ya aikata ba. Ita kuma Mimi hijabi kawai ta saka sai jakarta da ta auka da wayarta. Ta fito daga akin tana sharan kwallah ko tsinke nata ata dauka ba, Inna Meri na zaune a falo a kasa ta yi tagumi Hibba ma da Walida na zaune saman kujera sun kasa mgana Mimi ta yi sallama ta shigo. Gaba ayansu suka mi e ban da Inna da ba ta motsa ba ta kula su Hibba ba ta duka gaban Inna cikin dauriya ta ce" Ki yi hakuri da abin da zan fa a miki Inna." Sai kawai Inna ta aga mata hannu lokaci aya tana fa in"Ba ki bukatar wani bayani Binta, na ji duk abubuwan da suka faru ba zan hanaki tafiya ba, ki je gida ki yi ma iyayenki bayanin duk abin da ya faru, wallah ina jin kunya wlh naji kunya da na san haka tun faru da ni da kaina zan maida ke gaban iyayenki, amman yanzu ma ba ta i ba, zan je na ba ma Hajiya hakuri, ke kuma ina miki fatan samun farinciki rayuwa anan gaba. Dolen shi zai sake ki, in kuma ya i sakin ki nima ina goyan bayan ki kai shi kotu alkali ya nema miki ha in ki." Inna ta karishe fa a tana fashewa da kuka Ita kuka Mimi kuka Walida kuka, Hibba ce ba ta yi kuka ba ta na ta ba ma Mimin hakuri ta bari da safe sai ta tafi tun da dare ya yi amman Mimi ta ce sai ta tafi Inna Kuma ba ta kara mgana ba sai kawai ta ma shige cikin akinta tana kuka, Mimi kuma ta ce tafiya kam ba fashi, dole Hibba ta saka mayafi ita da Walida suka raka Mimi har bakin titi ba ta samu adaidaita ba sai ta hau mashin karon farko a rayuwarta. Suna tafe tama kuka harda shessshe a da gaske ta bar Aji, ta na son shi amman ya zama dole ta rabu da shi tun da Allah bai rubuta za su rayu tare ba..ba alheri a zama da wanda baya sonka kuma bai san darajan mahaifanka ba, babu amfanin zama da wanda zuciyarsa ba ta da kyau wanda baya afuwa da yafiya a yadda ta ji zuciyarta tana ji a ranta kamar har gaban abada ta are tsakaninta da Mansoor Aji kenan. arshen Littafi na Biyu.* *Janafty* *INZB3001* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI 08066726866 Mai mashin in da ya auki Mimi bai direta Ko ina ba sai ofar gidan